bayyinaat

Published time: 31 ,March ,2017      16:59:50
Wahayi a ma’anarsa ta isdilahi yana nufin abin da ake yi wa annabawa da manzanni sakonsa na daga zance ko ilhami da ake kimsa musu (a.s). Kuma shi hanya ce da Allah yake sanar da mutum ubangijinsa da kansa da shiriyarsa domin ya tsara rayuwarsa da zamantakewarsa da sauran halittu, da kuma yadda zai fuskanci ubangijinsa.
Lambar Labari: 79
Wahayi a ma’anarsa ta isdilahi yana nufin abin da ake yi wa annabawa da manzanni sakonsa na daga zance ko ilhami da ake kimsa musu (a.s). Kuma shi hanya ce da Allah yake sanar da mutum ubangijinsa da kansa da shiriyarsa domin ya tsara rayuwarsa da zamantakewarsa da sauran halittu, da kuma yadda zai fuskanci ubangijinsa.
Nau’o’in wahayi
Ta hanyar sauti da Annabi yakan ji
Ta hanyar mala’ika da yake jiyar da shi
Ta hanyar jefawa ga Annabi a cikin ransa
Ta hanyar mafarki
Wahayi Ga Manzon Rahama (s.a.w)
Allah madaukaki ya shirya annabinsa kuma ya tarbiyyantar da shi da tarbiyya mai kyau, ba domin komai ba sai domin saninsa da nauyin da zai dora masa na shiryar da dan Adam da tseratar da shi zuwa ga tafarki madaidaici, ya kasance farkon nau’in wahayin da ya fara ga manzon rahama shi ne ta hanyar mafarki na gari[1].
Daga cikin hanyoyin tarbiyyantarwa ga Annabi da ubangijinsa ya shirya masa sun hada da;
Ilhama da mafarkin gaske da yake nuna masa zahirin abin da yake faruwa a gaske
Soyantar masa da halwa da kebewa domin ya yi nazari cikin samuwar ubangiji da duniyoyin da ya samar da kuma fuskanta zuwa ga Allah madaukaki
Saukar Wahayi
A shekara ta 610 miladiyya ne Allah madaukaki ya saukar da wahayi ga manzo a watan Ramadan mai girma ya saukar masa da farkon surar alak.
Bayan nan ne annabin girma da daraja ya koma zuwa ga iyalansa yana mai dauke da wannan nauyi da ya kasance yana jiransa.
Imam Al-hadi (a.s) yana cewa:
Yayin da manzo (s.a.w) ya bar fatauci zuwa Sham kuma ya yi sadaka da dukkan abin da Allah ya arzuta shi da shi na dukiya, ya kasance yana tafiya kogon hira kowace rana yana hawa kansa yana duba zuwa ga ni’imomin rahamar Allah, da kuma nau’in kayatarwar rahamarsa da kyawawan hikimominsa, yana mai duba zuwa ga sama da kuma gefen kasa, da koguna, da dazuzzuka, da sasanni, yana mai tunawa ga ubangiji da wadannan ni’imomi, yana kuma bauta ga Allah hakikanin bauta.
Yayin da ya kai shekara arba’in sai Allah ya kalli zuciyarsa ya ga ita ce mafi kamalar zuciya, mafi haskenta, mafi biyayya, mafi tsoron Allah, mafi kaskan da kai, sai ya yi umarni aka bude kofofin sama Muhammad yana kallo zuwa garesu, kuma ya umarci mala’iku suka sauka yana ganinsu, kuma ya yi umarni da saukar da rahama daga kasan al’arshi zuwa kansa, ya ga Jibril dawisun mala’iku (a.s) yana mai damfare da haske; ya sauka gareshi ya kama damtsensa ya girgiza[2] ya ce: ya Muhammad! Ka karanta, ya ce: me zan karanta? …  (Ya karanta masa surar alak har zuwa aya ta biyar).
Sai ya yi wahayi gareshi da abin da Allah ya yi masa wahayi sannan sai ya hau sama.
Muhammad (s.a.w) ya sauka daga dutse, girman ubangiji ya riga ya mamaye shi, kuma zazzabi mai zafi ya same shi… ga tsoro mai tsanani ya kama shi na gudun kada kuraishawa su karyata shi a labarin da zai ba su, su kuma danganta shi da hauka, kuma da cewa shaidanu suna bujuro masa, alhalin ya kasance tun farko shi ne mafi hankalin halittar Allah, ma fi girman halittunsa, ma fi kin abu a wjansu shi ne shaidan da kuma ayyukan mahaukata da zantuttukansu.
  Sai Allah ya so ya yalwata kirjinsa, ya kuma karfafi zuciyarsa, ya sanya duwatsu da rairayi da kwararo suka yi magana, duk abin da ya hadu da shi daga cikinsu sai ya kira shi ya ce masa: Aminci ya tabbata gareka ya Muhammad, aminci ya tabbata gareka ya masoyin Allah, aminci ya tabbata gareka ya manzon Allah, ka yi albishir, Allah ya fifita ka, ya kawataka, ya adontar da kai, kuma ya girmama ka akan sauran talikai gaba daya na farko da na karshe, kada maganar kuraishawa na cewa kai mahaukaci ne ya bakanta maka rai, ko fadinsu na cewa; kai ka fitinu daga addini, domin mai fifiko shi ne wanda Allah ya fifita.
  Kada kirjinka ya yi kunci don karyatarwar kuraishawa da wawayen larabawa gareka, da sannu ubangijinka zai ba ka matsayin mafi daukakar karamomi, kuma ya daga ka zuwa mafi daukakar darajoji, kuma ya ni’imta masoyanka, ya faranta masu rai da wasiyyinka Ali dan Abu Talib (a.s), kuma ya yada iliminka a cikin bayi da garuruwa da mabudanka da kuma kofar birnin hikimarka: Ali dan abu Talib, kuma da sannu Allah zai sanyaya idanunka da ‘yarka Fatima (a.s), da sannu za a fitar daga gareta da kuma daga Ali (a.s); (‘ya’ya) Hasan da Husain (a.s) shugabannin samarin aljanna, da sannu Allah zai yada addininka a duniya, kuma ya girmama ladan masoyanka da kai da dan’uwanka, da sannu zai sanya tutar yabo a hannunka sai ka sanya shi a hannun dan’uwanka Ali (a.s) sai duk wani Annabi da siddiki da shahidi ya zama a karkashinsa, ya kuma zama jagoransu gaba daya zuwa aljannar ni’ima.
Abin Lura
Zan so in yi nuni da cewa manzo (s.a.w) ba ya ji tsoron mala’ika ba ne kamar yadda wasu suke kawowa, abin da yake jin tsoro shi ne kada shaidanu su bata kiran ta hanyar bata shi ko kuma bata hanyoyin kiransa. Amma sauran bayanai da darussa muna iya barin mai karatu da ruwaya domin ya yi nasa tunani.
Kira A Boye
 Yana daga hikimar da kiran Manzon rahama ya doru a kanta ita ce; kawo canji a duniya gaba daya domin gyara ‘yan’adamtaka da tseratar da mutane daga zalunci, da kafirci, da barna, kuma da dogaro da darasin da kiran manzo ya dauka na tarihin abin da ya faru a tarihin annabawa (a.s) da suka gabata ta yadda kafirai suka yi wa da’awarsu kwaf daya tun kafin ta je ko’ina. Sai manzon tsira ya fara kiransa a boye[3]; farkon wanda ya yi imani da shi su ne imam Ali (a.s) da sayyida Khadiza (a.s), sannan sai Zaid Dan Harisa.
 Bayan kammalar wannan al’amari na fara kiran mutanen gidansa, sai kuma ya kira danginsa da sauran na kusa da shi da abokansa wadanda yake da aminci da su, wannan hanyar ta kira a boye da kuma dauki daidai ta taimaka wajan kafa mutane na farko masu dauke da tunani irin na kiran manzo (s.a.w) da suka dauki nauyin kare kiran da kuma yada shi, kamar yaddda karancinsu da imaninsu suka taimaka wajan tarbiyyantar da su domin tunkarar irin wannan aiki mai wahala.
 Sun kasance suna boye imaninsu suna ibada a boye, ba sa bayyanar da musuluncinsu, kuma wannan marhala ta boye kiran ta dauki tsawon shekaru uku, wanda a cikinta aka tarbiyyantar da mutane masu yawa a makarantar farko ta musulunci wato gidan Arkam Almahzumi, masu tarihin suna cewa; a wannan marhala adadin musulmi ya kai arba’in.
Kiran Danginsa A Bayyane
Bayan shekaru uku sun gabata, sai kiran manzo (s.a.w) ya shiga sabon fagen kiran na fili da bayyanarwa, a wannan marhalar ya fara da makusantansa ne na jini, hikimar da hakan ta kunsa ita ce;
Kada a ce; don me bai kira makusantansa ba idan ya kansance kiran nasa alheri ne.
Bukatar kariya domin samun karfin yada da’awarsa.
Sai manzo (s.a.w) ya sanya imam Ali (a.s) da ya yi abinci ya kira dukkan makusantansa na Bani Hashim wadanda yawansu ya kai mutun arba’in da daya ko ba daya, sai suka ci abincin suka sha abin shan da yake na mutum daya ne, amma ya ishe su su duka gaba daya, amma kafin manzo (s.a.w) ya yi magana sai Abu lahab ya nuna cewa wannan ciyarwar sihiri ce, sai manzo (s.a.w) ya ki yin magana, kuma ya sanya imam Ali ya sake shirya musu wani abincin a rana ta gaba, bayan sun ci sun sha sai ya ce musu: "Ya Bani Abdulmudallib ni mai gargadi ne a gareku daga Allah (s.w.t) ni na zo muku da abin da wani daga larabawa bai zo da shi ba, idan kuka bi ne zaku shiriya ku rabauta ku tsira, wannan liyafa Allah ne ya umarce ni da ita; sai na yi muku ita kamar yadda isa dan Maryam (a.s) ya yi wa mutanensa;; wanda ya kafirce daga cikinku bayan wannan to Allah zai azabtar da shi azaba mai tsanani da bai azabtar da wani daga talikai da irinta ba, ku ji tsoron Allah ku ji abin da nake gaya muku, ku sani ya Bani Abdulmudallib: Allah bai aiko wani manzo ba sai ya sanya dan’uwa da yake waziri kuma wasiyyi kuma mai gado garshi daga ahlinsa, hakika ni ma ya sanya mini waziri kamar yadda ya sanya wa annabawan da suka gabace ni, kuma Allah ya aiko ni zuwa ga mutane gaba daya, ya saukar mini da ((Ka gargadi danginka makusanta)) da jama’arka masu tsarkake zuciya, kuma Allah ya ba ni labarinsa, kuma ya gaya mini sunansa, amma ni ina kiranku, ina kuma yi muku nasiha, ina bujuro muku; domin kada ku samu hujja bayan wannan, ku makusantana ne kuma jama’ata ta kusa, wane ne daga cikinku zai yi rigo zuwa ga wannan a kan cewa ya zama dan’uwana a al’amarin ubangiji, kuma ya taimaka mini a kan wannan al’amari a kan ya kasance dan’uwana, wasiyyina kuma halifana a bayana a cikinku. Sai mutanen suka tage (jugum) gaba dayansu, sai Ali (a.s) ya ce: Ni ne ya annabin Allah zan kasance mai taimakonka a kansa. Imam Ali (a.s) yana cewa: Sai ya rike kafadata, sannan sai ya ce: Hakika wannan dan’uwana ne, wasiyyina kuma halifana a cikinku ku ji daga gareshi kuma ku bi.
Sai mutanen suka rika dariya, suna cewa da Abu Talib: ya umarce ka ka ji daga danka ka bi. Sai Abu Talib (a.s) ya ce: Wallahi zamu taimaka masa, sannan zamu karfafe shi, ya dan dan’uwana idan kana son ka yi kira zuwa ga ubangijinka ka sanar da mu domin mu fito tare da kai da makamanmu”[4].
Bayan wannan ne labari ya yadu tsakanin kuraishawa da cewa Muhammad yana da’awar ana yi masa magana daga sama, sai wasu suka fara isgili, wasu suka fara tuhuma, sai Allah ya umarce shi da ya bayyanar da kira ga dukkan mutane da fadinsa: "Ka cigaba da abin da aka umarce ka, ka kawar da kai daga mushrikai, mu mun isar maka masu isgili”. Duba zuwa ga wannan aya, ina ganin zamu iya kiran wannan marhala a matsayin ta uku a kiran manzo (s.a.w), wato muna iya jera su kamar haka:
Marhalar boyewa
Marhalar bayyanarwa ga dangi
Marhalar bayyanarwa ga mutane
Kiran Mutane A Bayyane
Ruwayoyi da dama game da yadda ya bayyanar da da’awarsa ga mutane suna da yawa, amma zamu kawo daya daga ciki ne, an rawaito cewa: manzo (s.a.w) ya tsaya a kan Safa, sanna sai ya kira kuraishawa; sai suka taru, sannan sai ya ce da su: "Shin da zan ba ku labari cewa wasu mahaya sun kawo muku hari ta kan wannan dutsen zaku gasgata ni?. Suka ce: Na’am, kai a wajanmu ba abin tuhuma ba ne, kuma ba mu taba jin karya daga gareka ba. Sai ya ce: To ni mai gargadi gareku (daga wajan Allah) daga azaba mai tsanani. Sai Abu lahab ya mike tsaye ya ce da shi: Kaiconka! Yanzu saboda wannan ka tara mutane?. Sai mutane suka watse, sai Allah ya saukar da: Surar lahab[5].
Kuraishawa sun dauki matakin farko domin tsayar da wanna da’awa ta manzo (s.a.w) da tayin abubuwa gun Abu Talib (a.s) a kan cewa sharadin shi ne manzo (s.a.w) ya tsayar da kiransa kuma ya janye maganarsa, wadannan abubuwa suna hada da:
Ba shi dukiya mai yawa
Ba shi mulki a tsakaninsu
Ba shi mata kyawawa da yake so
Sai Abu Talib (a.s) ya tambayi manzo (s.a.w) domin ya ji menene zai fada, amma sai manzo ya ba shi amsa cewa; Da zasu dora rana a hannunsa na dama, wata a na hagu da ba zai bari ba, don haka ne ma Abu Talib (a.s) ya ce masa: Ka tafi ya dan dan’uwana ka ci gaba da abin da kake so, wallahi ba zan mika ka a kan wani abu ba har abada[6].
Da kuraishawa suka ga wannan ba ta ba su abin da suke so ba sai suka koma da jifa da kalmomi da isgili da tuhumomi masu yawa kan Annabi (s.a.w) da kiransa da abubuwa mabanbanta kamar:
Jifansa da hauka
Jifansa da sihiri
Sanya kaya a kofar gidansa
Wulakanta shi
Azabtar da wadanda suke yin imani da shi
Da manzo ya ga yawancin masu musulunta ba su da kariya kamar yadda yake da ita daga Abu Talib (a.s) sai ya umarce su da yin hijira zuwa Habasha, yana mai gaya musu: "A Habasha akwai wani sarki da ba a zaluntar wani gunsa”.
Bayan wannan hijira ta farko zuwa Habasha ne da jagorancin Ja’afar dan Abu Talib (a.s) sai kuraishawa suka yi kokarin dawo da su daga wajan sarkin Habasha amma ba su ci nasara ba, al’amarin da ya ba su haushi suka sanya takunkumi mai zafi kan Bani Hashim da ya yi sanadiyyar mutuwar Abu Talib da sayyida Khadiza (a.s) a wannan yanayi mai wahala da yunwa da kunci, har manzo (s.a.w) ya kira shekarar mutuwarsu da "Shekarar bakin ciki”.
Amma bayan shekara uku da wannan takunkumi mai muni na hana saye da sayarwa, da mu’amala, da auratayya, da sanya hannun jagorori arba’in na Kuraishawa da aka kakaba musu ne sai Allah ya sanya gara ta cinye rubutun wannan mummunan takunkumi da aka rubuta aka rataya a dakin Ka’aba, ba abin da ta bari sai kalmar "Bismikallahumm” wato Da sunanka ya Allah!.

Hafiz Muhammad Sa’id
www.haidarcenter.com
Haidar Center for Islamic Propagation
+234 803 215 6884 (Text only or (Line, Tango, Viber, Whatsapp, Telegram)
hfazah@yahoo.com – hfazah@hotmail.com
10 Rabi’ul awwal 1427
20 Parbardin 1385
9 Afrilu 2006
 
[1] – Almizan: 20/327.
[2] – Biharul anwar: 18/207-208.
[3] Siratul musdapha: 1/158.
[4] – Mausu’atut Tarih: 1/405. Mausu’atul mustapha wal itra: 1/108.
[5] Mausu’atut tarih: 1/430.
[6] – A’alamul hidaya: 1/94.
comments Masu kallo
Suna:
Adireshin Email:
* ra'ayi: