bayyinaat

Published time: 09 ,February ,2017      09:17:45
Tana karantar da gaskiyar Tashin Kiyama, kuma ayyukan mutum na duniya ana tsare da su domin hisabi da sakamako. Muna fatan za a ci gaba da bibiyar abin da muke kawo muku na fassara da tarjamar surorin Kur'ani, da fatan za a taya mu addu'a don samun ci gaban hakan.
Lambar Labari: 42
Tana karantar da gaskiyar Tashin Kiyama, kuma ayyukan mutum na duniya ana tsare da su domin hisabi da sakamako.


بِِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَنِ الرَّحِيمِ

Da sunan Allah, Mai rahama, Mai jin Kai

إِذَا السَّمَاءُ انفَطَرَتْ 

1. Idan sama ta tsage. 

وَإِذَا الْكَوَاكِبُ انتَثَرَتْ 

2. Kuma idan taurari suka watse. 

وَإِذَا الْبِحَارُ فُجِّرَتْ 

3. Kuma idan tekuna aka facce su. 

وَإِذَا الْقُبُورُ بُعْثِرَتْ 

4. Kuma idan kaburbura aka tone su. 

عَلِمَتْ نَفْسٌ مَّا قَدَّمَتْ وَأَخَّرَتْ 

5. Rai ya san abin da ya gabatar, da abin da ya jinkirtar. 

يَا أَيُّهَا الْإِنسَانُ مَا غَرَّكَ بِرَبِّكَ الْكَرِيمِ 

6. Ya kai mutum! Me ya ruءe ka game da Ubangijinka, Mai karimci. 

الَّذِي خَلَقَكَ فَسَوَّاكَ فَعَدَلَكَ 

7. Wanda Ya halitta ka sa'an nan ya daidaita ka, Ya kuma tsakaita ka. 

فِي أَيِّ صُورَةٍ مَّا شَاءَ رَكَّبَكَ 

8. Ya gina ka a kan kowace irin sura Ya so. 

كَلَّا بَلْ تُكَذِّبُونَ بِالدِّينِ 

9. A'aha, ba haka ba, kuna karyatawa game da sakamako!ٍ

وَإِنَّ عَلَيْكُمْ لَحَافِظِينَ 

10. Lalle ne akwai matsara a kanku. 

كِرَامًا كَاتِبِينَ 

11. Masu daraja, marubuta. 

يَعْلَمُونَ مَا تَفْعَلُونَ 

12. Suna sanin abin da kuke aikatawa. 

إِنَّ الْأَبْرَارَ لَفِي نَعِيمٍ 

13. Lalle ne, masu da'a ga Allah suna cikin ni'ima. 

وَإِنَّ الْفُجَّارَ لَفِي جَحِيمٍ 

14. Kuma lalle ne, fajirai, suna cikin Jahim. 

يَصْلَوْنَهَا يَوْمَ الدِّينِ 

15. Za su shige ta a ranar sakamako. 

وَمَا هُمْ عَنْهَا بِغَائِبِينَ 

16. Ba za su faku daga gare ta ba. 

وَمَا أَدْرَاكَ مَا يَوْمُ الدِّينِ 

17. Kuma me ya sanar da kai abin da ake ce wa ranar sakamako?

ثُمَّ مَا أَدْرَاكَ مَا يَوْمُ الدِّينِ 

18. Sa'an nan, me ya sanar da kai abin da ake ce wa ranar sakamako? 

يَوْمَ لَا تَمْلِكُ نَفْسٌ لِّنَفْسٍ شَيْئًا وَالْأَمْرُ يَوْمَئِذٍ لِلَّهِ

19. Rana ce da wani rai ba ya iya mallakar komai domin wani rai, al'amari a ranar nan ga Allah yake.

Hafiz Muhammad Sa'id
Haidar Center for Islamic Propagation
+234 803 215 6884 (Text only or (Line, Tango, Viber, Whatsapp, Telegram)
(hfazah@yahoo.com) (hfazah@hotmail.com)
comments Masu kallo
Suna:
Adireshin Email:
* ra'ayi: