bayyinaat

Published time: 12 ,December ,2020      02:52:39
Ƙiba idan ta wuce kima, tana haifar da matsaloli masu yawa ga mutum, daga cikin matsalolin akwai taruwar man cholesterol wanda ke haifar da cututtuka irin su hawan jini, Ciwon suga, mutuwar barin jiki (Stroke), da sauran su, wadanda suke kaiwa ga mutuwar farat daya. Idan ka kiyaye wadannan dabi'un to zaka zauna lafiya.
Lambar Labari: 392
Ƙiba idan ta wuce kima, tana haifar da matsaloli masu yawa ga mutum, daga cikin matsalolin akwai taruwar man cholesterol wanda ke haifar da cututtuka irin su hawan jini, Ciwon suga, mutuwar barin jiki (Stroke), da sauran su, wadanda suke kaiwa ga mutuwar farat daya. Idan ka kiyaye wadannan dabi'un to zaka zauna lafiya.

(1) Cin Abinci mai maiko, duk da cewa Abinci mai maiko na da nashi amfanin ga jiki, to amma idan mutum ya yawaita amfani da shi yana rage saurin narkewar Abinci, hakan kuma zai haifar da mummunar kiba. Domin Abincin zai zama kitse ya dankare a jiki.

(2) Yawaita kayan kwalam da makulashe, irin su nau'in Alawoyi, meat pie, snacks, egg roll da sauran su.

(3) Yawaita abin sha masu zaki, irin su lemon kwalba.

(4) Karanta shan ruwa tareda maye gurbin ruwan da kayan zakin da aka ambata a sama. Domin shi ruwa yana taimakawa wajen saurin narkewar Abinci.

(5) Rashin yin karin kumallo. Idan mutum ya karya, kwayoyin halitta da sassan jiki kan samu kuzari, suyi aikin da ya kamata na narkar da Abinci da tace shi.

(6) Karancin Barci ko rashin yinsa. Wannan kan sa jiki ya shiga kunci, ya kasa aikin sa na narkar da Abinci.

(7) Rashin cin kayan marmari da ganyayyaki. Su wadannan suna kunshe da sinadaran Vitamins da Minerals, su kuma suna taimakawa wajan saurin narkewar Abinci.

(8) Rashin ko karancin motsa jiki. Shi motsa jiki ya hada da tafiyar kasa, gudu, jojjoga da sauran su. Wannan ma yana taimakawa sosai wajan narkakewar Abinci.

Saboda haka duk wanda yake da dabi'ar rashin motsa jiki, karancin barci, karancin shan ruwa, karancin cin ganyayyaki da kayan marmari, rashin karin kumallo da sauran su, to ya shirya fuskantar hatsarin kibar da zata haifar masa da wadancan nau'ikan cututtukan karshe ga mutuwar farat daya.
comments Masu kallo
Suna:
Adireshin Email:
* ra'ayi: