bayyinaat

Published time: 22 ,January ,2017      11:14:47
Daga Muhammad dan Fudail daga Abul Hasan (a.s) ya ce: "Na tambaye shi: ina karanta Kur'ani sai fitsari ya kama ni sai in tashi in yi fitsari sannan in yi tsarki in wanke hannuna sannan sai in koma wa littafi sai in karanta shi? Sai ya ce: A'a, har sai ka yi alwalar salla". Daga littafin Hisal da sanadinsa daga Ali dan Abu Dalib (a.s) a wani hadisi guda dari hudu ya ce: bawa ba ya karanta Kur'ani idan ya kasance ba bisa tsarki ba har sai ya yi tsarki" .
Lambar Labari: 4
Falala Da Ladan Kur’ani
Akwai ruwayoyi da dama da suka kwadaitar da al’amura daban-daban game da kura’ani mai girma kamar haka;
1- Kwadaitarwa a kan karanta kur’ani
2- Ladan karanta kur’ani
3- Karanta kur’ani a cikin mushafinsa
4- Falalar koyon karatun kur’ani
5- Koyon kur’ani ga yara da samari
6- Ladan hardace kur’ani
7- Lada da falalar daukar kur’ani
8- Tasirin kur’ani a cikin gidaje
9- Mustahabbancin karanta kur’ani a cikin gidaje

Ladubban karanta kur’ani
Amma mu sani cewa kur’ani yana da ladubba da ya kamata a kiyaye su kamar haka;
Ladubban Zahiri
Ladubban zahiri, wadanda suka hada da:
1- Alwala domin karanta shi
2- Nutsuwa da kawaici
3- Ladabi: kamar fuskantar alkibla da zama waje daya da kaskan da kai
4- Farawa da ta’awizi da basmala
5- Rufewa da Sadakal-Lahul Aliyyul Aziim
6- Tartilin kur’ani; wato tsayawa wajan tunani game da ni’ima domin neman ta, ko azaba domin neman tsari daga gareta, da kuma neman gafara.
7- Tsarkake baki
8- Karantawa da murya ta mai alamar bakin ciki
9- Karantawa da sauti mai dadi
10- Daga sauti matsakaici

Ladubban Badini
Amma ladubban badini sun hada da:
1- Grimamawa ga zancen Allah
2- Halartar zuciya da barin waswasin zuciya da tunanin duniya
3- Tadabburi; wato halartar zuciya domin fahimtar me ake cewa, domin duk mai karanta kur’ani dole ya sani cewa da shi ne ake magana ba da waninsa ba.
4- Neman fahimta; shi ne gane abin da kowace aya take nufi, kamar magana kan hani da umarni da ni’ima da azaba da siffofin Allah da halayen masu gaskiya da na makaryata.
5- Jin cewa da shi mai karantawar ne kur’ani yake magana
6- Tasirantuwa da kur’ani ta yadda alamar abin da ake cewa zai bayyana a cikin ran mai karantawa
7- Jin cewa Allah yana magana da shi yayin karatun kur’ani, kuma wannan shi ne mafi girman mataki ga mai karanta shi, da fatan Allah ya ba mu dacewa kan hakan.

Daga Laduban Karanta Kur'ani
Daga Muhammad dan Fudail  daga Abul Hasan (a.s) ya ce: "Na tambaye shi: ina karanta Kur'ani sai fitsari ya kama ni sai in tashi in yi fitsari sannan in yi tsarki in wanke hannuna sannan sai in koma wa littafi sai in karanta shi? Sai ya ce: A'a, har sai ka yi alwalar salla".
Daga littafin Hisal da sanadinsa daga Ali dan Abu Dalib (a.s) a wani hadisi guda dari hudu ya ce: bawa ba ya karanta Kur'ani idan ya kasance ba bisa tsarki ba har sai ya yi tsarki" .
Daga Ahmad dan Fahad ya ce: Imam (a.s) ya ce: "mai karanta Kur'ani a cikin salla yana da lada dari ga dukkan harafi da yake karantawa a salla a tsaye, a zaune kuwa lada hamsin kuma yana mai tsarki, ba a salla ba lada ishirin da biyar, idan ba shi da tsarki lada goma, kuma ba na cewa: "A L M R" goma. Sai dai "A” lada goma kenan, "L” lada goma, "M” lada goma, "R” lada goma.
Daga Hasan dan Ali Askari (a.s) a tafsirinsa ya ce: Amma fadinsa wanda ya soyar da kai zuwa gareshi kuma ya umarce ka da karanta shi yayin karanta Kur'ani shi ne: "ina neman tsarin Allah mai ji masani daga shedan jefaffe, hakika Imam Ali (a.s) ya ce: ina neman tsari; ai ina neman kariyar Allah -har ya ce- neman tsari shi ne abin da Allah ya umarci bayi da shi gun karantawarsu ga Kur'ani, don haka idan ka karanta Kur'ani to ka nemi tsarin Allah daga shedan abin jefewa . kuma wanda ya ladabtu da ladubba, Allah zai kai shi zuwa ga shiriya madawwamiya. Sannan sai ya ambaci hadisin da tsayinsa daga Manzon Allah yana cewa: Idan kana son kada sharrinsu ya same ka, kuma kada makircinsu ya zo maka to ka fada idan ka wayi gari: "Ina neman tsarin Allah daga shedan jefaffe, to Allah zai kare ka sharrinsu.

Laduban Karanta Kur'ani Da Sauraronsa
Daga Jabir , daga Abu Ja'afar (a.s) ya ce: "Na ce: wasu mutane suna suma idan aka ambaci wani abu na Kur'ani ko aka fade shi sai su fadi kamar za a yanke hannunsu ko kafarsu ba zasu iya ji ba? Sai ya ce: subhanallah! Wannan daga shedan ne, ba da wannan ake siffanta su ba, shi ba komai ba ne sai taushi da hawaye da tsoro" .
Daga Abdullahi dan Abu ya'afur, daga Abu Abdullahi (a.s) ya ce: "na ce masa: mutumin da yake karanta Kur'ani, shin wajibi ne a kan wanda ya ji shi ya saurara kuma ya saurare shi? Sai ya ce: Haka ne, idan ya karanta Kur'ani gunka to wajibi ne a kanka ka saurara kuma ka saurare shi .
Daga Ali dan Mugira daga Abul Hasan (a.s) ya ce: Na ce masa: babana ya tambayi kakanka game da kammala Kur'ani a kowane dare, sai kakanka ya ce masa a kowane dare ne, sai ya ce masa: a watan Ramadan, sai kakanka ya ce masa: a watan Ramadan, sai babana ya ce masa haka ne daidai yadda zaka iya. Babana ya kasance yana kammala Kur'ani sau arba'in a watan Ramadan, sannan nima na sauke shi bayan babana. Saudayawa na kasa daga hakan ko kuma in dada sama da hakan, sannan sai na sanya ladan sauka daya ga Manzo (s.a.w) wata kuma saukar ga Imam Ali (a.s) wata kuma ga Fadima (a.s) sanan sai ga imamai daya bayan daya har na kawo kanka, sai na ba ka ladan sauka daya. To me nake da shi da wannan? Sai ya ce: zaka kasance tare da su a ranar kiyama. sai na ce: Allah mai girma ina da wannan?! Sai ya ce: E, har sau uku .
Daga Sulaiman dan khalid, daga Imam Ja'afar Sadik (a.s) ya ce: manzon Allah (s.a.w) ya zo wa wani saurayi daga Ansar sai ya ce: ni ina son in karanta muku Kur'ani duk wanda ya yi kuka yana da aljanna, sai ya karanta karshen surar Zumur: "Aka kora wadanda suka kafirta zuwa jahannama gargadawa" zuwa karshen sura. Sai kowa ya yi kuka banda wannan saurayin, sai ya ce: ya Manzon Allah (s.a.w) na nemi yin kuka amma idanuwana ba su zubo ba, sai ya ce: ni zan sake muku wanda ya nemi yin kuka to yana da aljanna, sai ya koma maimaitawa, sai mutane suka yi kuka, kuma shi ma wannan saurayi ya kirkiri kuka sai suka shiga aljanna gaba daya" .
Daga Ja'afar dan Muhammad daga babansa, daga iyayensa (a.s) ya ce: "ku koyi Kur'ani da larabcinsa…" . 
 Daga Sulaim daga babansa, daga Abu Abdullahi (a.s) ya ce: "ku koyi larabci domin shi ne zancen Allah da ya yi wa bayinsa magana da shi kuma magabata suka yi magana da shi" . 
A littafin Iddatud'da'i daga Abu Ja'afar Jawad (a.s) ya ce: mutane biyu ba su yi daidai ba a addini da cin nasara sai wanda ya fi su a wajen Allah (s.a.w) ya kasance shi ne wanda ya fi su ladabi. Sai na ce: na san fifikonsa a wajen mutane a majalisi, to Mene ne fifikonsa a wajen Allah (s.w.t)? Sai ya ce: Karanta Kur'ani kamar yadda ya sauka da karanta shi ba lahani, domin addu'a mai lahani ba ta hawa zuwa ga Allah".
Daga Sakuni daga Abu Abdullahi (a.s) ya ce: Annabi (s.a.w) ya ce: mutum ba'ajame daga al'ummata yakan karanta Kur'ani da ajaminsa sai mala'iku su daukaka shi sama wajen Allah da larabcinsa".

Karanta Kur'ani
Daga Abdullahi dan Sulaiman  ya ce: "na tambayi Abu Abdullahi (a.s) game da fadin Ubangiji "ka karanta Kur'ani karantawa" . Sai ya ce: Imam Ali (a.s) ya ce: ka bayyana shi a fili kada ka rera shi kamar waka, kuma kada ka daidaita shi kamar yashi, sai dai ku kwankwasa zukata kekasassu da shi, kuma kada hadafin dayanku ya zama shi ne ya kai karshen sura".
Daga salim alfarra'u daga wanda ya ba shi labari, daga Abu Abdullahi (a.s) ya ce: "Ka bayyana Kur'ani domin shi balarabe ne" .
 Daga Muhammad dan Fudail ya ce: Abu Abdullahi (a.s) ya ce: "An karhanta karanta kulhuwal-Lahau da lumfashi daya" .
Daga abu Basir, daga Abu Abdullahi ya ce: Fadinsa madaukaki: "Ka karanta Kur'ani karantawa". Ya ce: shi ne ka zauna a cikinsa ka kuma kyautata sautinka da shi" .
Daga Ummu Salama ta ce: "Manzon Allah (s.a.w) yana yanka karatunsa aya aya".
Daga ibn Abu umair, da wanda ya ambata, daga Imam Ja'afar Sadik (a.s) ya ce: "Kur'ani ya sauka da bakin ciki, ku karanta shi da bakin ciki" .
Daga Abdullahi dan Sinan daga Abu Abdullahi Imam Ja'afar Sadik (a.s) ya ce: "Allah ya yi wahayi ga Musa dan Imran (a.s) da cewa; idan ka tsaya a gabana, to ka tsaya matsayin mai kaskan da kai mabukaci, idan ka karanta Attaura to ka jiyar da ni da sauti mai bakin ciki" .
Daga Hafsu, ya ce: Ban ga wani mutum mafi tsananin tsoronsa a kan kansa daga Musa dan Ja'afar (a.s) ba, kuma ban ga wani mafi kauna daga gareshi ba, karatunsa ya kasance na mai bakin ciki ne, idan ya karanta to kamar yana magana da wani mutum ne" .

Karanta Kur'ani A Kodayaushe
Daga Mu'awiya dan Ammar  daga Abu Abdullahi a cikin wasiyyar Annabi ga Ali (a.s) ya ce: "ka yi riko da karanta Kur'ani a ko da yaushe"
Daga Zuhuri ya ce: na ce da Ali dan Husain (a.s) wane aiki ne ya fi? Ya ce: mai zuwa mai tafiya. Sai na ce: Mene ne mai zuwa mai tafiya? Sai ya ce: karanta farkon Kur'ani har zuwa karshensa, duk sadda farkonsa ya zo sai ya tafi karsensa" .
Daga Hafsu ya ce na ji Musa dan Ja'afar (a.s) yana cewa darajojin aljanna daidai gwargwadon ayoyin Kur'ani ne sai a ce: karanta ka yi sama sai ya karanta ya yi sama" .
Daga Abdullahi dan Sulaiman daga Abu Ja'afar (a.s) ya ce: " Kur'ani yana tsaye a sallarsa Allah zai rubuta masa kyakkyawa dari a kan kowane harafi kuma  shi a zaune a cikin sallarsa to Allah zai rubuta masa kyakkyawa hamsin a kan kowane harafi, kuma  ba a sallarsa ba to Allah zai rubuta masa kyakkyawa goma a kan kowane harafi" .
Daga bashir dan Galib al'asadi daga Husain dan Ali (a.s) ya ce:  aya daga littafin Allah madaukaki yana tsaye to za a rubuta masa kyakkyawa dari a kan kowane harafi, idan kuwa ba a salla ba ne to za a rubuta masa kyakkyawa goma, kuma idan ya saurari Kur'ani to Allah zai rubuta masa kyakkyawa da kowane harafi, idan kuwa ya kammala Kur'ani a dare to mala'iku zasu yi masa addu'a har safiya, idan kuwa ya kammala shi da rana to mala'iku masu kiyayewa zasu yi masa addu'a har maraice, kuma yana da addu'a da za a amsa masa kuma wannan ya fi masa abin da yake tsakanin sama da kasa. Sai na ce: wannan ga  Kur'ani kenan, wanda bai karanta ba fa? Sai ya ce: ya kai dan'uwan banu Asad Allah mai baiwa ne mai karimci idan ya karanta abin da ya sani Allah zai ba shi wannan" .

Karanta Kur'ani Da Duban Littafi
Daga Ya'akubu dan yazid  (ya dangana sanadinsa zuwa) ga Abu Abdullahi (a.s) ya ce: "Wanda ya karanta Kur'ani da duban mushafi to ganinsa ya dadada kuma za a rangwama wa iyayensa koda kuwa sun kasance kafirai ne".
Daga Annabi (s.a.w) ya ce: "Babu abin da ya fi yi wa shedan tsanani kamar karanta Kur'ani ta hanyar duban littafi" .
Daga Ishak dan Ammar, daga Abu Abdullahi (a.s) ya ce: ina fansarka da raina! Ni na hardace Kur'ani a zuciyata, shin in karanta shi da ka, ko da duba littafi, wanne ne ya fi? Sai ya ce: ka karanta da duba littafi shi ya fi, ba ka san duba cikin littafi ibada ba ne .
Daga Abuzar ya ce: "Na ji Manzon Allah (s.a.w) yana cewa: Duba zuwa ga Ali (a.s) ibada ce, duba zuwa ga iyaye da tausayawa da jin kai ibada ne, duba zuwa ga littafin Kur'ani shi ma ibada ne, haka nan duban Ka'aba ibada ne".
Daga Hammad dan Isa, daga Abu Abdullahi (a.s) daga babansa ya ce: "yana burge ni ya kasance akwai littafin Kur'ani a cikin gida da Allah yake kore shedanu da shi" .
Daga Abu Abdullah ya ce: "Uku suna kai kuka wajen Allah madaukaki "Masallaci da aka kauracewa mutane ba sa salla a ciki, da malami tsakanin jahilai, da littafi da aka rataye har kura ta hau kansa ba a karanta shi" .

Bayyana Karatun Kur'ani Da Boye Shi
Daga Saifu dan Umaira  daga wani mutum, daga Abu Ja'afar (a.s) ya ce: " "inna anzalnahu" yana mai bayyanar da sautinsa, to kamar mai zare takobinsa yana yaki a tafarkin Allah ne,  ta a boye to kamar mai cakuda jininsa ne a tafarkin Allah,  ta sau goma to za a shafe masa zunubai dubu".
Daga Mu'awiya dan Ammar ya ce: "Na ce da Abu Abdullah (a.s) mutumin da yake ganin yana wani abu na addu'a kuma yana karatu har sai ya daga sautinsa, sai ya ce: babu laifi, Ali dan Husain (a.s) ya kasance mafi kyawun sauti da Kur'ani, ya kasance idan ya daga sautinsa har sai mutanen gida sun ji sautinsa, kuma Abu Ja'afar ya kasance mafi kyawun mutane sauti da Kur'ani idan ya tsaya da dare yana karatu sai ya daga sautinsa sai masu wucewa na daga masu lambu da wasunsu su tsaya suna jin karatunsa" .
Daga Abuzar, daga Annabi (s.a.w) a wasiyyarsa ya ce: "ya Abuzar! Ka yi kasa da muryarka gun jana'iza da gun yaki da gun karatun Kur'ani" .
Daga Abdullahi dan Sinan, daga Abu Abdullahi (a.s) ya ce: Manzon Allah (s.a.w) ya ce: ku karanta Kur'ani da muryar larabawa da sautinsu kada ku yi sautin ma'abota fasikanci da masu ashararanci, ku sani wasu mutane zasu zo bayana suna maimaita Kur'ani kamar rera waka da kuma karar sauti da rahbaniyanci alhalin ba ya wuce makogaronsu, zukatansu a juye suke haka nan zukatan wanda suke burge shi" .
Daga Ali dan Muhammad Nufali, daga abul Hasan (a.s) ya ce: na ambaci murya gunsa sai ya ce: hakika Ali dan Husain (a.s) ya kasance yana karanta Kur'ani da yawa masu wucewa sukan tsaya sai ya kusa suma saboda kyawun sautinsa" .
Daga Abdullahi dan Sinan, daga Abu Abdullahi (a.s) ya ce Annabi (s.a.w) ya ce da ni komai yana da ado kuma adon Kur'ani shi ne sauti mai kyau" .
Daga Hasan dan Abdullahi tamimi daga babansa daga Ali Rida (a.s) ya ce: Manzon Allah (s.a.w) ya ce: "ku kyautata Kur'ani da sautinku ku sani sauti mai kyau yana dada wa Kur'ani kyau" .

Wanda Ya Saurari Karatun Kur'ani
Daga Muhammad dan Bashir  daga Ali dan Husain (a.s) hakika an ruwaito wannan hadisi daga Abu Abdullahi (a.s) ya ce: 'wanda ya saruari harafi daya daga littafin Allah ba tare da ya karanta ba to Allah zai rubuta masa kyakkyawa (lada) kuma ya shafe masa mummuna (zunubi) kuma ya daukaka shi daraja, kuma wanda ya koyi harafi Allah zai rubuta masa lada goma ya shafe masa zunubi goma kuma ya daukaka shi daraja goma. ya ce: ba na cewa: kowace aya, abin da nake nufi harafi kamar 'b', ko 't', da makamantansu, ya ce:  harafi yana zauni to Allah zai rubuta masa lada hamsin ya shafe masa zunubi hamsin kuma ya daga masa daraja hamsin. Kuma  harafi yana tsaye a salla to Allah zai rubuta masa lada dari kuma ya shafe masa zunubi dari kuma ya daukaka shi daraja dari, kuma wanda ya kammala shi to yana da addu'a da za a amsa masa da gaggawa da kuma ta jinkiri, ya ce: sai na ce: ina fansarka! kammala shi dukkansa? Ya ce: kammala shi dukkansa" .
Daga Ishak dan Ammar daga bu Abdullahi (a.s) ya ce: " aya ta Kur'ani yana salla da ita a kowane dare to Allah zai rubuta masa kunutin (ibadar) dare daya,  ayoyi dari ba a sallar dare ba to Allah zai rubuta masa sisin lada a lauhil mahafuz, sisi yana nufin; ukiyya dubu da dari biyu, kowace ukiyya tafi dutsen uhudu girma .
Daga Anas ya ce: Manzon Allah (s.a.w) ya ce: " aya dari ba za a rubuta shi daga masu gafala ba, kuma  aya dari biyu to za a rubuta shi cikin masu ibada, kuma  ayoyi dari uku to Kur'ani ba zai kai kararsa ba". Yana nufin wanda ya hardace shi kamar kwatankwacin hakan, masu magana sukan ce: yaron ya karance Kur'ani idan ya hardace shi .

Falalar Koyon Kur'ani Da Koyar Da Shi
Akwai ruwayoyi masu yawa da suka zo a littafin wasa'il: da zamu kawo wasu a nan don neman albarka da kuma fa'ida :
Daga Sa'adul khifaf daga Abu Ja'afar (a.s) ya ce: "ya Sa'ad ku koyi Kur'ani hakika shi zai zo ranar alkiyama cikin mafi kyawun sura da dan Adam yake iya gani (har ya ce): har sai ya je wajen Ubangiji mai izza sai Ubangiji ya kira shi da cewa; ya kai hujjata a duniya kuma zancena mai gaskiya daga kanka ka kuma tambaya za a ba ka, ka nemi ceto za a ba ka, yaya ka ga bayina? Sai ya ce: ya Ubangiji a cikinsu akwai wanda ya kiyaye ni ya kuma hardace ni bai tozartani ba, daga cikinsu kuma akwai wanda ya tozarta ni, ya wulakanta ni, ya karyata ni, kuma ni ne hujjarka a kan halittarka gaba daya.
Sai Allah ya ce: na rantse da grimana da daukakata da kuma daukakar matsayina yau zan saka wa mutane game da kai da mafi kyawun sakamako, kuma zan yi ukuba saboda kai da mai zafin azaba. (har ya ce): sai ka ga mutum daga shi'armu ya zo yana cewa da shi: ba ka san ni ba? Ni ne kura'anin da ya sanya ka rashin baccin dare da kuma wahalar rayuwa, sai ya tafi da shi wajen Ubangiji ya ce: ya Ubangiji! Bawanka wannan ya wahala saboda ni, ya kiyaye ni, ana gaba da shi saboda ni, kuma yana so kuma yana ki saboda ni, sai Ubangiji ya ce: ku shigar da bawana aljannata, ku tufatar da shi kayan ado na aljanna kuma ku sanya masa hular ado, idan aka yi masa haka sai a kawo shi wajen Kur'ani sai a ce da shi: shin ka yarda da abin da Ubangijinka ya yi wa masoyinka? Sai (Kur'ani) ya ce: ya Ubangiji wannan kadan ne, ka dada masa alheri dukkaninsa, sai ya Ubangiji ya ce: na rantse da girmana zan dada masa da shi da wadanda suke tare da shi irinsa abubuwa biyar: (su ne) su samari ne kuma ba zasu taba tsufa ba, kuma masu lafiya ba zasu taba yin rashin lafiya ba, kuma masu wadata ba zasu taba talauci ba, kuma masu farin ciki ba zasu taba bakin ciki ba, masu rayuwa ne ba zasu taba mutuwa ba… hadisi" .
Daga Yunus dan Ammar ya ce: Abu Abdullahi (a.s) ya ce: "za a kira mumini a yi masa hisabi, sai Kur'ani ya zo gabansa a sura mafi kyau ya ce: ya Ubangiji ni ne Kur'ani kuma wannan bawanka ne mumini da yake wahalar da kansa da karanta shi kuma yake tsawaita darensa da karanta shi, kuma idanuwansa suke rasa bacci, sai ka yardar da shi kamar yadda ya yardar da ni, ya ce: sai Ubangiji madaukaki ya ce: Bawana shimfida hannun damarka, sai ya cika ta da yardar Allah a kuma cika hagunsa da rahamar Allah sannan a ce: Wannan aljannar ta halatta gareka sai ka karanta ka kuma daukaka idan ya karanta wata aya sai ya dada daraja" .

Ma'abota Kur'ani Da Falalarsu
Daga Sakuni  daga Abu Abdullah (a.s) ya ce: Manzon Allah (s.a.w) ya ce: ma'abota Kur'ani suna cikin darajoji madaukaka kan dukkan mutane banda annabawa da manzanni, kada ku danne wa ma'abota Kur'ani hakkokinsu, ku sani suna da wani matsayi mai girma a wajen Allah madaukaki".
Daga Abdullah dan Abbas daga Manzon Allah (s.a.w) ya ce: madaukakan al'ummata su ne masu hardace Kur'ani kuma masu raya dare" .
Daga abu Sa'idul khuduri, ya ce: "Manzon Allah (s.a.w) ya ce: "masu hardace Kur'ani su ne malaman 'yan aljanna" .
Daga Imam Hasan Askari (a.s) a tafsirinsa, daga iyayensa daga Annabi (s.a.w) ya ce: masu hardace Kur'ani sun kebanta da rahamar Allah musamman, masu sanye da hasken Allah, masana zancen Allah, masu kusanci da Allah, wanda ya so su ya so Allah, wanda kuma ya ki su to hakika ya ki Allah, kuma Allah yana kare wa mai jin karatun Kur'ani dukkan bala'o'in duniya da albarkacinsu, kuma yana kare mai karanta shi daga bala'o'in lahira. Na rantse da wanda ran Muhammad (s.a.w) take hannunsa! mai jin karatun Kur'ani yana mai imani da shi ladansa ya fi na wanda ya yi sadaka da zainare mai girman Sabir, kuma mai karanta Kur'ani yana imani da shi ya fi ladan abin da yake daga al'arshi zuwa karkashin kasa" .
Daga Fudail dan yassar daga Abu Abdullahi (a.s) ya ce: mai hardace Kur'ani mai aiki da shi yana tare da safaratul kiram madaukakan mala'iku" .
Daga Abu Abdullah (a.s) ya ce: na ji shi yana cewa: "wanda yake karanta Kur'ani da kyar yana kiyaye shi da wahala da kuma karancin hardarsa, to yana da lada biyu" .

Masanin Kur'ani Da Ba Ya Aiki Da Shi
Daga Manzon Allah (s.a.w) ya ce : wanda ya koyi Kur'ani bai yi aiki da shi kuma ya zabi son duniya da kawarta to ya cancanci fushin Allah kuma yana matsayi daya da Yahudu da Nasara wadanda suka wurgar da littafin Allah a bayansu kuma  Kur'ani yana neman suna da duniya da shi to zai hadu da Allah fuskrasa babu tsoka ko daya kuma a Kur'ani ya tura keyarsa har sai ya shigar da shi wuta, kuma ya fada cikinta tare da wanda ya fada,  Kur'ani bai yi aiki da shi ba to Allah zai tashe shi ranar kiyama makaho sai ya ce: "ya Ubangiji me ya sa ka tashe ni makaho alhalin ina mai gani da can" . sai ya ce: "haka nan ne muka zo maka ayoyinmu sai ka manta su, kuma haka nan ne a yau za a manta da kai" . Sai a yi umarni da shi zuwa wuta, kuma  Kur'ani domin neman ladan Allah da ilimin addini yana da lada kamar na dukkan abin da aka ba wa mala'iku da annabawa da manzanni, kuma wanda ya koyi Kur'ani yana son riya da neman suna da shi domin ya yi jayayya da wawaye kuma ya yi alfahari ga malamai ya kuma nemi duniya da shi to Allah zai daidaita kashinsa ranar kiyama kuma babu wata wuta da ta fi azabar tasa, kuma babu wata na'uin azaba sai an yi masa ita saboda tsananin fushin Allah a kansa kuma wanda ya koyi Kur'ani ya kaskantar da kai a neman ilmi kuma ya sanar da bayin Allah yana neman abin da yake wajan Allah to babu wani wanda ya fi shi lada ko matsayi, kuma babu wata daraja madaukakiya ko matsayi sai ya samu rabo mafi girma da matsayi mafi daukaka daga gareta" .
Daga Annabi (s.a.w) ya ce: "hakika akwai wani wuri a jahannama da 'yan wuta suke neman tsari da shi kullum sau dubu saba'in (har ya ce) sai aka tambaye shi wannan azabar wa kenan? Ya ce: ga mai shan giya daga masu karatun Kur'ani masu barin salla" .
Daga Abul ash'hab annakha'i ya ce: Ali dan Abi Dalib ya ce: "wanda ya shiga musulunci yana mai biyayya kuma ya karanta Kur'ani a zahiri to yana da dinare dari biyu daga Baitulmalin musulmi idan aka hana shi a duniya to zai karba a lahira a lokacin da yake mafi bukata gareta" .
Daga Muhammad dan Ali dan Husain ya ce: Abu Abdullahi (a.s) ya ce:"kada ku sanya mata a dakuna kuma kada ku koya musu rubutu (kawai) kada ku koya musu surar Yusuf, ku koya musu saka da surar Nur… " hanin abin da ake nufi da shi wato rubutu da karatu na fitina.

Masu Hardace Kur'ani Da Siffofinsu
Daga Amru dan Jami'i  daga Abu Abdullah ya ce: Manzo Allah (s.a.w) ya ce: mafifinnci mutane da ya cancanci tsoro a fili da a boye, shi ne; mai hardace Kur'ani, kuma wanda ya fi cancantar salla da azumi a boye da fili shi ne mai hardce kura'ni.
 Sannan sai ya yi kira da sauti madaukaki: ya kai mai hardace Kur'ani kakaskantar da kai Allah zai daukaka ka, kada ka yi izza da shi sai Allah ya kaskantar da kai, ya kai mahardacin Kur'ani ka yi ado da shi saboda Allah sai Allah ya yi maka ado da shi, kada ka yi ado da shi ga mutane sai Allah ya aibata ka, wanda ya cika Kur'ani to yana kansa ne kada ya yi jahilci tare da masu jahilci kuma kada ya yi fushi cikin masu fushi kuma ya yi rangwame ya yi hakuri don girman Kur'ani, wanda aka ba wa Kur'ani sai ya yi tsammanin an ba wa wani abin da ya fi nasa to ya wulakanta abin da Allah ya girmama kuma ya girmama abin da Allah ya wulakanta .
Daga Abu Ja'afar (a.s) ya ce: masu karanta Kur'ani mutum uku ne, mutumin da ya karanta Kur'ani sai ya rike shi kayan hajarsa kuma ya nemi abin da yake hannun sarakuna da shi kuma ya daga wa mutane kai da shi. Da mutumin da ya karanta Kur'ani sai ya hardace harruffansa ya tozarta dokikinsa ya kuma munana kiyaye shi, to kada Allah ya yawaita wadannan daga cikin masu hardar Kur'ani. Da mutumin da ya karanta Kur'ani sai ya sanya maganin Kur'ani inda cutarsa take sai ya raya darensa da shi kuma ya ji yunwar ranarsa da shi kuma ya tsayar da sallolinsa da shi, ya kuma nisanci shimfidarsa da shi, da wadannan ne Allah ya kare bala'o’i daga mutane kuma da su ne Allah yake maganin makiya, da su ne Allah ya ke saukar da ruwan sama, wallahi! Wadannan a cikin mahardata Kur'ani su suka fi karanci daga jan kibrit .
Daga Husain dan yazid daga Ja'afar Sadik daga kakanninsa (a.s) a cikn hadisin da yake magana kan abubuwan da aka hana ya ce: " Kur'ani sannan sai ya sha haram da shi ko ya zabi son duniya da kawarta a kansa to ya samu fushin Allah sai dai idan ya tuba, ku sani wanda ya mutu ba tare da tuba ba to Allah zai yi masa hisabi, kuma ba zai gushe ba sai abin rusawa" .
Daga Isma'il dan abu ziyad daga Ja'afar Sadik daga kakanninsa (a.s) ya ce: Manzon Allah (s.a.w) ya ce: "mutum biyu daga al'ummata idan suka gyaru al'ummata ta gyaru idan suka lalace al'ummata ta lalace: sarakuna da makaranta" .
Daga Sakuni daga abu Abdullahi daga babansa daga iyayensa (a.s) ya ce: " Kur'ani yana cin hakkin mutane da shi to zai zo ranar lahira babu wata tsoka ko kashi a fuskarsa .

Wanda Ya Hardace Kur'ani Ya Manta
Daga abu Basir  ya ce: Abu Abdullahi (a.s) ya ce: wanda ya mance surar Kur'ani to za a lika masa ita a cikin sura mai kyau, idan ya gan ta sai ya ce: ke wacece? Kina da kyau sosai! Ina ma dai ke tawa ce! Sai ta ce: ba ka sanni ba ne? ni ce sura kaza da kaza, da ba ka manta da ni ba da na daukaka ka zuwa wannan matsayi".
Daga Ya'akubul Ahmar ya ce: na ce da Abu Abdullahi (a.s): ina da bashi a kaina mai yawa kuma Kur'ani ya kusa kubuce mini, sai Abu Abdullahi (a.s) ya ce: Kur'ani! Kur'ani! Ka sani sura aya ko sura daya a Kur'ani takan zo ranar kiyama har sai ta daukaka ka daraja wacce da ka kiyaye ta da ta kai ka can" .
Daga Ya'akubul Ahmar ya ce: na ce da Abu Abdullahi (a.s) in fansarka da raina bakin cikin ya same ni kuma ba abin da ya rage mini na alheri sai da wani abu ya kubuce mini daga gareshi har Kur'ani wani abu ya kubue ce mini daga gareshi. Sai hankalisa ya tashi da na ambaci Kur'ani sannan sai ya ce: mutum yakan manta da surar Kur'ani sai ta zo masa ranar kiyama har sai ta yi sama da shi da wasu darajoji sannan sai ta ce: aminci ya tabbata gareka, sai ya ce: aminci ya tabbata gareki ke wace ce? Sai ta ce: ni ce sura kaza da kaza ka tozarta ni ka bar ni, amma da ka yi riko da ni da na kai ka wannan daraja, sannan sai ya yi nuni da dan yatsansa sannan sai ya ce: ina umartar ku da karanta Kur'ani ku nemi saninsa ku sani daga mutane akwai wanda yake neman sanin Kur'ani don a ce masa wane mai karatu ne, daga cikinsu akwai wanda yake neman saninsa domin ya nemi suna da shi, sai a ce wane yana da murya mai kyau wadannan ba su da wani alheri. Daga cikinsu akwai wanda yake neman saninsa sai ya tsayar da shi dare da ranar ba ruwansa mutane sun sani ko kuwa ba su sani ba" .
Daga Sa'id dan Abdullahil A'araj ya ce: na tambayi Abu Abdullahi (a.s) game da mutumin da yake karanta Kur'ani sannan sai ya manta shi, shin yana da laifi? Sai ya ce: A'a .
Da kuma abin da yazo daga Husain dan Zaid daga Ja'afar Sadik (a.s) daga iyayensa (a.s) a wani hadisi (game da abubuwan da aka hana) cewa Manzon Allah (s.a.w) ya ce: "ku sani wanda ya koyi Kur'ani sannan sai ya manta shi to zai hadu da Allah ranar kiyama abin yi wa kukumi kuma a sallada masa maciji sakamakon kowace aya da ya manta ta ya kasance mai tafiya tare da shi zuwa wuta sai dai idan an gafarta masa". Wannan yana nufin wanda ya bar hukunce-hukuncensa ne.

Surar Fatiha Da Falalarta
Daga Hasan dan Ali Askari (a.s) daga iyayensa (a.s) ya ce: "Fatiha ita ce mafi daukakar abin da yake cikin taskokin al'arshi (har dai ya ce:)  ta yana mai imani da wilayar Muhammad da alayensa to Allah zai ba shi lada a kan kowane harafi kowanne daga ciki ya fi duniya da duk abin da yake cikinta na dukiya da alhairai, wanda kuwa ya ji mai karanta ta to yana da girman abin da yake ga mai karantawa, don haka kowannenku ya yawaita wannan alheri" .
Daga Fadl dan Hasan Dabarasi (majma'al bayan) daga Annabi (s.a.w) ya ce:"mafificiyar ibada ita ce karanta Kur'ani" .
Daga gareshi ya ce: "wannan Kur'ani shi ne igiyar Allah kuma haske mabayyani, kuma sheto mai amfani (har ya ce) ku karanta shi, ku sani Allah yana saka wa da lada goma a kan karanta shi da kowane harafi na karanta shi, ku sani ni ba na cewa: "A, L, M” goma kenan, sai dai "A” goma "L” goma "M” goma .
Daga gareshi (a.s) yana cewa: "ana cewa da mai karanta Kur'ani karanta ka daukaka, karanta kamar yadda kake karantawa a duniya ka sani matsayinka in da ka tsaya ne" .
Daga gareshi (a.s): " Kur'ani kamar an sanya annabta ne a goshensa sai dai shi ba a yi masa wahayi" . 
Daga Ahmad dan Fahad (a littafin Iddatud'da'i) daga Annabi (s.a.w) ya ce: "Ubangiji madaukaki ya ce: wanda ya shagaltu da karanta Kur'ani yana barin rokona to zan ba shi mafificin abin da nake ba wa masu godiya" .

Godiya Ta Tabbata Ga Ubangijin Talikai

Hafiz Muhammad Sa'id
Haidar Center for Islamic Propagation
+234 803 215 6884 (Text only or (Line, Tango, Viber, Whatsapp, Telegram)
(hfazah@yahoo.com) (hfazah@hotmail.com)
12 Rabi’ul awwal 1427 - 22 Parbardin 1385 - 11 Afrilu 2006

comments Masu kallo
Suna:
Adireshin Email:
* ra'ayi: