bayyinaat

Published time: 11 ,December ,2020      23:04:11
Abin la'akari shi ne: gaba dayan A'imma (A.S) hadafinsu daya ne, wannan hadafin kuwa shi ne: Sãmar da Hukumar Allah a doron kasa, a nesa ko a kusa, sai dai hanyoyin kaiwa ga hadafin ne suke caccanzawa daga lokaci zuwa lokaci daga wani yanayin zuwa wani
Lambar Labari: 385
Hakika kamar yadda jagoran juyin juya hãlin musulunci Sayyid Ali Khamna'i (dãmat barakãtuhu) ya bayyana a cikin littãfi mai suna *250 الإنسان بعمر*

Abin nufi mutum mai shekara 250, cewa: Ba za ka fahimci rayuwar A'imma(A.S), in ka kalle su a daidai ku ba, domin abin da za ka dinga gani shi ne: Wani abu mai kama da sabãni, misali kamar tubka da warwara ne, to amma kuma ba haka abin yake ba, sai dai abin da ake bukata shi ne: Ka kalleSu a matsayin shakhsun wãhid (mutum daya), wanda ya rãyu da bayyanannun manufofi kuma iyakantattu a bisa matakai na ilimi da hankali hade da hikimomi.

Rayuwar wannan mutumin ita ce: Ta shûde a tsawon rayuwar Imamai(A.S), wato tun daga shekara ta 11 bayan hijira (wato bayan wafati Manzo S.A.W) har zuwa shekara ta 260. {{farkon shekarar gaiba Sugura -Fakuwa karama- ta Imam Muhammad Al'mahadi (A.F) wanda kuma shi ne: Imam na ƙarshe daga cikin jerin Imãmai sha biyu}}.
In ka hada zai zamo mutum mai shekara 250 kenan.

Wannan mutumin, a wasu lokutan yanayi yakansa shi yayi sauri, a wani lokacin kuma yayi sassarfa, kai wani lokacin ma yana lumfasawa ne, lumfasawa mai cike da hikima da tsara al'amura (ba don tsoro ba, sai dai saboda yanayi).

A wannan nazariyar-mahanga- za ka kalli rayuwar Imam Ali, Imam Hasan, Imam Husain da sauran Imamai Ma'asumai (A.S), a matsayin motsi guda daya ne mikakke har zuwa tsawon wadannan shekarun.

A wannan nazarin, ba za ka ce mene ne yasa Amirul Muminin (A.S) ya zauna lafiya da Halifofin da suka gabace shi ba? shi kuma Imam Hasan Almujtaba (A.S) ya yi sulhu ba? yayin da Imam Husain (A.S) ya yi fito na fito ba? sai kuma Imam Zainul Abidin (A.S) ya lumfasa ya zauna da wadanda suka kashe mahaifinsa ba tare da ya zare takobi a kansu ba?

A rarrabe in ka kalli rayuwar A'imma (A.S) za ka ga kamar sun sassaba.

Abin la'akari shi ne: gaba dayan A'imma (A.S) hadafinsu daya ne, wannan hadafin kuwa shi ne: Sãmar da Hukumar Allah a doron kasa, a nesa ko a kusa, sai dai hanyoyin kaiwa ga hadafin ne suke caccanzawa daga lokaci zuwa lokaci daga wani yanayin zuwa wani.

Imam Sajjãd (A.S) bayan Waki'ar Karbala.
Imam Sajjãd (A.S) shi ɗa ne ga Imam Husain (A.S), kuma ya halarci karbala, Shi ne: Imam na hudu a jerin limaman shiriya goma sha biyu(A.S) bayan Manzon Allah (S.A.W).
An ambace shi da Sajjad ne, saboda yawan sujudarsa. Imam Sajjãd (A.S) bayan waki'ar Karbala, shi da wadanda suka yi saura daga cikin Ahlul Bait (A.S) tun lokacin da suka isa Shãm -Suriya- a matsayin ribatattun yaki, ya tsãra sabon manhaji na gwagwarmayar musulunci daidai da maslahar wannan lokacin da kuma yanayi.
Imam Sajjãd (A.S) bayan waki'ar Karbala ya tsãra wasu dabaru da hanyoyin da zai zama ba za'a iya cin nasarar shãfe addinin Allah da ma'abotansa daga doron kasa ba.
Imãm (A.S) ya dauki wasu matakai muhimmai guda biyu domin cinmma wannan hadafin.
*Zan cigaba....*
comments Masu kallo
Suna:
Adireshin Email:
* ra'ayi: