bayyinaat

Published time: 06 ,March ,2017      09:25:16
Kasancewarsa ba shi bangarori da yanke-yanke da suka hada shi, wato sai ya zama tilo a cikin samuwarsa, wannan shi ne ake cewa da shi “Ahad”. Kore masa bangarori yana iya kasancewa ta hanyoyi hudu;
Lambar Labari: 72
Kadaitakar ubangiji madaukaki
Bayan mun gama bincike game da samuwar mai samarwa, mai tsarawa, mai motsarwa ga talikai baki daya, abu muhimmi na gaba shi ne tabbatar da cewa shi wannan mai siffofin guda daya ne.

Kadaitaka A Cikin Zati
Kadaitaka a zatin Allah tana da ma’ana biyu:
Na daya; Kasancewarsa ba shi bangarori da yanke-yanke da suka hada shi, wato sai ya zama tilo a cikin samuwarsa, wannan shi ne ake cewa da shi "Ahad”. Kore masa bangarori yana iya kasancewa ta hanyoyi hudu;
Yanke-yanke na hankali
Kamar yadda mukan iya cewa a hankalci, bangarori biyu da suka hadu suka yi shi, kamar yadda mutum yake da su. Mutum ya hadu ne daga abin da ya yi tarayya da sauran dabbobi a cikinsa na rayuwa da kuma kebantuwa da hankaltuwa a tsakaninsu.

Yanke-yanke na kaddarawa
Kamar a kaddara cewa zai yiwu a tsattsaga ubangiji gida-gida, kamar yadda idan an kaddara akwai jiki zai iya kasuwa zuwa fadinsa da tsayinsa da kuma tudunsa. Kamar jiki irin na ilimin kimiyya da kere-kere.
Yanke-yanke na zahiri
Wannan su ne yanke-yanke da kuma guntaye na abin da yake jiki ne da muke iya gani, kamar guntayen katakon da aka hada aka yi kujera da shi.
 
Yanke-yanke na samuwa
Wadannan su ne bangarori da suka hadu suka samar da wani abu, kamar hakikanin samuwar mutum da kuma iyakokin samuwar tasa, wannan shi ne bangarori da falsafa take bincike a kansu a hankalce, kuma halittu suna siffantuwa da su.
Sakamakon haka dukkanin wadannan yanke-yanken Allah ya kubuta daga siffantuwa da su, domin da ya kasance yana da gabobi da ya bukace su, wannan kuwa yana kore kasancewarsa ubangiji. Haka nan da yana da gabobi da samuwarsu da tattaruwarsu domin su hada shi ta rigayi samuwarsa, alhalin madaukaki ne shi da babu wani abu da ya rigaye shi.

Na biyu; Shi ne kasancewar ubangiji (s.w.t) ba shi da abokin tarayya a cikin dukkan samammu, abin da ake kira da "Wahid”. Idan muka duba sosai cikin ma’anar ubangiji daya zamu tabbatar da cewa shi kadai ne wanda ba shi da iyaka, domin kasancewarsa maras iyaka yana kore samuwar wani ubangijin na biyu. Idan kuwa aka samu wani ubangiji to kenan ya zama mai iyaka, alhalin shi ba shi da iyaka.
Kamar yadda muna iya cewa; da an sami wani ubangiji bayansa da ya kasance da siffofi irin nasa, da ya zama kamarsa, da ya zama yana da mai kishiyantarsa a dukkan kamala, wannan kuma yana kore kasancewarsa ubangiji.

Dalilin Shari’a A kan Kadaitakar Zati
Kur’ani mai girma yana cewa: "Wani abu bai zama kamar tamkarsa ba” . Yana kuma cewa: Ka ce shi ne Allah makadaici. Allah wanda yake sidif (ba shi da yanke-yanke). Bai haifa ba kuma ba a haife shi ba. Kuma babu wani da ya kasance tamka a gareshi” .  


Hafiz Muhammad Sa'id
Haidar Center for Islamic Propagation
+234 803 215 6884 (Text only or (Line, Tango, Viber, Whatsapp, Telegram)
(hfazah@yahoo.com) (hfazah@hotmail.com)

comments Masu kallo
Suna:
Adireshin Email:
* ra'ayi: