bayyinaat

Published time: 22 ,January ,2017      11:38:48
Surar Alfijir, tana koyar da mu abubuwa masu yawa na rayuwar mutum da godiya ga Allah ko butulce wa ni'imarsa. Muna fatan za a ci gaba da bibiyar abin da muke kawo muku na fassara da tarjamar surorin Kur'ani, da fatan za a taya mu addu'a don samun ci gaban hakan.
Lambar Labari: 7
سورة الفجر

Surar Alfijir

بِِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَنِ الرَّحِيمِ

Da sunan Allah, Mai rahama, Mai jin Kai

وَالْفَجْرِ 

1. Ina rantsuwa da alfijiri. 

وَلَيَالٍ عَشْرٍ

2. Da darare goma. 

وَالشَّفْعِ وَالْوَتْرِ 

3. Da (adadi na) cika da (na) mara. 

وَاللَّيْلِ إِذَا يَسْرِ 

4. Da dare idan yana shudewa. 

هَلْ فِي ذَلِكَ قَسَمٌ لِّذِي حِجْرٍ 

5. Ko a cikin wadannan akwai abin rantsuwa ga mai hankali.

أَلَمْ تَرَ كَيْفَ فَعَلَ رَبُّكَ بِعَادٍ 

6. Ba ka ga yadda Ubangijinka Ya aikata da Adawa ba? 

إِرَمَ ذَاتِ الْعِمَادِ 

7. Iramawa masu sakon kirar jiki. 

الَّتِي لَمْ يُخْلَقْ مِثْلُهَا فِي الْبِلَادِ 

8. Wadanda ba a halitta kwatankwacinsu ba a cikin garuruwa.

وَثَمُودَ الَّذِينَ جَابُوا الصَّخْرَ بِالْوَادِ 

9. Da samudawa wadanda suka fasa duwatsu a cikin Wadi.

وَفِرْعَوْنَ ذِي الْأَوْتَادِ 

10. Da Fir'auna mai turaku. 

الَّذِينَ طَغَوْا فِي الْبِلَادِ 

11. Wadanda suka ketare iyakarsu, a cikin garuruwa.

فَأَكْثَرُوا فِيهَا الْفَسَادَ 

12. Sai suka yawaita yin barna a cikinsu. 

فَصَبَّ عَلَيْهِمْ رَبُّكَ سَوْطَ عَذَابٍ 

13. Saboda haka Ubangijinka Ya zuba musu bulalar azaba. 

إِنَّ رَبَّكَ لَبِالْمِرْصَادِ 

14. Lalle ne, Ubangijinka Yana nan a mafaka. 

فَأَمَّا الْإِنسَانُ إِذَا مَا ابْتَلَاهُ رَبُّهُ فَأَكْرَمَهُ وَنَعَّمَهُ فَيَقُولُ رَبِّي أَكْرَمَنِ 

15. To, amma fa mutum idan Ubangijibsa Ya jarraba shi, wato Ya girmama shi kuma Ya yi masa ni'ima, sai ya ce; Ubangijina Ya girmama ni.

وَأَمَّا إِذَا مَا ابْتَلَاهُ فَقَدَرَ عَلَيْهِ رِزْقَهُ فَيَقُولُ رَبِّي أَهَانَنِ 

16. Kuma idan Ya jarraba shi, wato Ya kuntata masa arzikinsa, sai ya ce; Ubangijina Ya wulakanta ni.

كَلَّا بَل لَّا تُكْرِمُونَ الْيَتِيمَ 

17. A'aha! Bari wannan, ai ba kwa girmama maraya! 

وَلَا تَحَاضُّونَ عَلَى طَعَامِ الْمِسْكِينِ 

18. Ba kwa kwadaita wa junanku ga (tattalin) abincin matalauci! 

وَتَأْكُلُونَ التُّرَاثَ أَكْلًا لَّمًّا 

19. Kuma kuna cin dukiyar gado, ci na tarawa. 

وَتُحِبُّونَ الْمَالَ حُبًّا جَمًّا 

20. Kuma kuna son dukiya, so mai yawa. 

كَلَّا إِذَا دُكَّتِ الْأَرْضُ دَكًّا دَكًّا 

21. A'aha! Idan aka nike kasa nikewa sosai. 

وَجَاء رَبُّكَ وَالْمَلَكُ صَفًّا صَفًّا 

22. Kuma Ubangijinka Ya zo, alhali mala'iku na jere, safu- safu. 

وَجِيءَ يَوْمَئِذٍ بِجَهَنَّمَ يَوْمَئِذٍ يَتَذَكَّرُ الْإِنسَانُ وَأَنَّى لَهُ الذِّكْرَى 

23. Kuma a ranar nan aka zo da Jahannama. A ranar nan mutum zai yi tunani. To, ina fa tunani yake a gare shi!

يَقُولُ يَا لَيْتَنِي قَدَّمْتُ لِحَيَاتِي

24. Yana dinga cewa, Kaicona, ina ma dai na gabatar (da aikin kwarai) domin rayuwata!

فَيَوْمَئِذٍ لَّا يُعَذِّبُ عَذَابَهُ أَحَدٌ 

25. To, a ranar nan babu wani mai yin azaba irin azabar Allah. 

وَلَا يُوثِقُ وَثَاقَهُ أَحَدٌ 

26. Kuma babu wani mai dauri irin daurinSa. 

يَا أَيَّتُهَا النَّفْسُ الْمُطْمَئِنَّةُ 

27. Ya kai rai mai natsuwa!

ارْجِعِي إِلَى رَبِّكِ رَاضِيَةً مَّرْضِيَّةً 

28. Ka koma zuwa ga Ubangijinka, alhali kana mai yarda, abin yardarwa. 

فَادْخُلِي فِي عِبَادِي 

29. Sabobda haka, ka shiga cikin .

وَادْخُلِي جَنَّتِي 

30. Kuma ka shiga Aljannata.


Wadi: Shi ne "Wadil-kura" sunan wuri ne a kasar Siriya "Sham".




Hafiz Muhammad Sa'id
Haidar Center for Islamic Propagation
+234 803 215 6884 (Text only or (Line, Tango, Viber, Whatsapp, Telegram)
(hfazah@yahoo.com) (hfazah@hotmail.com)
comments Masu kallo
Suna:
Adireshin Email:
* ra'ayi: