bayyinaat

Published time: 09 ,February ,2017      08:30:48
Ayoyinta 7 ne, Ana kiranta Uwar Littafi domin ta tara ilmin da yake a cikin Kur’ani a dunkule. Basmala a cikinta take ga kira’ar Asim, ruwayar Hafs, amma banda a kira’ar Warsh. Muna fatan za a ci gaba da bibiyar abin da muke kawo muku na fassara da tarjamar surorin Kur'ani, da fatan za a taya mu addu'a don samun ci gaban hakan.
Lambar Labari: 37

بِِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَنِ الرَّحِيمِ

1. Da Sunan Allah Mai Rahama Mai Jin Kai.

الْحَمْدُ لِلّهِ رَبِّ الْعَالَمِينَ

2. Godiya ta tabbata ga Allah ubangijin talikai.

اَلرَّحْمَنِ الرَّحِيمِ

3. Mai rahama mai jin kai.

مَالِكِ يَوْمِ الدِّينِ

4. Mai mallakar ranar sakamako.

إيَّاكَ نَعْبُدُ وإِيَّاكَ نَسْتَعِينُ

5. Kai kadai muke bautawa kuma kai kadai ne muke neman taimako.

اِهْدِنَا الصِّرَاطَ المُسْتَقِيمَ
6. Ka shiryar da mu tafarki madaidaici.

صِرَاطَ الَّذِينَ أَنعَمْتَ عَلَيهِمْ غَيرِ المَغضُوبِ عَلَيهِمْ وَلاَ الضَّالِّينَ 

7. Tafarkin wadanda ka yi wa ni’ima, ba wadanda aka yi fushi da su ba, kuma ba batattu ba.

Ubangijin halittu ya tara ilmin Tafiyar da lamurran bayi da halitta su, kamar rayarwa, da matarwa, da ciyarwa, da shayarwa, da tufatarwa, Mai rahama Ya tara dukan rahamar duniya da dukkan ni'imomin samarwa gaba daya. Mai jin kai ya tara ni'imar duniya mai dogewa zuwa Lahira kamar ni'imar imani. Mai mallakar ranar sakamako, ya hada dukan abin da ya shafi makoma. Kai muke bauta wa kuma Kai muke neman taimako, ya tara tauhidin bauta da ibada. Hanya madaidaiciya, ta hada Littafin Allah da Ahlul Baiti (a.s) a matsayin wasiyyar Ma'aikin Allah. Wadanda aka yi wa ni'ima, su ne Alayen Ibrahim da Alayen Muhammad (a.s). Wadanda aka yi fushi da su, da kuma batattu, sun tara dukkan mutanen da suka kauce wa tafarki madaidaici.


Hafiz Muhammad Sa'id
Haidar Center for Islamic Propagation
+234 803 215 6884 (Text only or (Line, Tango, Viber, Whatsapp, Telegram)
(hfazah@yahoo.com) (hfazah@hotmail.com)

comments Masu kallo
Suna:
Adireshin Email:
* ra'ayi: