bayyinaat

Published time: 20 ,April ,2017      23:30:13
Sigar lafazin kulla auren mutu'a shi ne, bayan an ambaci kudi ko nawa ne zai ba ta, ko kuma mene ne zai yi mata a matsayin sadaki kamar koyar da ita ilimi, ko wani aiki da zai yi mata, sai mace ta ce:
Lambar Labari: 86
Babu wani bambanci tsakanin yadda ake kulla auren "Mutu'a" da da aure "Maras Iyaka" sai a lafazin iyaka da ake ambato a wurin kulla auren "Mutu'a" don haka ne ma idan aka manta ambaton iyaka to ya koma maras iyaka kai tsaye. Ana kulla auren mutu'a da siga ne wato lafazi tsakanin masu son yin auren ko kuma wanda suka wakilta, ko kuma daya daga cikinsu ya yi sigar da yardar daya bangaren. Da wani ya kulla musu aure ba da izininsu ba, to bai yi ba, sai idan sun amince daga baya sun yarda. Don haka idan mutum ya kulla auren mutu'a tsakaninsa da wata ba da izininta ba, to sai ya gaya mata ya kulla musu auren sai ta yarda, to shi ke nan ya yi. Haka nan da wani zai kulla auren mutu'a tsakanin wani da wata, sannan sai ya gaya musu cewa ya kulla musu aure sai suka amince da ya yi. Haka nan batun hukuncin neman izinin kulla auren ga mace da tasyawar waliyyi babu bambanci tsakanin auren mutu'a da na da'imi (maras Iyaka ko maras lokaci), don haka idan da mace babu bukatar izinin mahaifanta kamar wacce ba budurwa ba ce kamar bazawara, ko mai zaman kanta zata kulla auren mutu'a, to ita ce take zama mai ikon kulla wa kanta aure.
Sigar lafazin kulla auren mutu'a shi ne, bayan an ambaci kudi ko nawa ne zai ba ta, ko kuma mene ne zai yi mata a matsayin sadaki kamar koyar da ita ilimi, ko wani aiki da zai yi mata, sai mace ta ce:
أنكحت نفسي لك على المهر المعلوم إلى أجل مسمى 
Wato; Na aurar maka da kaina bisa sadaki ayyananne, zuwa lokacin da aka ambata .
Sai shi kuma namijin ba tare da wani daukar lokaci ba sai ya ce: قبلت"" Wato; Na karba. Ko ya ce: قبلت التزويج لنفسي على المهر المعلوم Wato: Na karbi auren ga kaina bisa sadakin sananne (ayyananne). Kuma tun da auren mutu'a ne ya zama dole a ambaci cewa zuwa wani lokaci wanda suka ayyana, don haka ne dole a kara da cewa: إلى أجل مسمى Wato; zuwa lokacin da aka ayyana.
Ana iya amfani da kalmar زوجت maimakon أنكحت. Kuma tun da auren mutu'a ne ana iya amfani da kalmar متعت maimakon wadannan kalmomi guda biyu.
Sannan dole ne siga ta kasance da larabci, amma idan ba zasu iya yi da larabci ba, to sai su yi da wani yare da yake fassarar daidai yadda sigar take da larabci.
Idan ya kasance wakilai ne biyu daya daga bangaren mace, daya kuma daga bangaren namiji, sai wakilin mace ya ce:
أنكحت موكلك فلانا موكلتي فلانه على المهر المعلوم إلى أجل مسمى
Wato; "Na aurar da wacce ta wakilta ni wance ga wanda ya wakilta ka wane bisa sadakin da aka ayyana, zuwa lokacin da aka yi magana".
Sai shi kuma wakilin namijin ya ce:
قبلت النكاح لموكلي على المهر المعلوم إلى أجل مسمى
Wato; Na karbi auren ga mai wakilta ni wane bisa sadakin da aka ayyana, zuwa lokacin da aka yi magana.
Idan uba ne na yarinya zai kulla mata auren mutu'a sai ya ce: 
أنكحت ابنتي فلانة ابنك فلانا على المهر المعلوم إلى أجل مسمى 
Wato; Na aurar da 'yata wance ga danka wane bisa sadakin da aka ayyana, zuwa lokacin da aka yi magana. 
Shi kuma uban yaro sai ya ce: 
قبلت النكاح لابني على المهر المعلوم إلى أجل مسمى 
Wato; Na karbi auren ga dana bisa sadakin da aka ayyana, zuwa lokacin da aka yi magana.
Zai iya yiwuwa namiji ya kulla wa kansa aure da matar da zai aura, kamar idan sunanta Fati sai ya ce: Na aura wa kaina mai wakilta ni Fati, bisa sadakin da aka ayyana, zuwa lokacin da aka yi magana, kuma na karbi auren ga kaina. Sai dai ba ya kasancewa da Hausa sai idan an rasa iya larabci.
Haka nan mutum daya yana iya daura musu wannan auren sai ya ce: Na aurar da Fati ga Ali bisa sadakin da aka ayyana, zuwa lokacin da aka yi magana, kuma na karbi auren ga Ali, duk wannan da larabci, sai dai idan ba zai iya ba, to sai ya yi da yarensa.
Ya halatta mutum ya daura wa wani da wata aure, sannan sai ya tambaye su, idan suka amince to auren ya wakana ke nan, wannan kuwa a aure Da'imi ne ko na Mutu'a.
Haka nan idan wani yana son wata yana iya daura wa kansa aure da ita, idan ya tambaye ta cewa ya daura musu aure, idan ta yarda shi ke nan sun zama miji da mata, amma idan ba ta yarda ba, to shi da ita ba miji da mata ba ne, sai ya kasance wannan kullin da ya yi na aure da shi da ita kamar bai faru ba ke nan. Kuma ita ma mace tana iya yi masa hakan .
Sabani Kan Auren Mutu'a
An yi sabani da yawa kan lamurran hukunce-hukuncen musulunci, wani lokaci sabanin ya kan kai ga wasu su haramta wani abu, wasu kuma su halatta shi kan lamari daya, auren mutu'a yana daga cikin abubuwan da suka samu kansu a cikin wannan yanayi. Idan mun duba saki misali muna iya ganin yadda Imam Musa Kazim (a.s) ya yi wa Abu Yusuful Kadhi nasiha kan yadda suka cire shedu biyu a kan saki, suka mayar da su a daurin aure, wato shedu biyu a aure Allah bai wajabta su ba, amma ya wajabta su a saki, sai suka juya lamarin. Kamar yadda zamu iya ganin yadda Imam Bakir (a.s) ya kausasa magana kan wanda ya haramta auren mutu'a yana mai dogaro da haramcin Umar dan Khaddabi, kamar haka:
Al’abi ya ce: A cikin littafin Nasruddurar: An rawaito daga Abdullahi dan Mu’ammar Allaisi ya ce da Abi Ja’afar (a.s): Labari ya zo mini cewa kai kana bayar da fatawa da yin auren mutu’a? ya ce: Allah ya halatta ta a littafinsa kuma Manzo (s.a.w) ya sunnanta, sannan sahabbansa sun yi aiki da ita, sai Abdullah ya ce: Ai Umar ya hana yin ta. Sai imam Bakir ya ce: Kai kana kan maganar sahibinka (Umar), ni kuma ina kan maganar Manzon Allah (s.a.w). Sai Abdullah ya ce: Shin zai faranta maka rai (‘ya’yan) matanka su aikata haka? Sai Abu Ja’afar (Imam Bakir) (a.s) ya ce: Kai wawa? Wannan da ya halatta a littafinsa kuma ya halatta ga bayinsa ya fi ka kishi da kai da wanda ya hana, yana mai dora wa kansa nauyi, a yanzu zai faranta maka rai cewa ‘yarka tana karkashin auren wani masaki daga masakan garin Yasrib (Madina)? Sai ya ce: A’a. Sai Imam Bakir (a.s) ya ce: Me yasa kake haramta abin da Allah ya halatta? Sai ya ce: Ba na haramtawa, amma dai masaki ba tsarana ba ne. Sai ya ce: Ai hakika Allah ya yarda da aikinsa ya so shi, ya aura masa Hurul-i’n, a yanzu kana kin wanda Allah yake son sa? kana kin wanda yake tsaran Hurul-i’n din aljanna saboda shisshigi da girman kai? Sai Abdullah ya yi dariya ya ce: Wallahi ba na ganin kirazanku (zukatanku) sai mabubbugar ilimi, sai ‘ya’yan itacensa suka zama a hannunku, ganye kuwa ya rage a hannun mutane .
Sahabbai Sun Yi
A fili yake cewa; musulmin farko na zamanin manzon Allah (s.a.w) da lokacin Halifa Abubakar ba su san haramcin auren mutu'a ba. Muna iya gani kusan dan farko da aka samu sakamakon auren mutu'a shi ne Abdullahi dan Zubair dan Awwam da Asma’u ‘yar Abubakar, da suka kulla wannan auren aka sami dansa Abdullah, wannan lamarin kuwa dan Abbas ya gaya wa Abdullah dan Zubair shi yayin da suka yi jayayya, dan Zubair ya haramta bisa umarnin Umar, sai dan Abbas ya ce masa: Je ka tambayi uwarka idan haramun ne.
Domin idan mun duba zamu ga halaccinta lokacin Manzo (s.a.w) da kuma lokacin halifan farko, da wani bangare na lokacin halifancin halifa Umar, har sai da halifa na biyu Umar dan Khaddabi ya fadi mash'huriyar kalmarsa da yake cewa: "Mutu'a biyu (wato auren mutu'a da hajjin tamattu'i) sun kasance a lokacin Annabi (s.a.w) amma ni na hana su, kuma zan yi ukuba (ladabi) a kan yin su" . A fili yake gun musulmi cewa; Umar shi ne farkon wanda ya haramta. Duba Tarihul Khulafa na Suyudi, yayin da ya sanya Umar cewa shi ne farkon wanda ya haramta auren mutu'a .
Wannan haramcin na Umar hatta da dansa Abdullahi dan Umar bai yarda da shi ba, yana mai kafa hujja da cewa; hanin Umar ba ya rushe umarnin Annabi (s.a.w). Da wannan ne zamu ga cewa; dukkan al'umma sun yi ittifaki a kan cewa; Umar ya haramta, sai dai wasu don su gyara abin sun so su mayar da hanin zuwa ga lokacin manzon Allah (s.a.w) sai suka fada cikin rudewa kamar yadda zamu gani.
Wanda ya haramta wato: Umar dan Khaddabi ya fadi cewa; Mutu'a ta kasance a lokacin Annabi (s.a.w) amma shi ya hana, sai ya yi nuni da cewa; akwai auren a lokacin Annabi (s.a.w) amma shi yanzu ya hana. Kuma an yi tawiloli kan dalilin da ya sa ya hana, sai dai wannan ba ya kore cewa; shi ne ya haramta. Don haka mutu'a hukuncin musulunci ne da yake nan daram har alkiyama ta tashi, kuma babu wani lokaci da zai zo ba ta kasance daya daga cikin hukuncin shari'a ba wanda yake da amfani mai matukar yawa ga al'umma.
Mutu'a ba zata gushe ba tana nan a matsayin hanyar warware matsalolin yammacin duniya, da latin Amurka, da Afrika da sauran nahiyoyi gaba daya, ba zata gushe ba a matsayin hanyar warwarar matsalolin al’umma da nisantar zina, ko kuma a lokacin tafiya da cakude, ko a matsalolin gidan samari, ko gidajen haya da za a iya auren 'ya'yan juna don ya halatta cakuduwar zaman tare.
Mutu'a zata iya warware matsalar fasikanci ga dalibai da cakuduwa da zaurawa da takan kai su ga lalacewa, kuma tana iya daidaita sahun karuwai da suka saba mu'amala da mazaje daban-daban ba zasu iya aure maras iyaka ba. Hada da matsalar mutanen da suke tsayawa titina don su samu wanda zai dauke su; irin wadannan mutanen suna iya samun masu shiryar da su domin su daina shashanci su koma hanyar shiriya.
Wani yana iya cewa; mutu'a tana da dokokin shari'a, shin  da wannan lamarin da muka lissafa zai yiwu a kiyaye wadannan dokokin kuwa? Amsarmu a nan ita ce E. Zai yiwu a kiyaye dokokinta, matakin farko dole ne mutane su san cewa; addini ne, sannan kuma a sanar da mutane dokokinta domin su kiyaye, sannan kuma su sani cewa auren mutu'a aure ne fa suke yi ba shashanci ba, don haka dole ne su kiyaye kimar lamarin aure.
Aure ne mai daraja kamar sauran aure, don haka da da za a iya samu dansu ne, sai dai bambancinsa da aure maras iyaka ya shafi abubuwa ne kamar; gado, da wajabcin ciyarwa, da raba kwana, da saki, wannan lamarin ne ma ya sanya shi kasancewa mai sauki matuka, kuma wannan ne ma ya sanya shari'a ta kira shi da auren "Mutu'a", mutu'a a larabci tana nufin "Jin dadi".
Idan Imam Ali (a.s) yana cewa: "Ba don Umar ya haramta auren Mutu'a ba, da babu wanda zai yi zina sai fasiki" . Shin a cikin al'ummarka akwai wanda ya taba tunanin yadda za a warware matsalar saduwa barkatai, da warware matsalar mata masu zaman kansu, da masu jin tsoron zina kuma sun rasa mai aurensu, da masu istimna'i (jawo mani da fitar da shi da hannunsu ko wani abu da kansu) har rayuwarsu ta lalace gaba daya, da matsalolin cakuduwa da juna, da ma masu shirin fina-finai (fila-filai) suna cakuduwa da juna?!. Hada da mazajen da matansu suke tura su gun matan banza saboda mummunan hali da suke musu kamar na "Nushuzi" .
 Sai dai kada mu manta a auren mutu'a ba dole ba ne a sadu don ana iya shardanta masa rashin saduwa, ana iya yin sa misali don zama tare a mota a tafiya har a isa inda za a rabu, ko wurin wasan kwaikwayo, ko zama a wurin kallo, da makamancinsu.

Hafiz Muhammad Sa'id
Haidar Center for Islamic Propagation
+234 803 215 6884 (Text only or (Line, Tango, Viber, Whatsapp, Telegram)
(hfazah@yahoo.com) (hfazah@hotmail.com)
Tuesday, October 13, 2009 - Shawwal 24, 1430 - Mihir 21, 1388
comments Masu kallo
Suna:
Adireshin Email:
* ra'ayi: