bayyinaat

Published time: 09 ,February ,2017      09:16:06
Tana karantar da Tashin kiyama gaskiya ne, kuma Kur’ani gaskiya ne, daga Allah yake, babu ragi babu kari, ya taho ta hannun aminci daga Allah zuwa ga Annabi.Muna fatan za a ci gaba da bibiyar abin da muke kawo muku na fassara da tarjamar surorin Kur'ani, da fatan za a taya mu addu'a don samun ci gaban hakan.
Lambar Labari: 41
Tana karantar da Tashin kiyama gaskiya ne, kuma Kur’ani gaskiya ne, daga Allah yake, babu ragi babu kari, ya taho ta hannun aminci daga Allah zuwa ga Annabi. 

بِِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَنِ الرَّحِيمِ

Da sunan Allah, Mai rahama, Mai jin Kai 

إِذَا الشَّمْسُ كُوِّرَتْ 

1. Idan aka kisfe rana. 

وَإِذَا النُّجُومُ انكَدَرَتْ 

2. Kuma idan taurari suka gurbace.

وَإِذَا الْجِبَالُ سُيِّرَتْ 

3. Kuma idan duwatsu aka tafiyar da su. 

وَإِذَا الْعِشَارُ عُطِّلَتْ 

4. Kuma idan rakuma masu cikkuna aka sake su wawai.

وَإِذَا الْوُحُوشُ حُشِرَتْ 

5. Kuma idan dabbobin daji aka tattara su.

وَإِذَا الْبِحَارُ سُجِّرَتْ 

6. Kuma idan tekuna aka mayar da su wuta. 

وَإِذَا النُّفُوسُ زُوِّجَتْ 

7. Kuma idan rayuka aka aurar da su (ga matattu). 

وَإِذَا الْمَوْؤُودَةُ سُئِلَتْ 

8. Kuma idan wadda aka turbude ta da rai aka tambaye ta. 

بِأَيِّ ذَنبٍ قُتِلَتْ 

9. Saboda wane laifi ne aka kashe ta?

وَإِذَا الصُّحُفُ نُشِرَتْ 

10. Kuma idan takardun ayyuka aka watsa su.

وَإِذَا السَّمَاءُ كُشِطَتْ 

11. Kuma idan sama aka fede ta. 

وَإِذَا الْجَحِيمُ سُعِّرَتْ 

12. Kuma idan Jahim aka hura ta.

وَإِذَا الْجَنَّةُ أُزْلِفَتْ 

13. Kuma idan Aljanna aka kusantar da ita. 

عَلِمَتْ نَفْسٌ مَّا أَحْضَرَتْ 

14. Rai ya san abin da ya halartar. 

فَلَا أُقْسِمُ بِالْخُنَّسِ 

15. To, ba sai Na yi rantsuwa da taurari matafa ba. 

الْجَوَارِ الْكُنَّسِ 

16. Masu gudu suna buya. 

وَاللَّيْلِ إِذَا عَسْعَسَ 

17. Da dare idan ya bayar da baya. 

وَالصُّبْحِ إِذَا تَنَفَّسَ 

18. Da safiya idan ta yi lumfashi. 

إِنَّهُ لَقَوْلُ رَسُولٍ كَرِيمٍ 

19. Lalle ne shi (Kur'ani), maganar wani manzo ne mai girma. 

ذِي قُوَّةٍ عِندَ ذِي الْعَرْشِ مَكِينٍ 

20. Mai karfi, mai daraja a wurin Mai Al'arshi. 

مُطَاعٍ ثَمَّ أَمِينٍ 

21. Wanda ake yi wa da'a ne, amintacce a can. 

وَمَا صَاحِبُكُم بِمَجْنُونٍ 

22. Kuma abokinku ba mahaukaci ba ne. 

وَلَقَدْ رَآهُ بِالْأُفُقِ الْمُبِينِ 

23. Kuma lalle ne, ya gan shi a cikin sararin sama mabayyani. 

وَمَا هُوَ عَلَى الْغَيْبِ بِضَنِينٍ 

24. Kuma shi, ga gaibi ba mai rowa ba ne. 

وَمَا هُوَ بِقَوْلِ شَيْطَانٍ رَجِيمٍ 

25. Kuma shi ba maganar shedni abin la'ana, ba ce. 

فَأَيْنَ تَذْهَبُونَ 

26. Shin, to ina za ku tafi?

إِنْ هُوَ إِلَّا ذِكْرٌ لِّلْعَالَمِينَ 

27. Lalle ne shi ba komai ba ne sai ambato ga talikai. 

لِمَن شَاءَ مِنكُمْ أَن يَسْتَقِيمَ 

28. Ga wanda ya so daga cikinku, ya shiryu. 

وَمَا تَشَاؤُونَ إِلَّا أَن يَشَاء اللَّهُ رَبُّ الْعَالَمِينَ 

29. Kuma ba zaku so ba sai idan Allah Ubangijin talikai ya yarda.

Hafiz Muhammad Sa'id
Haidar Center for Islamic Propagation
+234 803 215 6884 (Text only or (Line, Tango, Viber, Whatsapp, Telegram)
(hfazah@yahoo.com) (hfazah@hotmail.com)
comments Masu kallo
Suna:
Adireshin Email:
* ra'ayi: