bayyinaat

Published time: 23 ,January ,2017      09:18:05
Ya zo a babin ci da shan manzon Allah (s.a.w) cewa: "Manzon Allah (s.a.w) ya kasance yana cin dukkan nau'o'in abinci, tare da iyalansa da masu yi masa hidima, kuma yana ci tare da wadanda ya kira su na musulmi a kasa, kuma a kan abin da suka ci da kuma daga abin da suka ci, sai dai idan bako ya zo masa to sai ya ci tare da bakonsa".
Lambar Labari: 8

Wadannan wasu bayanai ne muhimmai game da halayen manzon Allah Muhammad dan Abdullah (a.s) da rayuwarsa.
Manzon Allah (s.a.w) da iyalan gidansa wadanda ya bar mana su a matsayin makoma da idan mun yi riko da su ba zamu taba bata ba har abada su ne ya dace ga dukkan musulmi ya rike su alkibla makoma da zai dogara da ita har abada, kuma su ne jirgin annabi Nuhu (a.s), kofar tuba, haskakan shiriya.
Domin samun tsira dole ne mutum ya kasance yana da akida sahihiya, da biyayya ga umarnin Allah da manzonsa da suke kunshe cikin littafin Allah da sunnar manzonsa, da kuma bibiyar kyawawan halaye manzon rahama Muhamamd dan Abdullah (s.a.w) da wasiyyansa tsarkaka da suka kama tun daga Imam Ali har zuwa Imam Mahadi (a.s). Don haka babu wani wanda ya fi dacewa a yi nuni da halayensa don a yi koyi da shi sai wannan gida da Allah bai yi kamarsa ba.

Ya zo a babin ci da shan manzon Allah (s.a.w) cewa: "Manzon Allah (s.a.w) ya kasance yana cin dukkan nau'o'in abinci, tare da iyalansa da masu yi masa hidima, kuma yana ci tare da wadanda ya kira su na musulmi a kasa, kuma a kan abin da suka ci da kuma daga abin da suka ci, sai dai idan bako ya zo masa to sai ya ci tare da bakonsa".
Ba mu taba samun wani mutum mai kamala a tarihi kamar manzon rahama (s.a.w) ba, irin daukakar da yake da ita wurin Allah da babu wani mahaluki da ya taka sawunsa balle ma ya hango kurarsa, amma sai ga shi ba mu samu wani wanda ya kai shi kaskan da kai ga mutane ba.
Wani abin da yake nuna mana haka a fili shi ne abubuwan da suka zo a cikin babin cinsa da shansa, akan siffanta shi da cewa yana cin dukkan nau'in abin ci ba tare da ya aibata wani daga abin ci ba, domin dukkaninsu ni'imomin Allah ne da ya bayar da su ga bayinsa domin su gode masa, wannan siffa ta gode wa ni'imomin Allah ta bayyana cikin ayyukansa da zantuttukansa hatta ga abin ci ko sha. 
Sannan yana ci tare da iyalansa da masu yi masa hidima, idan muka ce mutum yana ci da iyalansa ta yiwu mutane su ga zai yiwu saboda kusancinsa da su, sai dai ba mu samu al'adun hausa suna yin haka ba, an dauka cewa mace ba ta da wani aiki sai dahuwa da kwanciya, kamar dai wata na'ura ce ta dafa abinci kawai, amma a zauna tare da ita a ci abinci wannan bai ta so ba, haka ma ba a san yin hira da ita ba.
Sai dai tayiwu a samu canji ga mutanenmu na yau sakamakon shigowar al'adu da wayewa da a yau ta fi na mutanenmu na gargajiya, da kuma wayewa da ilimi a yau da suka fi da yawa, ta yadda a yau idan ka dauki matarka kun tafi yawo babu mai ganin hakan a matsayin sabon abu.
Amma cinsa tare da masu yi masa hidima shi ne mafi girman lamarin da ya kamata mu lura da shi sosai, domin masu aikin gida kamar masu wanke-wanke, da masu cefane, da masu yi wa mutumm gadi a cikin al'ummu ba a daukar su da kima, hasali ma mutane sukan iya yi musu tsawa, wasu ma har da duka, kuma tayiwu saboda wani abu ne kankani da suka manta da shi ko suka gafala ba su yi ba.
Sai dai manzon rahama mafi kamalar dan Adam yana daukarsu a matsayin mutane kamar kowa, don haka yana cin abinci tare da su ba tare da wani kyama ba, kuma yana fifita su a kansa, domin su ji cewa su ma al'umma ce mai daraja kuma mutane ne masu kima a cikin al'umma.
Bai taba zagi ko duka ko daka tsawa ga dayansu ba, har ma ya kasance ana cewa yakan ce da su da an yi abu kaza da shi ya fi, tsira da amincin Allah su tabbata gareshi, sai Allah ya siffanta shi da cewa shi ne mafi daukakar bayi a kyawawan halaye. Tawali'unsa ya kai ga balaraben kauye yakan shigo birni sai ya zo majalisin annabi (s.a.w) amma sai ya tambaya ya ce: "Waye Muhammad a cikinku?.
A kasashenmu na kasa da shugaban ba ya iya ganin sa, kuma tayiwu idan ya ce zai gan shi ya kasnace ya yi shekaru bai samu wannan ba, ko kuma ya kasance ana shakkunsa koda kuwa yana son su gaisa ne kawai. Sannan yawanci kallon da shugaban zai yi masa bai wuce kallon wani wanda yake da rashin kima ba, ko kuma ya kalle shi a matsayin wani kayan cimma burin siyasarsa kawai.
Wannan lamarin ne ya sanya hatta da samari ana raba musu kayan shaye-shaye kuma a raba musu makamai domin su kashe junansu, kuma a nesanta su daga ilimi da hankali, don haka ne ake ba su kayan maye. Yayin da shi mai ba su din ba zai yarda ba daya daga cikin kannensa su shiga wannan aikin balle 'ya'yansa kuma, amma ya dauki al'ummarsa abin gwaji domin cimma nasa hadafi ba nasu hadafin ba.
Balle kuma su samu matsayin da zasu je su zauna da shi domin su ci abinci a teburi daya, su gaya masa matsalolinsu, ya share masu hawayensu. Amma sai ga wanda duk wani abu da aka halitta yana kasan darajarsa, wanda shi ne ya samu feshin ilimin Allah na farko da kuma siffofinsa madaukaka, sai ya kasance mai rahama da jin kai, sai ga shi yana zama da wadanda suka zo wurinsa suna cin abinci tare.
Yana ci tare da wadanda suka zo wurinsa na daga musulmi, kuma a kan kasa, wannan halayen na fiyayyen halitta da an samu shugabannin duniya sun kwatanta kashi 10% na wannan halaye masu daraja da an samu ci gaban dan Adam. A kasarmu akwai shahararren malami guda miloniya ne domin yana da kudi da gidaje da ba sa kirguwa, amma babu wani wanda zai ce ya taba zuwa gidansa ya samu wani abin sha koda kuwa ruwa ne balle kuma abinci.
Kai tir da masu sanya rigar sunan musulunci balle malanta amma suna da dabi'un da ko fir'auna ya fi kyautatawa ga mabiyansa. Ba komai ya sanya ni fadin haka ba sai domin fir'auna yana jiyar da mai biyayya gareshi na daga kabilarsa ta kibdawa dadi, yana kaskantar da wasu kabilu ne na Banu Isra'il da yake ganin sun zo bakin haure sun mamaye musu wuri wadanda a ganinsa sun zo sun bata masu addini da gargarjiya ne tun lokacin annabi Yusuf (a.s).
Kuma ayar Kur'ani mai daraja ta yi nuni da wani lamari mai muhimmanci yayin da ta yi wa wasu daga sahabban annabi (s.a.w) fadar cewa idan sun ci abinci a gidansa sai su fita, ba sai ya yi musu nuni ba da cewa su fita. Wato manzon Allah (s.a.w) mai tsananin kawaici da kunya ba ya iya gaya musu cewa idan an ci abinci a fita daga gidansa, sai da ubangiji mai tsananin kishi gareshi ya yi musu fada da abin da suke yi bai dace ba.
Sannan kaskan da kansa ya sanya shi ci a kasa, ba tare da kallon kansa da matsayinsa wurin Allah ba, sai ya kalli kansa a matsayin cewa shi daga kasa yake, kuma cikinta zai koma bayan mutuwarsa, don haka sai ya kasance mai daukakar kaskan da kai, bai kalli turbayar sama ba wacce tasa ta bambanta da ta sauran sahabbansa wanda da ya ga dama da ya yi hakan, amma sai ya kalli turbayar kasa domin ya daidaita kansa da sauran, sai ya bar musu darasi yayin da zasu kasance shugabanin al'umma bayan wucewarsa.
Sai ya ci abin da suke ci, kuma ya sha abin da suke sha, bai ware nasa kwanon daban ba a matsayin kwanon annabi, ko cokalin annabi, ko kofin shan ruwan annabi. Sai ya yarda ya yi tarayya da sauran kan dukkan abin da yake amfani da shi, kamar yadda ya yarda ya ci daga dukkan abin da suke ci.
Bai yarda da ware wani nau'in abinci mai maiko a matsayin nasa daban ba, kuma wannan mummunar dabi'ar da annabi ya yaka mun same ta hatta tsakanin masu da'awar su ne masu kishin addini a duniya, sai a ware wa shugaban wani abinci da talakan da ake tare da shi ba zai iya cin sa ba.
Lallai baban Kasim (s.a.w) duk wanda ya yi da'awar yana kan halayenka daga mutanen duniya da suke raye in banda halifanka na goma sha biyu Imam Mahadi (a.s), ko waye kuwa to wallahi ya yi karya, wanda duk ya yi da'awar ya kiyaye sunnarka kamar yadda kake ya yi jafa'i ga Allah mahalicci kuma ya yi isgili da dukkan kyawawan halaye.
Ba kawai manzon Allah (s.a.w) hatta da Imam khomain wanda bai kai darajar kurar da manzon Allah (s.a.w) ya taka ba, amma sai ga shi Fedal Kasto na Cuba da ya ga gidan da yake rayuwa yana cewa: "Idan dai kwaminisanci yana nufin mu rayu iri daya da babu bambanci tsakanin talaka da jagora to lallai Imam Khomain ya fi mu kwaminisanci", wannan ga malamin gaskiya mai imani da tsoron Allah da yake kokarin ya kwantanta rayuwar manzon Allah (s.a.w) ke nan, ina ga a ce Fedal Kasto ya ga annabin ne kansa.
Sannan kuma yana ci da bakonsa wannan ma wani abu ne mai muhimmanci wanda ya kamata duniya ta yi rubuce rubuce a kansa, domin mafificin al'ummar duniya amma yana ci da baki, kuma yawancinsu mun san mutane ne da suke zo masa daga kauyuka. Don haka mai ji da sarauta ko takamar yana da dukiya ko matsayi ya duba matsayin gaskiya na mafificin halitta, ya yi koyi da shi, ya sauke rawanin tsiya da ya sanya a kansa, domin samun mafi tsira a lahira, da soyayyar Allah madaukaki da bayinsa a duniya.
Manzon Allah (s.a.w) ya kasance yana tuna Allah (s.w.t) a kowane abu, don haka zamu ga idan aka ajiye abinci a gabansa sai ya ambaci sunan Ubangiji madaukaki, idan kuwa ya gama sai ya gode masa, kuma bai taba gafala ba ko sau daya ko mantuwa da yin hakan, hatta da sahur da shan ruwa.


Idan kuwa zai ci abinci sai ya zauna kamar yadda bayi suke zama don kaskan da kai ga Allah (s.w.t), kuma ya zauna da nutsuwa sai ya ambaci Allah (s.w.t), sannan sai ya ci da 'yan yatsu uku ko hudu ko da tafinsa, kuma yana cin gabansa ne ba ya bin gaban wasu, sannan idan shi ne ya zo da abicin sai ya fara.
A kowane abu manzon Allah (s.a.w) yana kiyaye hakkin mutane, don haka ne ya kasance ba ya cin tafarnuwa ko albasa, ko wani abu da yake da warin da mutane suke cutuwa idan sun shake shi. Sai dai duk da haka ba ya kushe abin da ba ya cin sa, idan ya kayatar da shi sai ya ci, idan kuwa abin ci bai kayatar da shi ba sai ya bari ba tare da ya kushe shi ba.
Idan ya gama cin abinci sai ya sude hannunsa, sannan sai ya tsarkake ta da wani kyalle, sannan sai ya wanke hannun, ya shafe shi da wani kyalle, don haka ne ba a samun hannunsa yana kanshin abin da ya ci.
 Sannan ba ya ci shi kadai sai ya samo mai taya shi, yana ganin mafi sharrin mutane shi ne wanda ya ci shi kadai, ya daki bawansa, ya hana mutane abincinsa. Kuma ba ya cin mai zafi yana yana umarni da a bari sai ya yi sanya, yana ganin shedan yana da rabo a abinci mai zafi.
Sannan akwai abin ci masu yawa da ruwayoyi suka kawo cewa manzon Allah (s.a.w) yana cin su da suka hada da dabino, da sukari, da gishiri, da alkama, da duma, da kankana, da gishiri, da kayan marmari, da inabi, da gurasa, da nono tare da dabino. Haka nan yana cin nama gasasshe, yana ganin yana da amfnai wurin karfafa ji da gani, yana cin naman kaji, da tsuntsaye, yana son karfata daga tumaki da awaki. Kuma yana cin gurasa da mai, yana shan kunu, yana cin abubuwan da suke a kasa kamar irinsu dankali da makani.
Idan muka koma batun sha zamu ga yana sha a kwano, kuma yana sha bayan ya ambaci Allah sannan idan ya kare sai ya gode masa, yana zukar ruwa ne ba ya kwankwandarsa, kuma ba ya lumfashi a cikin kwanon shan ruwa, idan zai yi lumfashi sai ya yi nesa da kofi ko kwanon shan ruwan.
Sannan akwai matakai masu mihimmanci bayan ci kamar kurkure baki, da muka fi sani a  yau da yin burush kafin mutum ya kwanta domin kada abin da ya bari na kufan abinci ya lalata masa hakora, da sauran matakan tsafta da mai aminci ya yi nuni da su a aikace.
An ruwaito daga gareshi mai aminci cewa: Ka ci kana sha'awa, ka bari kana sha'awa. Wannan lamarin yana nuna mana muhimmancin rashin cika ciki ya yi yawa, don haka riko da wadannan nasihohi nasa mai aminci shi ne hanyar da zai samar da lafiya ga al'umma.
Akwa maganganun masu yawa a wannan babin da suka hada da abubuwan da  ya kamata a ci, da lokacin da ya kamata a ci, da zamanin da ya dace da cin su, da kuma abubuwan da bai kamata a ci ba, da amafanin abubuwan ci daban-daban, sai dai zmau takaita a nan zuwa wani jikon.
Amma idan muka duba adon manzon Allah (s.a.w) zamu ga ya ba wa wasu abubuwa muhimmanci kamar turare.  Imam Jafar Sadik (a.s) yana cewa: Manzon Allah (s.a.w) ya kasance yana kashe wa turare kudi fiye da yadda yake kashe wa abinci. Kuma ba a ba shi wani turare sai ya sanya shi yana cewa: Shi kanshinsa mai dadi ne, daukarsa mai sauki ce, kuma ya kasance yana yin turare da almiski. Kuma a cikin duhun dare ana iya gane shi da kanshin turarensa kafin a gan shi, don haka idan ya wuce sai a ce; wannan manzon Allah ne (s.a.w).
Ya kasance yana taje gashin kansa da gemunsa da matajin karfe ko na katako, kuma matansa suna taje masa gashinsa da gemunsa, sai su dauki gashin da ya fadi kasa, kuma sau da yawa yana taje gemunsa sau biyu a rana. Ya kasance yana son gyara gashi yana kin buja-buya, yana farawa da kai sannan sai gemu sai kuma sauran inda yake da gashi.
 Manzon Allah (s.a.w) ya kasance yana shafa mai, kuma yana farawa da girarsa sannan sai gashin baki, sai kansa sai gemu. Kuma yana sanya kwalli sau uku a dama sannan sai hagu sau biyu, kuma yana sanya kwalli har a lokacin azumi. 
Ya kasance yana duba madubi, yana kuma duba ruwa ya gyara keyarsa, yana ado ga sahabbansa balle ga matansa. Yana cewa: Ubangiji yana son bawan da idan zai fita cikin mutanensa ya shirya musu ya yi musu ado.
Amma sunnonnin manzon Allah (s.a.w) a wannan lokacin musulmi sun yi wurgi da mafi yawancinsu, sai suka dauki wani abu daban ba su ba, aka jefar da mafi yawan dabi'unsa da halayensa, aka musanya su da wasunsu, sai musulmi suka musanya kaskan da kansa da girman kai da dagawa, kyawawan halayensa kuwa aka wurga su kwandon shara aka dauki munanan halaye aka yafa.
Manzon Allah (s.a.w) ya kasance yana kallon kasa-kasa yayin tafiya, yana fara wa wanda ya hadu da shi da sallama, ba ya magana sai gwargwadon bukata, yana girmama ni'imomin Allah ba ya rena komai daga garesu, sai ya gode wa Allah madaukaki, yana dariya amma ta murmushi, yana tambayar sahabbansa idan bai ga dayansu ba, yana tambayar mutane don ya san halinsu, yana tashi da zama bisa ambaton Allah, yana zama inda ya samu wuri ne, yana girmama abokan zamansa ba tare da ya nuna fifiko ba, ba ya hana wanda ya roke shi sai dai iban babu sai ya yi masa magana mai dadi ko addu'a ko ya yi masa nuni da inda zai samu bukatarsa, ba ya jayayya da nuna isa kan wasu don wulakanta su, ba ya hassada ko kullata, yana barin abin da babu ruwansa, ba ya yanke wa wani maganarsa, yana daidaita kowa a kallo, ya fi kowa fasaha, yana magana mai tattare da hikima, yana da yawan kunya, ya fi kowa karfi da jarumta, yana kuka don tsoron Allah, yana tuba da istigfari sau 70 a kowace rana, yana zama da talakawa, yana ci da miskinai, yana sadar da zumunci, yana dinke tufafinsa, yana gyara takalmansa, yana ci kamar yadda bayi suke ci, yana zama a kasa, yana hannu da talaka da mai kudi, ba ya wulakanta talaka don talaucinsa, yana sallama ga kowa talaka da mai kudi, babba da yaro, yana kallon mudubi, yana zabar mafi tsanani don saba wa ransa da saba wa son rai, yana cin gabansa, ba ya ci yana kishingide, yana sha da lumfashi uku, yana son yin abu da hannun dama; damansa domin abinci, hagunsa domin jikinsa, idan ya yi magana sai ya yi murmushi, mafi yawan zamansa yana kallon alkibla ne, idan aka zo da yaro sai ya yi masa addu'a ya kai shi dakinsa, kuma tayiwu yaron ya yi masa fitsari a daki sai ya bari sai mutanen sun tafi sai ya wanke da kansa, ba ya bari wani ya tafi tare da shi idan yana kan abin hawa sai dai idan mutumin zai hau tare da shi (wato manzon Allah ya goya shi kan dabba), idan kuwa mutumin ya ki hawa sai ya ce masa: Yi gaba sai ka same ni a wurin da kake so. Kuma ya kasance idan bai ga mutum kwana uku ba sai ya tabamya, idan ba ya nan ne sai ya yi masa addu'a, idan yana nan sai ya kai masa ziyara, idan maras lafiya ne sai ya je ya gai da shi.




Manzon Allah (s.a.w) ya kasance bai taba cewa da mai yi masa hidima don me ka yi kaza ba, sai dai ya ce; da ka yi kaza da ya fi. Yana kiran kowa da kinayarsa domin girmamawa, yana sanya kinaya ga maras kinaya, yana ba wa wanda ya shigo matashinsa, idan kuwa ya ki sai ya nace masa har sai ya karba, yana futowa bayan bullowar rana, domin yana yin addu'a ne tsakanin alfijir da bullowar rana, idan ya shiga gida sai ya zauna a farkon wurin da ya samu a kowa.
Ya kasance bai taba yi wa kowa magana gwargwadon hankalinsa ba, sai dai gwargwadon hankalin su mutanen domin tausaya musu, shi mai yawan rusunawa da roko ga Allah ne, mai yawan addu'a, yana yanke akaifarsa, yana rage gashin baki kafin ya fita sallar juma'a, yana yin raha don tausaya wa al'ummarsa domin kada wasu su wuce gona da iri a kansa su rike shi kamar yadda kirista suka riki Isa (a.s).
Yana yi wa na kusa da shi magana da abin da ya dace da su, idan suna maganar lahira sai ya yi tare da su, idan ta duniya ce sai ya yi tare da su, idan suka ci ko suka sha sai ya kasance tare da su. Ba ya duba na ha'inci zuwa ga abin da bai  halatta ba, ko nuni da hannu haka nan, idan ya yi magana sai ya maimaita sau uku domin mai ji ya fahimta kuma ya fahimce shi ko ya isa da shi ga mutanensa.

Idan aka tambaye shi yin wani abu; idan zai yi sai ya ce; Na'am, amma idan ba zai yi ba sai ya yi shiru, ba ya kallon abin da yake na shagaltuwar duniya domin kada ya shagaltu da shi ko ya dauke masa hankali, kuma idan wani abu ya bata masa rai sai ya shiga yin salla, yana son kebewa shi kadai domin yin ambaton Allah da tunani da lura shi kadai, yana tanadar ruwan sallar darensa, yana tamaka wa matansa ayyukan gida, yana yanka nama, baya kura wa wani ido, yana sanya zoben azurfa a hinsar na dama, yana yin aswaki, yana raka janaza, yana gaida maras lafiya, ba ya tsawaita salla idan wani yana jiran sa sai ya gama salla ya ce masa: Kana da wata bukata ne?
Ya kasance yana fadin gaskiya a fushi ne ko a yarda, yana son miskinai, idan zai yi bacci sai ya yi alwala ya yi salla raka'a biyu gajeru sannan sai ya kwanta, ya ambaci Allah yayin kwanciya ya gode masa yayin tashinsa, yana yin matashi da damansa. Yana son aure yana kwadaitar da yin sa, yana da kishin matansa matuka, da safe kuwa yana shafa kan 'ya'yansa da jikokinsa, yana kyautata sunayen yara da aka haifa yana yi musu akika (ragon suna(, idan talauci ya same su sai ya ce da iyalansa ku tashi mu yi salloli.
Idan ya yi tafiya yana daukar madubi, da kwalli, da miswaki, da mataji, da kwalbar turare, da allura da zare, idan yana tafiya baya girman kai kuma ba ya nuna ragwanta ko kasala ko gajiyawa, idan an zo gangara sai ya yi tasbihi, idan kuwa an zo hawa sai ya kabbara, kuma duk inda ya sauka sai ya yi raka'a biyu tukun, sannan yana kin mutum ya yi tafiya shi kadai.
Manzon Allah (s.a.w) ya kasance mafi yawan tufafinsa farare ne, kuma yana son koren tufafi, sannan yana kwadaitar da mutane kan yin tsafta. Yana da zobuna da yake sanya su a hannun dama, sannan yana sanya kafar dama kafin hagu a sanya takalminsa, amma yana fara cire hagu kafin dama, yana da tufafi na musamman don sanya su ranar juma’a.
Allah madakaki ya girmama shi da abubuwa, ya sanya yin salati gareshi tare da alayensa a matsayin wajibi addini da ya hau kan musulmi, sannan ya sanya biyayya gareshi da alayensa wajibi ne a kan dukkan mutane baki daya. Zancensa da na alayensa wasiyyansa dukkansa hikima ne kuma hujjar Allah ce kan talikai, kuma tafarkin tsira da shiriya ga duniya baki daya.
Domin hadafin manzon Allah (s.a.w) shi ne tsiratar da duniya gaba daya, don haka ne ya sanya soyayya da kauna su kasance jagorori a cikin al’umma baki daya, sannan ya sanya ‘yan’uwantaka tsakanin musulmi a zamaninsa sai dai ban da gado da hani ya zo a kansa daga baya sai dai ga makusanta na jini. Da haka ne ya kafa wata al’umma mai karfi da ilimi, da son juna, wacce ta dauki nauyin yada wannan addini a duk fadin duniya baki daya.
Ya kasance ba ya tashi ko zama sai bisa ambaton Allah madaukaki, kuma yana zama inda ya samu sarari ne ba ya gwamatsar mutane, ya kasance yana daidaita kowa a bisa girmamawa. Majalisinsa wuri ne na jin kunya, da hakuri, da gaskiya , da amana, da kawaici, da girmama babba, da tausaya wa karami, da biyan bukatun mabukata.
Bai kasance mai kaushin hali ba, ya kasance mai sakin fuska, mai fara’a, mai taushin hali, ba ya aibatawa, ba ya zagi, ba ya alfahasha, kuma yana kau da kai daga abin da yake sha’awa, idan ya yi magana duk sai mutane su sunkuyar da kai kamar dai a kansu akwai tsuntsaye ne, sai dai idan ya yi shiru ne to sais u yi magana, kuma ba sa jayayya gunsa.
Da zai bar duniya ya bar wa al’ummarsa abubuwa biyu day a gaya musu idan sun yi riko das u ba zasu taba bata ba har abada, su ne; Littafin Allah da wasiyyansa alayensa tsarkaka goma sha biyu, hada da mai tsarki uwar alayensa matar wasiyyinsa na farko sayyida Zahara as, Allah ya sanya mu cikin cetonta. Ya wajabta son su kan kowa, da biyayya garesu da taimaka musu, da tsayawa idan suka tsayar da al’umma, sai dai al’umma ta yi watsi da wannan wasiyyar kamar yadda aka yi watsi da wasiyyar sauran annabawa

Rufewa:
Yayin da Allah ya halicci mutum yayin nufin alheri da rabautar duniya da ni'imar lahira da aljanna gareshi amma wannan duk ba ya samuwa sai idan mutum ya yi amfani da hankalinsa da kuma abin da ya dace da ruhinsa da jikinsa, wannan kuwa yana bukatara abin da zai dauke wadannan bukatu wadanda ba wanda zai iya samar da dukkan wannan sai mahaliccin mutum din da ya san shi kuma ya san bukatunsa.
Tun da Allah yana son rabauta ne ga mutum shi ya sa halicce shi, don haka ne sai ya samar masa da hanya kamila da zai bi domin samun rabauta ta hanyar wasu amintattun bayi nasa da suke ma'asumai daga dukkan kuskure da mantuwa kuma tsarkaka daga dukkan aibobi da zunubai wadannan su ne annabawa da manzanni.
Don haka ne: Annabi shi mutum ne da Allah ya yi masa wahayi ya zabe shi a cikin mutane kuma sun kasu gida biyu:
Annabi dan sako shi ne wanda aka aiko domin ya tseratar da mutane daga duhu zuwa haske daga barna zuwa gaskiya daga camfi zuwa gaskiya daga jahilci zuwa ilmi.
Annabi ba dan sako ba: shi ne wanda aka yi masa wahayi zuwa ga kansa kuma ba a umarce shi ya isar da sakon ga mutane ba.
Yahudawa suna bin Annabi Musa (a.s) kiristoci kuma Annabi Isa (a.s) musulmi kuma Annabi Muhammad (s.a.w) da sauran annabawa duka. Sai dai musulunci ya shafe sauran addinai da suka rigaya, bai halatta ba ma'abotansu su wanzu a kansu, dole ne a kan kowa ne mutum ya bi koyarwar musuluncici. Ubangiji yana cewa: "wanda ya yi riko da wani addini ba musulunci ba to ba za a karba daga gareshi ba, kuma shi a lahira yana daga cikin masu hasara" .
Don haka yahudanci da kiristanci barna ne da aka shafe su, amma musulunci mai wanzuwa ne har zuwa ranar kiyama.
Annabi Muhammad (s.a.w) shi ne karshen annabawa kuma addininsa shi ne musulunci mai shafe duk wani addini kuma shari'arsa zata wanzu har zuwa kiyama kuma ita kadai ce shari'ar da zata arzuta mutum da tabbatar masa da burinsa da amincinsa har zuwa karshen rayuwa duniya da lahira. Kamar yadda shi kadai ne mutum abin koyi ga dukkan duniya baki daya, dukkan mutanen duniya idan suna son alheri ga kawukansu to dole ne su bi tarfarkinsa su yi koyi da kyawawan halyensa (s.a.w) da kuma sanin sashen tarihinsa da ba makawa mu kawo wasu daga siffofinsa (s.a.w): 
Shi ne Muhammad dan Abdullah (s.a.w) kuma babarsa ita ce Aminatu 'yar Wahab. An haife shi a Makka ranar juma'a goma sha bakwai ga watan Rabi'ul awwal bayan bollolwar alfijir a shekarar giwa, a zamanin sarki mai adalci Kisra . (wato idan an kwatanta shi da ire-irensa).
An aiko Annabi Muhammad (s.a.w) da sako a 27 ga Rajab bayan yana dan shekara 40 yayin da Jibrilu (a.s) ya sauka gareshi daga wurin Allah (S.W.T) yana kogon Hira wanda yake dutse ne a Makka ya ce masa ka karanta kuma ya saukar masa da ayoyi biyar na surar Alaki .
Sai ya zo ya tsaya a kan dutsen Safa a masallaci mai alfarma na Makka a lokcin akwai jama'a masu yawa a wurin da ake taruwa ya isar da sakon Allah na shiryar da mutane zuwa ga imani da shi yana cewa da su: "Ku ce babu abin bauta sai Allah kwa rabauta" .
A lokacin tunda mutanen Makka mushrikai ne, kuma suna ganin maslaharsu ita ce shirka kuma suna tsoron maslaharsu sai suka rika yi masa isgili suna yi masa dariya suna cutar da shi. Kuma duk sa'adda ya dage wajen shiryar da su sai su dage wajen cutar da shi har ya ce: "Ba a cutar da wani Annabi ba kamar yadda aka cutar da ni" .
Ba wanda suka yi imani da shi sai mutane kalilan, na farkonsu Imam Ali sannan sai matarsa Hadiza (a.s) sannan sai wasu mutane.
Farkon wanda ya yi imani da shi daga maza Imam Ali (a.s) sannan daga mata sai Hadiza (a.s).
Yayin da takurawar mushrikai ta yi yawa sai ya yi hijira zuwa Madina wannan kuwa ita ce hijirar farko a tarihin Musulmi, yayin da suka yi yawa sai karfinsu ya dadu kuma suka samu koyarwa daga Manzon Allah da shari'arsa mai sauki mai hikima, da kuma misali na kyawawan halaye da mutumtaka da wayewa da cigaba a Madina har suka fi dukkan duniya da addini na sama da wadanda ba na sama ba.
Kuma an samu yakoki masu yawa a Madina kuma dukkanninsu sun zama domin kare kai ne daga makiya mushrikai da yahudawa da kiristoci da suke kai hari kan musulmi, kuma Annabi a kowne lokaci yana zabar bangaren sulhu da zaman lafiya ne da rangwame, don haka ne ma adadin wadanda ake kashewa daga bangarorin biyu ba su da yawa a dukkan yakokinsa tamanin da wani abu, wato; wadanda aka kashe na musulmi da kafirai duka ba su kai sama da dubu daya da dari hudu ba.
Tun lokacin da aka aiko Annabi da sako har ya tafi daga duniya wahayi yana sauka gareshi kuma Jibrilu (a.s) shi ne ake aiko masa daga wajen Ubangiji (S.W.T) a hankali a hankali har littafin Kur'ani ya ciki a cikin shekaru ishirin da uku, sai Manzo (s.a.w) ya yi umarni da a hada shi kamar yadda yake a yau din nan.
Manzo (s.a.w) ya kasance yana tsara wa musulmi duniyarsu da addininsu, yana sanar da su littafi da hikima kuma yana yi musu bayanin dokokin ibada da biyayya da mu'amala da zamantakewa da siyasa da tattalin arziki da sauransu.
Bayan cikar addini da kafa Ali dan Abu Dalib (a.s) shugaba na al'umma kuma halifa bayan Annabi (s.a.w) wannan kuwa ya faru a ranar Gadir ne goma sha takwas ga zulhajji a shekarar hajjin bankwana sai Allah ya saukar da ayar: "A yau ne na kammala muku addininku, na cika ni'imata gareku kuma na yardar muku da musulunci shi ne addini" . Sai Annabi ya yi rashin lafiya mai sauki, sai dai ya yi tsanani har sai da ya hadu da Ubangijinsa a 18 ga watan safar na 11H. 
Kuma wasiyyinsa halifansa Imam Ali (a.s) shi ne ya yi masa wanka da salla da binne shi a dakinsa a Madina inda kabarinsa yake yanzu.
Ya kansace abin koyi ne shi a rikon amana da ikhlasi da gaskiya da cika alkawari da kyawawan halaye, da girma, da kyawawna dabi'u, da baiwa, da ilmi, da hakuri, da rangawame, da afuwa, da sadaukantaka, da tsentseni, da takawa, da zuhudu, da baiwa, da adalci, da kaskan da kai, da jihadi.
Jikinsa ya kasance kololuwa wajen kyau da kuma daidaito da dacewa, kuma fuskarsa kamar wata ne mai haske da ya cika, kuma zuciyarsa da ruhinsa sun kai matuka wajen kamala, mafi kamalar halaye da ladabi da dabi'a kuma sunnarsa tana haske kamar rana a tsaka-tsakinta.
Atakaice, ya tattara dukkan wata dabi'a mai kyau da girma da daukaka da kuma ilimi da adalci da takawa da kuma iya tafiyar da al'amuran duniya da na lahira, wadanda babu wani mahaluki da yake da irinsu.
Wannan shi ne annabin musulmi kuma wannan shi ne addinin musulunci, kuma addininsa shi ne mafificin addinai, littafinsa shi ne mafifcin littattafai domin shi: "Barna ba ta iya zo masa ta gabansa da ta bayansa, abin saukarwa ne daga mai hikima abin yabo" .
Muhimmancin samuwar wannan annabi mai daraja wanda ya kasance hanyar shiriya ga dukkan talikai da suke bayan kasa ne ya sanya musulmi yin murna da bikin ranar haihuwar manzon Allah (s.a.w) da aka fi sani da mauludi.

Hafiz Muhammad Sa'id
hfazah@yahoo.com

comments Masu kallo
Suna:
Adireshin Email:
* ra'ayi: