bayyinaat

Published time: 06 ,March ,2017      09:20:24
Muna ganin ni’imomin halitta da suka babaye mu, ni’imar rana, da ni’imar dare da ba mu san iyakacin su ba, ni’imar iska, da ruwa, da lafiya, da tunani, da zafi, da sanyi, da shiriya, ta hankali da ta wahayi, da sauran ni’imomi da ba zasu kirgu ba.
Lambar Labari: 71
Shin akwai inda muka taba ganin samamme da ya zamanto ba mai samar da shi, shin akwai wanda ya taba ganin bisa haka nan kawai wani abu ya samu ba daga wani da ya samar da shi ba, da wani zai ce maka wuri ya yi kazanta amma ba wani abu da ya yi sanadin hakan ko kuma wasu masu bata wajan, ko kuma ya zama wani yana da cutar malariya amma ba tare da wani dalili ba shin hankula gaba daya zasu iya yarda da hakan.
Da wani zai ce ya taba ganin wata mota a daji, ko wani gida a cikin sahara, ko kuma mu ga wata takarda da rubutu a kai amma sai wani ya zo ya ce mana: motar nan da gidan nan da rubutun nan su suka samar da kawukansu, da menene hankalinmu zai yi hukunci da shi? Don haka ne wannan dalili namu na kididdiga yake cewa; tunda ba a taba samun wani abu a cikin samuwa da ba shi da dalili ba, to wannan ka’ida ta mamaye dukkan wani wanda samuwarsa daga wani take, don haka duk ababan halitta suna da mai samar da su da ya yi su wanda shi kuma shi ne karshe da ba wanda ya samar da shi, domin in ba a samu tukewa zuwa gareshi a matsayinsa na wanda ba ya bukatar mai samarwa ba domin shi ya samar da kansa, to zamu samu rashin tukewar salsala, wannan kuwa dalili ya gabata a kansa a binciken dalilin tukewar salsala

Dalilin Mai Tasirantuwa A kan Mai Tasirantarwa
Duk wani fararre da wanda ya farar da shi, wannan kuwa yana afkuwa ne sakamakon wajabcin alaka tsakanin mai samarwa da wanda aka samar, ko kuma mai tasirantarwa da mai tasirantuwa, amma mun samu wasu daga masana kamar su Dabid Hume da suka yi musun irin wannan mai tasirantarwa da mai tasirantuwa, suka tafi a kan cewa al’amarin yana faruwa ne bisa haduwa da dacewa ba a bisa wajabcin alakarsu ba ne.
Raddin da zan yi wa Dabid Hume shi ne; Koda mun yarda da cewa alaka tsakanin mai tasirantarwa da mai tasirantuwa tana kasancewa a bisa dacewa da haduwa ne ta yadda ba sa rabuwa har abada, to matukar har abada haka ne ta yadda ba sa sabawa a tsakaninsu, to wannan ba zai cutar da wannan dalili ba.
Don haka koda alakar wuta da kuna ta kasance bisa dacewa ne ta haduwa tsakanin samuwar wuta da kuna, matukar har abada haka ne wannan ba zai iya cutar da dalilinmu ba. Don haka sai ya zama bisa dacewa ta har abada ne da ba ta sabawa samuwar Allah (s.w.t) ta haifar da samuwar wadannan halittu gaba daya. A cikin musulmi akwai ash’arawa da Nicolas Malebranche daga masu tunani kuma malamin Falsafa a yammacin duniya da suke da tunani makamancin wannan na musun tasiri tsakanin mai tasirantarwa da mai tasirantuwa.
Ash’arawa daga cikin musulmi kuma da Nicolas Malebranche daga malaman yamma sun tafi a kan cewa; duk sa’adda aka samu alaka ta samuwa tsakanin abu biyu kamar wuta da zafi to wannan alakar ba ta hanyar tasirantarwa da tasirantuwa ba ne, domin sun yi musun alakar tasiri tsakanin ababan halitta, kamar ruwa da kashe kishirwa, ko wuta da zafi, suna ganin wuta ba ta zafi kamar yadda magani ba shi da waraka, suna masu imani da cewa abin da yake faruwa shi ne; duk sadda wuta ta samu sai Allah ya haifar da zafi tare da ita, haka ma duk sadda aka samu magani sai Allah ya sanya masa warkarwa, ba tare da wata rawa da wuta ko magani zasu taka ba, wannan kuma al’amari ne da rashin ingancinsa yake a fili.

Dalilin Godiya
Yawancin littattafai suna kawo wannan a matsayin dalilin da yakan tunkuda mu domin mu yi tunani game da samuwar Allah madaukaki, amma ni zan yi amfani da shi a matsayin kafa dalilin samuwar Allah kai tsaye;
Muna iya cewa; muna ganin ni’imomin halitta da suka babaye mu, ni’imar rana, da ni’imar dare da ba mu san iyakacin su ba, ni’imar iska, da ruwa, da lafiya, da tunani, da zafi, da sanyi, da shiriya, ta hankali da ta wahayi, da sauran ni’imomi da ba zasu kirgu ba.
A yanzu wadannan ni’imomi ba zasu sanya mu tabbacin cewa akwai wanda yake kwararo su zuwa garemu ba, ashe idan ba mu yarda da cewa akwai mai kwararo wadannan ni’imomi ba kare da idan ya ga kasusuwa sun fado daga sama, da ya tabbatar da cewa ba yadda za a yi kasusuwa su jefo kansu yakan waiwaya domin ganin waye ya jeho su domin ya gode masa, ba zai fi mu hankali ba kenan.
Kuma shin kare da ake ba shi kasusuwa amma ya kwana yana gadi domin gode ni’imomin wadannan kasusuwa da ake ba shi yana lashewa ya dangana da su, ba zai fi mu tunani da hankali ba a matsayinmu na mutane idan ba mu gode ba.   

Dalilin Hattara
Wannan dalilin ana amfani da shi kamar yadda ake amfani da na samansa, amma na yi amfani da shi kai tsaye a matsayin dalili maimakon abin da zai sanya mu mu shiga bincike da neman dalili kamar yadda na yi amfani da na samansa ta hakan, ta hanyar cewa;
Da yawa muna ganin halaka da tabewa da mummunar makoma tana samun masu kin Allah da saba masa tun a nan duniya, kuma muna ganin darasin da yake samun rayuwarsu da makomarsu mummuna, ashe kenan wannan yana iya sanya mu, mu san cewa da akwai mahallici mai daukar fansa da ukuba ga masu kinsa da keta huruminsa, wannan dalili duk da an dauke shi daga daukar darasin abin da yake wakana amma zai iya zama mai karfafawa kamar yadda mai biyo masa yake.
Idan ya kasance muna ganin darasi kamar mu ga gawar bayin Allah da suka yi shahada a tafarkinsa ta yi shekaru dubu amma har yanzu jini yana zuba, kuma mu ga makiyansa cikin minti daya tana zubar da tsutsa, shin wannan ba ya iya zama mana tabbacin akwai Allah da ya dauki nauyin yin hakan, domin jiki ba shi da bambanci da jiki idan haka ne.
Don haka idan muna ganin mai bayar da labarin cewa akwai ‘yan fashi a hanya yana sanya mu kin bin wannan hanyar, shin ba zai zama wauta ba muna ganin irin wadannan darussa sannan sai mu rufe idonmu mu ki yarda da samuwar mahalicci mai iko da ya dauki nauyin wadannan ayyukan. 
Hada da cewa muna ganin mutanen da suka fi mu hankali da tunani na daga annabawa (a.s) da wasiyyansu (a.s) duk ba wanda ya saba a cikinsu a kan maganar cewa akwai mahalicci.
 
Dalilin Gamsarwa
A nan muna son cewa ne a yi imani da mahalicci da aiki da hakan koda an kaddara da cewar babu shi ya fi zama abin hankalta a kan rashin yarda da hakan, domin idan an koma masa; idan an kaddara babu shi to da mu da wadanda ba su yi imani da shi ba mun zama daya, kuma wahalar da muka sha wajan bautarsa ba zata cutar da mu ba, amma idan akwai shi fa! kenan mun tsira su kuma sun halaka, kuma Imam Sadik (a.s) ya kawo wannan dalili ga Addisani.
William James daya daga cikin jigan-jigan Pragmatism da ire-irensa suna ganin wannan dalili a matsayin abin da zai taimaka mana wajan tabbatar da cewa lallai addini wani abu ne da a hankalce yana da kyau a bi shi, amma a sani kallon Willian da kallonmu game da wannan dalili ya saba, domin su suna ganin wannan zai sa a ga mai addini akalla ba yana hauka ba ne, wato riko da addini da ya yi abu ne da hankali zai iya karbarsa, amma mu muna ganin cewa addini wani abu ne da ya zama tilas a yi riko da shi domin mahallici a wajanmu samamme ne, dalilin a wajenmu domin karin gamsar da wanda bai yi imani da Allah ba ne, da kuma karfafawa ga dalilanmu a kan waninmu, ba kamar yadda su wadancan ‘Yan maslahar hankaltuwar riko da addini suka tafi a kai ba ne.

Dalilin Shari’a
Dalilin Shari’a Na Tabbatar Da Samuwar Allah
Wannan dalilin yana zuwa bayan an tabbatar da samuwar Allah ta hanyar hankali ne, ayoyin kur’ani masu yawa sun zo game da tabbatar da samuwar Allah madaukaki, kamar yadda ruwayoyi masu yawa suka zo daga hadisan Manzon Allah da Ahlul Bait (a.s) game da hakan.
Samuwar Allah a cikin kur’ani mai girma wani abu ne wanda kur’ani ya dauke shi a matsayin bayyananne da hankli kubutacce ingantacce ba ya musun sa, shi ya sa a wurare da dama ya yi nuni da hakan, a wasu wurare kuma yakan zo da sigar tamabya ne, kamar fadinsa madaukaki: "Shin akwai kokwanton samuwar Allah” ? Da sauran ayoyi masu yawa da suka zo game da bayanin tauhidi, don haka ya fi karfafawa kan tauhidin kadaita shi da ibada, ko ya yi nuni yana mai karfafa a kan kadaita shi cikin tafiyar da al’amuran bayi, ko kadaita shi ta hanyar kore masa abokin tarayya. Abin da surar Fatiha ta kunsa babban misali game da hakan, don haka sai mai karatu ya koma zuwa ga tafsirinta. 
Daga cikin dalilai da kur’ani ya kafa a kan samuwar Allah akwai aya da ta kunshi dalilin samamme a kan mai samarwa, da dalilin mai tsari a kan mai tsarawa da fadinsa madaukaki:
"Hakika a cikin halittar sammai da kasa, da sabawar dare da rana, da jirage da suke gudana a kogi (dauke) da abin da yake amfanar mutane, da abin da Allah ya saukar daga sama na daga ruwa sai ya rayar da kasa da shi bayan mutuwarta, kuma ya watsa a cikinta daga dukkan dabbobi, da juyawar iskoki da girgije horarre a tsakanin sama da kasa, hakika akwai ayoyi ga mutane masu yin hankali” .




Hafiz Muhammad Sa'id
Haidar Center for Islamic Propagation
+234 803 215 6884 (Text only or (Line, Tango, Viber, Whatsapp, Telegram)
(hfazah@yahoo.com) (hfazah@hotmail.com)
comments Masu kallo
Suna:
Adireshin Email:
* ra'ayi: