bayyinaat

Published time: 06 ,March ,2017      09:11:16
Domin da ya kasance kamarta ne, da ya bukaci mai samarwa, don haka dole a tuke zuwa ga mai samarwar da ba samar da shi aka yi ba, wanda yake shi ne ainihin samuwa.
Lambar Labari: 70
Farkon abin da aka dora dalilan samuwar mahalicci a kansa shi ne dalilin sanin Allah ta hanyar kallon halittunsa. Da zamu yi la’akari da rana, da wata, da sama, da kasa, da koguna, da sauran halittu, da kuma tsarin da suke kunshe da shi, da mun san cewa akwai wanda ya tsara su a kan hakan.
Da mun kalli tsarin halitta da kuma hikimar da take tattare da su da zamu san cewa babu yadda zata kasance ita ta yi kanta ko kuma wanda yake shi ma yin sa aka yi , wanda yake kamarta, shi ya yi ta, don haka ne kenan dole ne ya kasance wannan ya gangaro ne daga samamme, mai kamala, da babu wani mai kama da shi a nau’in samuwarsa. 
Domin da ya kasance kamarta ne, da ya bukaci mai samarwa, don haka dole a tuke zuwa ga mai samarwar da ba samar da shi aka yi ba, wanda yake shi ne ainihin samuwa.

Dalilan Hankali
Dalilin Hankali Kan Samuwar Ubangiji
Akwai dalilai na tabbatar da samuwar Allah da dama wadanda a nan zamu kawo wasu daga cikinsu, kamar Dalilin mai tsarawa da mai tsari, da dalilin mai samarwa da samamme da sauransu.

Dalilin Mai Tsari A kan Mai Tsarawa
Wannan dalilin yana cewa ne, duk sa’adda ka ga abu mai tarsi to hakika akwai wanda ya tsara shi, kamar mutum ya ga gida a tsakiyar daji da aka kayata shi, ko wata mota a jeje da aka yi mata wata kira ta musamman, ko kuma ya ga gidan wata tururuwa a sahara da tsarin bangaren ma’aikata da na masu tsaro da kuma sito da wajan uwargijiyarsu, hankali kubutacce a nan ba abinda zai yi hukunci da shi sai wajabcin samuwar mai tsarawa da ya tsara wadannan abubuwan kamar yadda ya so bisa tsari. Don haka muna iya cewa; duk mai tsari yana da mai tsarawa gareshi .

A Lura Cewa
Tsararre (mai tsari) ba ya iya ba wa kansa tsari, da yana ba wa kansa tsari da ya zabi wani abu daban ba yadda yake ba, misali da mutum shi yake tsara kansa da bai so ya tsufa ba, ko ya yi rauni ya takwarkwashe, kamar yadda da haka ne cewa yana iya tsara kansa ko tsara wa kansa al’amuransa na halittawa da samarwa da ya aikata abin da ya so ya ga dama, don haka samun sabanin haka yana nuna mai tsarawa daban tsararre (abu mai tsari) daban, amma mai tsarawa shi ne yake tsara tsararre (mai tsari) yadda ya so, don haka tsari yana kasancewa kamar yadda mai tsarawa yake so ne, ba kamar yadda abu mai tsari ya so ba.
Don haka hankali yana tabbatar da cewa kowane tsararre (mai tsari) ko kuma tsarin kansa to akwai mai tsara shi.

Dalilin Samamme A kan Mai Samarwa
Wannan dalilin yana nuna cewa; duk sadda aka sami samamme da samuwarsa ba daga gareshi take ba, to akwai mai samarwa da ya yi shi.
Don haka wadannan duwatsu da koramu da tuddai da shuke-shuke da sauran halittu da muke gani dole ne akwai mai samarwa da ya samar da su.
Idan ka ga sawun rakumi to lallai akwai rakumi , domin ba yadda za a yi a same shi sai da dalili, wannan dalilin kuwa shi ne samuwar rakumi. Don haka samuwar mutane tana nuna lallai akwai wanda ya yi su, domin samuwarsu ba ta gaza samuwar sawun rakumi ba a cancanta da kuma kasancewar tana da mai samarwa, musamman idan muka duba kima da girman kyawu, da kamala, da tsari, da suke tattare da dan Adam fiye da na sawun rakumi.
An tambayi wata mata mai saka tana cikin saka cewa; menene dalilin samuwar Allah? Sai ta dakatar da sakar  ta ce: Ku duba dalilina. Wato matukar na dakata, to zare da allura da itacen saka duk zasu dakata, domin ba mai motsa su, amma idan na cigaba to sai aiki ya cigaba domin akwai mai motsar da su.
Kamar yadda balaraben kauye ya tabbatar da samuwar Allah ta hanyar cewa kashin rakumi yana nuna mana cewa akwai rakumi.
Ana iya kuma gani a fili cewa dalilin wannan mata ya saba da dalilin da muke magana akai kamar yadda na balaraben kauye ya yi daidai da dalilinmu. Ita wannan mata dalilinta zai iya zama na uku, sai ya zama shi dalili ne na mai motsi a kan cewa akwai mai motsarwa.

Dalilin Mai Motsi A Kan Mai Motsarwa
Ya gabata cewa mun kawo misali da wannan mata kamar yadda kuke iya gani, sannan kuma muna da karin wani misali da yake kama da na mai samarwa da samamme, da kuma dalilin mai tsarwa da mai tsari, da kuma mai motsarwa da mai motsi.
Wani malami sun taba musu da shi da wani mai musun samuwar Allah (s.w.t), sai suka yi alkawarin haduwa a rana ta musamman da lokaci ayyananne, amma sai malamin ya yi lati, har shi zindike ya yi tsammanin ko malamin ya gudu ne ya ji tsoron tattaunawar da zasu yi.
Bayan nan sai ga malamin ya isa, sai mai musun samuwar Allah ya ce da shi: Don me ka yi lati.
Sai malamin ya ce: Kun san gidana yana waccan gabar kogi ne, na zo zan hau jirgina sai wata iska ta taso ta kakkarya mini jirgin ruwana ta daidaita shi. Ina tsaye na rasa yadda zan yi sai ga wani abin mamaki! Katakwayen nan suna haduwa har suka hada jirgi ya dawo kamar yadda yake, sai na hawo shi na zo domin mu tattauna. Sai mai musun samuwar Allah ya fara yin isgili da dariya ga malamin yana cewa da shi: Da na dauka kai mai ilimi ne, na so in tattauna da kai, amma yanzu karancin hankalinka ya bayyana gareni, a yanzu akwai mai hankalin da zai yarda da maganarka cewa wai kwale-kwale ya gyara kansa?!
Sai malamin ya ce ai kai ne kafi kowa wauta, domin babu hauka irin naka, idan kwale-kwale ba zai iya yin kansa ba, to yaya wannan duniya maras iyaka a fadi zata samar da kanta ba tare da wani mai halittawa, mai samarwa, mai motsarwa ba.

Abin lura
Allah madaukaki ba samamme ba ne da ma’anar wanda aka samar, shi samamme ne da ma’anar mai samuwa kuma mai samarwa da ba shi da wanda ya samar da shi, kamar yadda Allah ba tsararre ba ne domin shi ba mai tsari ba ne, shi mai tsarawa ne, domin duk abin da yake mai tsari to dole ne ya zama yana da gabobi ko yanke-yanke da suka hada shi suka bayar da tsari, don haka Allah madaukaki ya kubuta daga yanke-yanke. Kamar yadda Allah ba ya motsi, amma shi mai motsarwa ne, domin duk mai motsi yana samun canje-canje ne, kuma Allah ya kubuta daga samun canje-canje.

Dalilin Tukewar Salsala
Idan muka ce akwai wani mutum mai suna "D” da yake da mahaifi wanda yake shi ne "C”, shi kuma yana da uba sunansa "B”, wanda shi kuma "B” yana da baba mai suna "A”, shin ba zai yiwu a samu uba na asali da tushe da wannan salsala ta tuke zuwa gareshi ba da zai zama shi ne uba na farko da babu wani uba sama da shi ba, shin zai yiwu a hankalce a ce tafiya ta tafi ta yadda babu uba da suka faro daga gareshi tun farko. Sannan kuma tunda kowane uba ba shi ya samar da kansa ba, ashe hankali ba zai yi hukunci da cewa dole ne a samu wanda ya samar da uba na farko a wannan salsalar ba. (A yi tunani)
Wani misalin shi ne; Idan da za a samu ziro (sifiri) daya ko biyu, ko uku har zuwa dubu, ko miliyoyi shin muna ganin zasu iya ba mu adadi idan ba a samu wata lamba da zata haifar da adadin ba, kamar karshensu mu sanya lamba daya ko biyu.
Haka nan ma yake ga halittu da samar da su aka yi, wadanda samuwar ba daga garesu take ba, dole ne su samu wani wanda shi ne ya samar da su tun asali domin su sami samuwa, in ba haka ba, kamar yadda tarayyar sifirori ba zasu iya ba mu wani adadi ba, haka ma tarayyar halittu matukar babu asali da suka samu samuwa daga gareshi babu wata samuwa da zata kasance garesu. Don haka tunda mun ga samammu to dole ne akwai samamme da yake shi samuwa zatinsa ce, ba wanda ya ba shi ita, wanda shi ne ya samar da sauran halittu.
Dokokin lissafi da Mantik suna iya yin amfani a yayin da muka yi amfani da su a cikin abin da yake bayani game da samuwa a irin wannan fage, don haka a yi tunani kan wannan dalili.

Dalilin Kewayo (Gewayo)
Idan muka ce "A” baban "B” ne, shi kuma "B” baban "C” ne, amma kuma "C” wanda yake jika a wannan misalin shi ne ya haifi "A” kakansa, shin hankali zai taba yarda da hakan.
Wannan ne ya sanya ake cewa; ba yadda za a yi kewayo ya yiwu a al’amarin halitta, don haka ba zai yiwu ba wanda aka samar ya samar da wanda ya samar da shi, domin wannan yana kai wa ga kewayo cikin al’amarin samar da halitta ne, al’amarin da yake mustahili a cikin hankali.
Wannan dalili yana tabbatar mana da cewa, wannan samuwar da muke gani ba daga wanda aka samar take ba, wajibi ne ta kasance daga wanda shi mai samarwa ne, ba a samar da shi, domin matukar wani daga cikin su ne ya samar da shi to za a samu kewayo, wanda yake al’amari ne mustahili kamar yadda muka gani.


Hafiz Muhammad Sa'id
Haidar Center for Islamic Propagation
+234 803 215 6884 (Text only or (Line, Tango, Viber, Whatsapp, Telegram)
(hfazah@yahoo.com) (hfazah@hotmail.com)

comments Masu kallo
Suna:
Adireshin Email:
* ra'ayi: