bayyinaat

Published time: 06 ,March ,2017      09:32:55
Ku kuna cewa Dadadde Madaukaki (s.w.t) ya hade da Masihi Dansa (a.s). Me kuka nufi da wannan magana?. Shin kuna nufin Dadadde ya zama Fararre saboda wannan Fararren da ya hade da shi wanda shi ne Isa (a.s) ko kuna nufin Fararren da yake shi ne Isa (a.s) ya koma Maras farko kamar samuwar Dadadde wanda yake shi ne Allah?.
Lambar Labari: 74
Sa’annan sai ya fuskanci Kiristoci ya ce da su: Ku kuna cewa Dadadde Madaukaki (s.w.t) ya hade da Masihi Dansa (a.s). Me kuka nufi da wannan magana?. Shin kuna nufin Dadadde ya zama Fararre saboda wannan Fararren da ya hade da shi wanda shi ne Isa (a.s) ko kuna nufin Fararren da yake shi ne Isa (a.s) ya koma Maras farko kamar samuwar Dadadde wanda yake shi ne Allah?. Ko kuma ma’anar ya hade da shi ya shiga jikinsa a wajanku yana nufin ya kebance shi da karama da girmamawa ne wacce bai girmama waninsa da irinta ba?. Idan kuka ce: Dadadde ya koma Fararre to kun rushe, domin Dadadde bai yiwuwa ya juya ya koma Fararre. Idan kuma kuna nufin Fararre ya koma Dadadde to kun yi warwarar magana domin mustahili ne Fararre ya koma Dadadde. Idan kuma kuna nufin ya hade da shi domin ya kebance shi ya zabe shi a kan sauran bayi to kun yi furuci da cewa Isa (a.s) Fararre ne da ma’anar ya hade shi saboda haka, domin idan Isa (a.s) ya kasance Fararre Allah (s.w.t) ya kasance ya hade da shi da ma’anar ya sanya shi Mafificin halitta a wajansa to Isa (a.s) ya zama daya daga cikin fararru da wannan ma’ana, wannan kuwa sabanin abin da ku kuke bayyanawa ne.
Sai Kiristocin suka ce: Ya Muhammad! Yayin da Allah ya bayyanar da abubuwan mamaki a hannun Isa (a.s) to ya rike shi da ne ta hanyar girmamawa. Sai Manzo (s.a.w) ya ce: Ai kun ji abin da na gaya wa Yahudawa a irin wannan ma’ana da kuka ambata, sannan ya maimaita abin da ya fada wa Yahudawa dalla -dalla, sai suka yi shiru banda mutum daya a cikinsu da ya ce da shi: Ya Muhammad! Shin ba kuna cewa Ibrahim (a.s) Khalilul-Lahi ba? Sai Manzo (s.a.w) ya ce: Mu Muna cewa hakan. Sai ya ce: Idan kuna cewa haka domin me zaku hana mu fadar waccan maganar? Sai Manzo (s.a.w) ya ce: Maganganun ba su yi kama da juna ba, domin ma’anar Khalilul-Lahi an ciro shi daga Khulla wato Bukata da Talauci domin shi ya kasance Mabukaci zuwa ga Ubangijinsa ne, Mai yankewa zuwa gare shi, Mai kamewa ga barin waninsa, wannan a lokacin da aka jefa shi wuta da manjanik (majaujawa) ne sai Allah ya aika Jibra’il (a.s) da ka je ka riski bawana, sai ya zo ya riske shi a cikin iska, Ya ce da shi: Ka umarce ni da duk abin da kake so hakika Allah ya aiko ni da in taimake ka, Sai Ibrahim (a.s) ya ce da shi: "Hasbiyal-Lahu Wa ni’imal Wakil”, Ni ba na tambayar wani wata bukata sai Shi, ba na bukata sai gare Shi". Saboda haka sai ya kira shi da Khalilinsa wato Mabukaci Mai yankewa daga komai sai zuwa gare shi, idan ya zama ma’anar Khulla wato ya tsaya a kan wasu sirri da babu wanda ya same su, ma’anar Khulla zata zama masani da sirrinsa, a nan babu wani kamanta shi da halittarsa. Shin ba kwa gani ne cewa idan bai yanke zuwa gare shi ba bai zama Khalilinsa ba haka ma idan bai san sirrinsa ba bai zama Khalilinsa ba? Amma wanda mutum ya haifa ko da kuwa ya wulakanta shi ya nesantar da shi daga gare shi ba ya fita daga kasancewa dansa ne, domin ma’anar haihuwa ta tsayu da wannan. Sa’anan idan ya wajaba domin ya ce da Ibrahim (a.s) Khalili ku kiyasta ku ce da Isa (a.s) dansa ya wajaba kenan ku ce da Musa (a.s) dansa domin mu’ujizar da take tare da shi ba ta gaza ta Isa (a.s) ba. Sai ku ce Musa (a.s) shi ma dansa ne, kuma ya halatta inda haka ne ku ce da shi: Shaihin Allah ko Shugabansa ko Amminsa ko Amirinsa kamar yadda na riga na gaya wa Yahudawa hakan.
Sai wadansunsu suka ce: Ai a cikin Littafi saukakke hakika Isa (a.s) ya ce: "Ni zan tafi zuwa ga Babana kuma Babanku”. Sai Manzon Allah (s.a.w) ya ce: Idan kun kasance kuna amfani da Littafin ne, to a cikinsa an ce: "Ni mai tafiya ne zuwa ga Babana kuma Babanku”, Idan haka ne ku ce da wadanda Isa (a.s) ya yi magana da su gaba daya ‘Ya’yan Allah ne kamar yadda Isa (a.s) yake dansa ta fuskar da Isa (a.s) yake dansa. 
Sa’annan abin da yake cikin wannan littafin yana karyata abin da kuke rayawa cewa Isa (a.s) ya zama dansa ta fuskacin kebanta, domin kuna cewa shi dansa ne ta fuskacin kebantarsa da ya yi da abin da bai kebanci wani da shi ba, sannan kun sani cewa abin da ya kebanci Isa (a.s) da shi bai kebanci wadannan mutane da Isa (a.s) ya ce da su "Ni mai tafiya ne zuwa ga Babana kuma Babanku” da shi ba, sai wannan ya nuna cewa bai kebanta da Isa (a.s) ba domin ya tabbata a wajanku cewa Isa (a.s) ya gayawa wanda bai da wannan matsayi irin nasa, sai kuka hakaito maganar Isa (a.s) kuka yi tawilinsa ba bisa ma’anarsa ba, domin shi da ya ce: "Ni mai tafiya ne zuwa ga Babana kuma Babanku”  abin da yake nufi ba shi ne abin da kuka tafi a kai ba. Me ya sanar da ku ko yana nufin ni mai tafiya ne zuwa ga Babana Adam (a.s) ko zuwa ga Nuhu (a.s) kuma Allah zai daukaka ni zuwa gare su ya hada ni tare da su, tare da Adam Babana kuma Babanku, kai ba abin da yake nufi sai wannan. Imam Sadik (a.s) ya ce: Sai Kiristoci suka yi shiru suka ce: Ba mu taba ganin mai wuyar kayarwa mai hujjoji masu karfi irinka ba, zamu tafi mu duba al’amuranmu.



Hafiz Muhammad Sa'id
Haidar Center for Islamic Propagation
+234 803 215 6884 (Text only or (Line, Tango, Viber, Whatsapp, Telegram)
(hfazah@yahoo.com) (hfazah@hotmail.com)

comments Masu kallo
Suna:
Adireshin Email:
* ra'ayi: