bayyinaat

Published time: 09 ,February ,2017      09:02:13
Surar Naba'i, tana da muhimmanci kwarai da gaske a kan lamarin halitta da yadda ubangiji ya tsara ta. Muna fatan za a ci gaba da bibiyar abin da muke kawo muku na fassara da tarjamar surorin Kur'ani, da fatan za a taya mu addu'a don samun ci gaban hakan.
Lambar Labari: 38
بِِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَنِ الرَّحِيمِ

Da sunan Allah, Mai rahama, Mai jin Kai

عَمَّ يَتَسَاءَلُونَ 

1. A kan me suke tambayar juna.

عَنِ النَّبَإِ الْعَظِيمِ 

2. A kan muhimmin labari mai girma.

الَّذِي هُمْ فِيهِ مُخْتَلِفُونَ 

3. Wanda suke saba wa juna a cikinsa?.

كَلَّا سَيَعْلَمُونَ 

4. A'aha! Za su sani. 

ثُمَّ كَلَّا سَيَعْلَمُونَ 

5. Kuma, a'aha! Za su sani. 

أَلَمْ نَجْعَلِ الْأَرْضَ مِهَادًا 

6. Ashe, ba Mu sanya kasa shimfida ba?

وَالْجِبَالَ أَوْتَادًا 

7. Da duwatsu turaku (ga rike kasa)?

وَخَلَقْنَاكُمْ أَزْوَاجًا 

8. Kuma, Mun halitta ku maza da mata?

وَجَعَلْنَا نَوْمَكُمْ سُبَاتًا 

9. Kuma, Muka sanya barcinku hutawa?

وَجَعَلْنَا اللَّيْلَ لِبَاسًا 

10. Kuma, Muka sanya dare (ya zama) sutura?

وَجَعَلْنَا النَّهَارَ مَعَاشًا 

11. Kuma, Muka sanya lokacin rana na neman abin rayuwa?

وَبَنَيْنَا فَوْقَكُمْ سَبْعًا شِدَادًا 

12. Kuma, Muka gina sammai bakwai masu karfi, , a samanku?

وَجَعَلْنَا سِرَاجًا وَهَّاجًا 

13. Kuma, Muka sanya fitila mai tsanin haske (rana(. 

وَأَنزَلْنَا مِنَ الْمُعْصِرَاتِ مَاءً ثَجَّاجًا 

14. Kuma, Muka saukar ruwa mai yawan zuba daga cikakkun giragizai?

لِنُخْرِجَ بِهِ حَبًّا وَنَبَاتًا 

15. Domin, Mu fitar da kwaya da tsiri da shi?

وَجَنَّاتٍ أَلْفَافًا 

16. Da itacen lambuna masu lillibniya?

إِنَّ يَوْمَ الْفَصْلِ كَانَ مِيقَاتًا 

17. Lalle ne, ranar rarrabewa ta kasance abin kayyade wa lokaci. 

يَوْمَ يُنفَخُ فِي الصُّورِ فَتَأْتُونَ أَفْوَاجًا 

18. Ranar da za a yi busa a cikin kaho, sai ku zo, jama'a-jama'a. 

وَفُتِحَتِ السَّمَاءُ فَكَانَتْ أَبْوَابًا 

19. Kuma, aka bude sama, sai ta kasance kofofi. 

وَسُيِّرَتِ الْجِبَالُ فَكَانَتْ سَرَابًا 

20. Kuma, aka tafiyar da duwatsu, sai suka kasance kura. 

إِنَّ جَهَنَّمَ كَانَتْ مِرْصَادًا 

21. Lalle ne, Jahannama ta kasance madakata. 

لِلْطَّاغِينَ مَآبًا 

22. Makoma ce ga masu ketare iyakoki. 

لَابِثِينَ فِيهَا أَحْقَابًا 

23. Suna, masu zama a cikinta, zamunna. 

لَّا يَذُوقُونَ فِيهَا بَرْدًا وَلَا شَرَابًا 

24. Ba su dandanar wani sanyi a cikinta, kuma ba su dandanar wani abin sha. 

إِلَّا حَمِيمًا وَغَسَّاقًا 

25. Sai dai tafasasshen ruwa da rubabben jini. 

جَزَاءً وِفَاقًا 

26. Sakamako mai dacewa. 

إِنَّهُمْ كَانُوا لَا يَرْجُونَ حِسَابًا 

27. Lalle ne, su, sun kasance ba su fatar wani saukin hisabi. 

وَكَذَّبُوا بِآيَاتِنَا كِذَّابًا 

28. Kuma, suka karyata da ayoyinMu, karyatawa!

وَكُلَّ شَيْءٍ أَحْصَيْنَاهُ كِتَابًا 

29. Kuma kowane abu Mun kididdige shi, a rubuce. 

فَذُوقُوا فَلَن نَّزِيدَكُمْ إِلَّا عَذَابًا 

30. Saboda haka ku dandana, domin haka ba za Mu kara muku komai ba sai azaba. 

إِنَّ لِلْمُتَّقِينَ مَفَازًا 

31. Lalle ne, masu takawa na da wani wurin samun babban rabo. 

حَدَائِقَ وَأَعْنَابًا 

32. Lambuna da inabobi. 

وَكَوَاعِبَ أَتْرَابًا 

33. Da cikakkun 'yan mata, tsaran juna. 

وَكَأْسًا دِهَاقًا 

34. Da hinjalan giya cikakku. 

لَّا يَسْمَعُونَ فِيهَا لَغْوًا وَلَا كِذَّابًا 

35. Ba sa jin yasassar magana a cikinta, kuma ba sa jin karyatawa. 

جَزَاءً مِّن رَّبِّكَ عَطَاءً حِسَابًا 

36. Sakamako daga Ubangijinka, kyauta mai yawa. 

رَبِّ السَّمَاوَاتِ وَالْأَرْضِ وَمَا بَيْنَهُمَا الرحْمَنِ لَا يَمْلِكُونَ مِنْهُ خِطَابًا 

37. Ubangijin sammai da kasa da abin da yake a tsakaninsu, Mai rahama, ba su da ikon yin wata magana daga gare Shi. 

يَوْمَ يَقُومُ الرُّوحُ وَالْمَلَائِكَةُ صَفًّا لَّا يَتَكَلَّمُونَ إِلَّا مَنْ أَذِنَ لَهُ الرحْمَنُ وَقَالَ صَوَابًا 

38. Ranar da Ruhi da mala'iku zasu tsaya a cikin sahu, ba sa magana, sai wanda Allah Ya yi masa izini, kuma ya fadi abin da yake daidai. 

ذَلِكَ الْيَوْمُ الْحَقُّ فَمَن شَاءَ اتَّخَذَ إِلَى رَبِّهِ مَآبًا

39. Wancan shi ne yini na gaskiya, to wanda ya so, ya riki makoma zuwa ga Ubangijinsa. 

إِنَّا أَنذَرْنَاكُمْ عَذَابًا قَرِيبًا يَوْمَ يَنظُرُ الْمَرْءُ مَا قَدَّمَتْ يَدَاهُ وَيَقُولُ الْكَافِرُ يَا لَيْتَنِي كُنتُ تُرَابًا 

40. Lalle ne, Mu, Mun yi muku gargadin azaba makusanciya, ranar da mutum ke dubi zuwa ga abin da hannayensa suka aikata, kuma kafiri ya ce; Kaicona, da dai na zama turbaya!

Hafiz Muhammad Sa'id
Haidar Center for Islamic Propagation
+234 803 215 6884 (Text only or (Line, Tango, Viber, Whatsapp, Telegram)
(hfazah@yahoo.com) (hfazah@hotmail.com)
comments Masu kallo
Suna:
Adireshin Email:
* ra'ayi: