bayyinaat

Published time: 22 ,April ,2017      17:01:48
Wadannan dukkaninsu sun tafi akan halarcin auren mtutu'a suna masu dogara da wannan ayar, har wasunsu ma sun kara kalmar "zuwa wani lokaci" a gaban wannan ayar kamar haka:
Lambar Labari: 87




Dalilan Kur'ani
Ayar nan ta:  فَمَا اسْتَمْتَعْتُم بِهِ مِنْهُنَّ فَآتُوهُنَّ أُجُورَهُنَّ فَرِيضَةً  "Abin da kuka ji dadi da shi daga gare su, to ku ba su ladansu bisa wajibi”
Wannan aya tana nuna dalilin halarcin auren mutu'a, kuma akwai manyan sahabbai da manyan malamai da suka tafi a kan haka kamar Imam Ali (a.s) da Abdullah dan Mas'ud, da Ubayyu dan Ka'ab, kuma wadannan su ne madogara wajan fahimtar ma'anar Kur'ani gun Sunna da Shi'a. Daga cikin tabi'ai akwai irinsu: Sa'id bn Jubair, da Mujahid, da Katada, da Saddiyyi.
Wadannan dukkaninsu sun tafi akan halarcin auren mtutu'a suna masu dogara da wannan ayar, har wasunsu ma sun kara kalmar "zuwa wani lokaci" a gaban wannan ayar kamar haka:  فما استمتعتم به منهنّ إلى أجل فآتوهنّ أجورهنّ، "إلى أجل" Domin su nuna ma'anarta da tafsirinta cewa game da auren mutu'a ne. Abdullahi dan Abbas ya kasance yana rantsewa cewa wannan aya ta sauka game da mutu'a ne. mai son karin bayani yana iya duba tafsirai kamar: Tabari, da Kurdabi, da Ibn Kasir, da Kasshaf, da Durrul mansur, da Ahkamul Kur'ani na Jassas , da Sunan Baihaki , da sharhin Nawawi na Muslim , da Mugni na Ibn Kuddama . Kuma ana iya duba: Ahkamul Kur'an na Jassas: 2/147, Sunanul Kubura: 7/205, Almugni fil fikhil Hanafi: 7/571, Al'jami'u li Ahakamil Kur'an: 5/130.
Dalilin Mutu'a Daga Sunna
Akwai ruwayar da ta zo a Hadisin Annabi (s.a.w) da take nuna halarcin auren mutu'a kamar haka. Daga Abdullahi dan Mas'ud ya ce: Mun kasance muna yaki tare da manzon Allah (s.a.w) ba mu da mata tare da mu, sai muka ce: Ko zamu fidiye kawukanmu! Sai ya hana mu wannan, sannan sai ya yi mana rangwame da mu yi aure da mace da (sadakin) tufafi zuwa wani lokaci, sannan sai ya karanta wannan ayar a karshen maganarsa kamar haka:
يَا أَيُّهَا الَّذِينَ آمَنُوا لاَ تُحَرِّمُوا طَيِّبَاتِ مَا أَحَلَّ اللهُ لَكُمْ وَلاَ تَعْتَدُوا إِنَّ اللهَ لاَ يُحِبُّ الْمُعْتَدِينَ
"Wato: Ya ku wadanda kuka yi imani, kada ku haramta dadadan abin da Allah ya halatta muku, kuma kada ku yi shisshigi, Allah ba ya son masu shisshigi" . 
Kuma nufinsa da karanta wannan ayar saboda haramcin da aka yi lokacin halifa na biyu ne. Sannan sai Adiyya ya shiga bayanin hukunce-hukuncen wannan aure. Wannan hadisin ya zo a Kitabun Nikha (wato: Babin Aure) a Sahihul Buhari, da Kitabun Nikha a littafin Muslim, da Kitabun Nikha a Masnad Ahmad bin Hambal.
Dalilin Mutu'a A Ittifakin Malamai
Amma idan muka duba Ijma'in Malamai (Ittifakin Malamai), babu wani sabani game da halaccin auren mutu'a tsakanin dukkan musulmi kamar yadda babu sabanin kan cewa halifa na biyu Umar dan Khaddabi ne ya haramta shi. Wannan yana nuna mana akwai dalilai na Kur'ani da Sunna da Ijma'in malamai a kan halaccin auren mutu'a. Kuma ya zo a Masnad Ahmad bn Hambal: 1/402, da Tafsiru Tabari: 5/9, da Aljami'u Li Ahkamil Kur'an: 5/132.
A littafin Tamhid, na Ibn Abdulbarr, yana cewa: Malamai sun hadu a kan cewa auren mutu'a babu shaidu a cikinsa, kuma shi aure ne zuwa wani lokaci, kuma rabuwa a cikinsa tana kasancewa ba tare da saki ba, kuma babu gado tsakaninsu .

ASALIN SABANI KAN AUERN MUTU'A
Bisa ga abubuwan da suka faru, idan mun duba zamu ga sabanin da ake da shi game da auren mutu'a ya taso ne sakamakon shafe hukuncinsa da haramta shi da ya faru a lokacin halifancin Umar dan Khaddabi. Domin idan mun duba zamu ga halaccinsa lokacin Manzo (s.a.w) da kuma lokacin halifa na farko, da wani bangare na rayuwar halifancin halifa na biyu, har sai da halifa na biyu ya fadi mash'huriyar kalmarsa da yake cewa: "Mutu'a biyu (wato auren mutu'a da hajjin tamattu'i) sun kasance a lokacin Annabi (s.a.w) amma ni na hana su, kuma zan yi ukuba (ladabi) a kan yin su" .
Malamai gaba dayansu sun tafi a kan cewa a fili yake haramcin ya zo daga halifa na biyu a karshen kwanakin halifancinsa, wannan kuma shi ne abin da Ata' yake kara karfafawa yayin da yake cewa muna yin auren mutu'a a lokacin Manzon Allah (s.a.w) da Abubakar, da Umar, har sai da ya kasance a kwanakin karshe na halifancin Umar, sai Amru dan Haris (ko Hurais) ya yi mutu'a da wata mata da Jabir ya gaya mini sunanta amma na manta, sai matar ta yi ciki, sai labarin ya je ga Umar, sai Umar ya hana yin auren mutu'a . 
Wannan haramcin ya zo a littattafai masu yawa, sannan kuma da kausasawa kan wanda ya saba masa, ta yadda ana iya jefe koda kuwa kabarinsa ne bayan mutuwarsa. Sannan kuma Umar ya hana auren ne a kusan karshen rayuwarsa; Duba: Almusannif na Abdurrazak bn Hammam: 7/467, da Muslim sharhin Nawawi: 6/127, da Masnad Ahmad: 3/304, da Sunanul Kubura: 7/237.
Ya ci gaba da cewa, amma wannan haramcin ba kamar sauran haramci ba ne domin shi haramci ne na ladabi da ukuba, kuma haramci ne tare da tsoratarwa da jifa. Ku duba ku gani Umar yana cewa: Da labari ya zo mini cewa wani mutum ya yi shi (Auren Mutu'a), sannan kuma ya riga ya mutu, da na jefe kabarinsa .
Umar dan Khaddabi yana cewa: "Da labari ya zo mini wani mutum ya yi auren mutu'a da wata mata, ko da kuwa na same shi ya riga ya mutu to sai na jefe kabarinsa" . Wannan haramcin yana nuna mana cewa kafin lokacin halifa na biyu babu shi, Haramcin Auren Mutu'a bai zo ba sai daga Umar dan Khaddabi.
Wani mutumin Sham (Siriya) ya kasance ya zo sai ya auri wata mata auren mutu'a, sannan sai ya fita daga gari, sai Umar ya ji labari ya sa aka kamo shi. Sai ya ce da shi: Me ya sa ka yi? Sai ya ce: Mun kasance muna yi lokacin Manzon Allah (s.a.w) bai hana ba har Allah ya karbi ransa, da kuma lokacin Abubakar shi ma bai hana ba har Allah ya karbi ransa, sannan muna yi a lokacinka ba ka hana shi ba. Sai Umar ya ce: Na rantse da Allah da na riga na hana yin sa sannan sai ka yi shi, da na jefe ka! .
Wannan yana nuna har zuwa wannan zamanin babu wannan hanin, don haka daga nan ne wannan hanin ya faru. Don haka ne zamu ga imam Ali (a.s) yana cewa: "Ba domin Umar ya hana Auren Mutu'a ba, da ba wanda zai yi zina sai tababbe" . (ba wanda zai yi zina sai ya tabe ya tsiyata). Kuma dukkan malamai sun danganta haramcin zuwa ga Umar ne.
Ibn Abbas yana cewa: Mutu'a ba komai ba ce, sai rahamar Allah ga bayinsa da ya tausaya musu da ita, ba domin Umar ya hana ba, da ba mai yin zina sai ya tsiyata (ya tabe).
Idan mun dogara da wasu littattafai da bugunsu ya zo da kalmar haka: إلاّ شفى maimakon   إلاّ شقيto ma'anar maganar imam Ali (a.s) zata kasance ne kamar haka: Ba domin Umar ya hana mutu'a ba, ba wanda zai yi zina sai 'yan kadan.
Suyudi a littafinsa na Tarikhul khulafa, ya kawo cewa: Farkon wanda ya haramta auren mutu'a shi ne Umar dan Khaddabi . Wannan lamari yana nuna mana halaccinsa a asalin shari'a, duk da wasu daga malamai sun bi haramcin Umar har zuwa ranar mu wannan. Amma manyan sahabbai irinsu imam Ali suna da matakin da suka dauka sabanin haka karara domin ba su taba yarda da saba wa sunnar annabi (s.a.w) ba. Don haka ne zamu ga kalmar nan mash’huriya ta Imam Ali (a.s) da yake cewa: "Ba don Umar ya hana auren mutu’a ba, da babu wanda zai yi zina sai shakiyyi (tababbe)".
Ibn Hazam yana cewa: Wasu jama'a sun tabbatar da halaccinta har bayan wafatin Manzon Allah (s.a.w) kamar: Asma'u 'yar Abubakar, da Jabri dan Abdullah, Ibn Mas’ud, Ibn Abbas, Mu’awiya dan Abu Sufyan, Abu Sa’idul Khuduri, Ibn Hurais, da Salma da Ma’abad ‘Ya’yan Umayya. Daga Tabi’ai kuwa suna da yawa da suka hada da: Dawus, da Ada’, Sa’idu bn Jubair, Sauran malaman Makka .
Amma Kurdabi yana ganin cewa wasu daga sahabbai daga cikinsu akwai Umran dan Hasin, da kuma sahabban Ibn Abbas daga mutanen Makka da Yaman duk sun tafi kan halaccin auren mutu’a bisa mazhabar Ibn Abbas .
Haramta auren mutu'a da Umar ya yi yana daga cikin abin da imamiyya suka sanya shi daga cikin rashin cancantarsa ga halifanci, domin aikin halifa kamar yadda mai littafin Sharhul Mawakif yake fada shi ne; ya kare addini daga ragi da dadi, da kare shubuhohi da ake jifan sa da su. Ba ya rushe dokokin da manzon Allah (s.a.w) ya zo da su ba, wadanda misalansu suna da yawa, kamar yadda ya zo da sababbin dokokin da suka saba wa musulunci!.
Idan muka duba dukkanin hujjojin da suke kawowa kan haramcin auren mutu'a zamu ga ba sa wuce uku:
Wani Ra'ayin yana ganin cewa; Hanin da Umar ya yi wa auren mutu'a yana karfafa wa ne ga hukuncin da yake manzon Allah ya boye shi bai bayyana wa mutane ba, har sai da Umar ya hau halifanci sai ya shelanta wa mutane . Mai tafsirin yana nuna cewa; Ya tabbata ne gun Umar cewa; an shafe ta a lokacin Annabi (s.a.w) don haka shi ma sai ya shelanta hakan, wato; kamar ka ce; Annabi ya ba wa Umar hukuncin ne da zai shelanta shi idan ya kasance halifa, sai kowa ya jahilci hukuncin sai Umar ne kawai ya sani! .
Sai dai wannan tawili da yake nuna kin gaskiya a fili yana rushewa da dalilai kamar haka:
Umar da kansa ya ce: Halal ce a lokacin manzon Allah (s.a.w) amma shi ya hana kuma zai yi ukuba a kan hakan. Hada da cewa da Umar yana son shelanta wannan lamari ne, da ya fada tun farkon da ya zama halifa, amma sai karshen rayuwarsa ya fada cewa; ya haramta. Sannan kuma dukkan sahabbai hatta da dansa ba su yarda da haramcin da ya yi ba, kuma sun nuna cewa; Ba yadda za a yi haramcin Umar ya kasance hujjar shafe sunnar manzon Allah (s.a.w) sannan sai a yarda da shi .
Don haka a fili yake cewa Umar da kansa ya shelanta cewa; Shi ne ya haramta, kuma sahabbai masu yawa sun musanta masa wannan haramcin ba su karba ba. Sai dai wasu suna cewa; Tun da dai shi halifa ne, kuma sunnar halifofi an samu umarnin riko da ita, don haka sai mu yi riko da wannan haramcin na Umar!. Wadannan mutanen sun ga hadisan da aka ruwaito na haramcinta a lokacin manzon Allah (s.a.w) daga Samura bin Ma'abad ba su inganta ba, kuma sun ci karo da hadisan manyan sahabbai da ayyukansu tun lokacin manzon Allah (s.a.w) don haka sai suka koma kan wancan tawili na yin riko da sunnar halifofi. Duba raunin maganar haramcin auren mutu'a a lokacin manzon Allah (s.a.w) game da ruwayar Sahih Muslim a cikin Littafin: Tahzibut Tahzib: 6/349.
A nan sai mu ce: Babu yadda za a yi aikin halifan manzon Allah (s.a.w) ya saba da nasa, domin halifa yana kare abin da manzon Allah (s.a.w) ya bari ne, wannan ne ma daya daga cikin manyan dalilan da suke nuna cewa; Umar ba ya daga cikinsu. Kuma wannan lamarin ya sanya Shi'a cewa: Mun karbi maganarsa a kan cewa; Allah da manzonsa sun halatta, amma kuma mun yi watsi da nasa hukuncin yayin da yake cewa: Amma ni na haramta. Sannan kuma halifofin manzon Allah (s.a.w) ba su ne guda hudu ko biyar ba, halifofinsa su ne alayensa (a.s) guda goma sha biyu da ya hada su wuri guda da Kur'ani ya shelanta mana wajabcin riko da su, wanda na farkonsu shi ne imam Ali (a.s) na karshensu kuwa imam Mahadi (a.s).
Wasu kuwa suna cewa: Umar ne kawai ya san haramcin auren mutu'a ban da sauran sahabbai don haka sauran sahabbai kamar su imam Ali (a.s), da Abdullahi dan Mas'ud, da Ubayyu dan Ka'abu, da Jabir dan Abdullah, da Abdullahi dan Abbas da makamantansu masu yawa ba su san Annabi (s.a.w) ya haramta ba ne, don haka sai Umar ya shelanta a karshen rayuwarsa! .
Wannan magana ta fi kowacce rauni da nuni zuwa ga barnataccen tawili maras madogara da kan gado, hada da cewa; Umar yana cewa: Ni ne na haramta bayan ya shelata cewa; Allah da manzonsa sun halatta. Masu wannan ra'ayin suna kokarin ganin sun mayar da haramcin zuwa ga manzon Allah ne, don haka sai suka fada cikin dimuwar rashin sani da ayyana takamaimai wace shekara ce kuma a wane lokaci ne aka haramta ta.
Idan mun duba wadannan madogara da zamu kawo a kasa zamu ga sun yi maganganu masu yawa da karo da juna kan yaushe ne aka haramta auren mutu'a bisa shekaru mabambanta domin dai su kare wancan haramcin na Umar da samar masa mafuta .
Wasu su ce: Shekarar Hajjin bankwana, wasu kuwa, a yakin Hunain, wasu kuma a yakin Audas, wasu kuwa a Umarar ramuwa, wasu kuma a yakin Haibar, da masu ra'ayin yakin Tabuka, da masu cewa; a Bude Makka. Da wannan ne suka jingina wa shari'a wasa da hankulan mutane, sai suka so su hada dukkan wadannan maganganun, sai su ce; an halatta a nan, sai kuma aka haramta, sai aka sake halattawa, kuma aka sake haramtawa, haka aka yi ta yi har sau bakwai!. 
Ga Ibn Kayyim yana cewa: Ba a taba samun hukuncin shari'a da aka haramta kuma aka halatta shi har sau biyu ba, (balle sau bakwai)! .
Muna iya ganin yadda Kurdabi mai Littafin "Jami'u Li Ahkamil Kur'an"  ya kawo yadda kididdigar wannan haramcin ya kasance har a wurare bakwai. Ga kuma Ibnul Kayyim yana sake karfafa cewa; Babu wani hukunci da aka hana sama da sau daya, ko aka shafe shi sama da hakan .
Ganin yadda Masu wannan tunanin suka kasa samun mafita cikin alakakai din da suka fada ne, sun kasa danganta ingancin wannan haramcin ga manzon Allah (s.a.w), sun kasa wanke Umar domin yaya za a yi ya kasance shi kadai ne ya san wannan hukuncin sai karshen rayuwarsa ne ya shelanta shi, shi ma kuma saboda wani abu da ya faru ya ba shi haushi?! Sun kuma kasa gyara abin da hadisin sunnar halifofin manzon Allah (s.a.w) ya yi magana a kai, domin halifa yana kare abin da ya gada ne, ba ya soke shi ko ya kore shi ba. Don haka sai suka kirkiro wa Imam Ali (a.s) kagen cewa shi ma ya tafi a kan haramcin auren mutu’a alhalin shi ne Imami mai kariya ga shari’a, masani da hukuncin Allah da manzonsa, don haka sai aka nemi shafa masa kashin kaji, aka kirkiro masa kagen haramcin mutu’a, domin dai a sanya shi wanda ya yi tarayya da Halifa Umar cikin shafe hukuncin shari’ar manzon Allah (s.a.w).
Amma sai suka manta da abu guda yayin da suka nuna cewa; Imam Ali (a.s) ya nakalto wannan haramcin ne daga manzon Allah (s.a.w), suna masu jahilta da gafalar cewa; Ya tabbata babu sabani cewa; Umar ne ya haramta, don haka ne ma sai ga shi suna ta karo da juna kan cewa; a yaushe ne manzon Allah (s.a.w) ya haramta, sai wani ya ce; a shekara kaza, a wuri kaza, wani ma ya kawo nasa!.
Sai wani ya ce: Ali (a.s) ya ce: An haramta ne a Tabuka , wani kuma a Khaibari , da Hunai  a sanadi daya da dukkan ruwayoyinsa guda biyu suka tuke zuwa ga Zuhuri. A wani kuma an dangata masa cewa; ya ce da dan Abbas an haramta mutu’a a yakin Khaibar . Wannan kuwa domin sun san cewa; Abdullahi dan Abbas ya kasance yana halatta mutu’a har karshen rayuwarsa ne.
Sanadi daya ne a ruwayar kage da aka kirkira aka jingina wa Imam Ali (a.s) ita, daya tana cewa: An haramta a Khaibar ne, wata kuwa tana cewa; a Hunain ne . Wannan lamarin ya nuna raunin wannan kagen da aka jingina masa! A cikin sanadin ruwaya daya ta kage, sai ga maganganu biyu masu karo da juna . 
Amma sai muka samu wasu mutanen masu kariya ga shari’a sun musanta wannan maganganu da aka jingina wa manzon Allah da wasiyyinsa Imam Ali (a.s), muna ganin yadda Suhaili yake cewa: Wannan mummuna ne, wannan karya ce. Haka nan Ibn Abdul Barr, da Baihaki, da Ibn Hajar Askalani, da Kastalani mai Irshadus Sari, da Ainu mai Umdatul Kari; suka ce: Haramcin Mutu’a a Khaibar babu wani ma’abocin tarihi da ya ruwaito shi. Don haka babu wani wanda ya rage a kan cewa; wani ya haramta, sai dai kawai haramcin nan na Umar da aka yi ittifaki a kansa .
Don haka ne kuma sai suka koma kan cewa; Ai Ibn Abbas shi ma ya daina fadin haramcinta, amma sai ga su Ibn Hajar, suna cewa: Duk da Ali (a.s) ya gaya masa da kakkusar murya cewa; haramun ne, amma har ya mutu bai daina fadin halaccin auren mutu’a ba .
Amma a wani wurin sai ga Ibn Kasir ya kawo dainawar Ibn Abbas ga fadin halaccinta, don haka yanzu babu wani dai wanda ya rage kan haramcinta sai maganar harmancin nan da Umar ya yi mata, kuma masu goyon bayansa ba su iya kare shi kan abin da ya yi ba ta kowace hanya. Sun kago wa manzon Allah (s.a.w) hadisai kirkirarru, sun kuma ce: Imam Ali (a.s) shi ma yana cewa; An haramta, sannan sun koma suna neman cewa Ibn Abbas ma ya daina fadin halaccinta, duk dai don kariya ga wancan haramcin na Umar da aka yi ittifaki a kan shi ya haramta!
Don haka muna iya ganin wanda aka ruwaito ya halatta ta a ruwayar da aka kirkira wa manzon Allah (s.a.w) Zuhuri ne, shi kuwa Zuhuri malamin fadar Banu Umayya ne, kuma Imam Sajjad (a.s) ya yi masa nasiha kan abubuwan da yake yi na halatta musu abin da suke so da haramta abin da ba sa so, amma wasikarsa ba ta yi wa Zuhuri tasiri ba. Wannan wasikar tana nan hatta da Gazali mai littafin "Ihya’u Ulumuddin" ya kawo ta . Sannan kuma Zuhuri ya kasance mai tsananin saba wa imam Ali (a.s) ne, ya kasance mutum ne wanda yake kirkiro hadisai yana jingina wa Ahlul-baiti (a.s), har ma ya kirkiro cewa; Abubakar da Umar ne suka yi wa Sayyida Fadima (a.s) salla, haka nan idan ya tashi kirkirar kage sai ya jingina wa Ahlul-baiti (a.s).
Sannan muna iya ganin yadda malamai daga tabi’ai masu yawa suka yi wannan auren, muna ganin yadda Abdulmalik dan Abdulaziz dan Juraij, wanda ya mutu a shekara ta 149 H, wanda yake daga manyan tabi’ai, kuma daga malaman fikihu da hadisi, daga malaman Sihah assitta, wannan mutumin ya auri sama da mata casa’in auren mutu’a, kuma ya yi wa ‘ya’yansa wasiyya da kada su auri wasu matan saboda matan babansu ne, muna iya duba "Siyaru A’alamun Nubula" da sauran littattafai .
Kamar yadda ya zo cewa; Yahaya dan Aksam yana cewa da wani shehin Basara: Da wa ka yi koyi a auren mutu’a? sai ya ce: Da Umar dan Khaddabi. Sai ya ce: Yaya haka, alhalin ka san cewa shi ne ya fi kowa tsakanin kiyayya da ita a cikin mutane? Sai ya ce: Saboda labari ingantacce ya zo cewa; ya hau kan mimbari, sai ya ce: Hakika Allah da manzonsa suna halatta mutu’a biyu (wato; auren mutu'a, da hajjin tamattu'i) kuma ni ina haramta su, kuma ina yin ukuba a kansu, sai muka karbi shedarsa, ba mu karbi haramcinsa ba .
Haka nan Yahaya dan Aksam ya hana Ma’amun Abbasi (sarkin Abbasawa) shelanta halaccin auren mutu’a da da’awar cewa; Zai sanya fitina cikin al’umma, yayin da Ma’amun ya soki Umar dan Khaddabi a kan soke hukuncin Allah da manzonsa a shari’a, bai gushe ba har sai da ya yi galaba kan Ma’amun da kada ya shelanta hakan .
Da wannan ne zamu ga cewa; Auren mutu'a yana nan a halaccinsa daram, kuma babu wani wanda Allah (s.w.t) ya yi umarnin karbar umarni da haninsa ba tare da raddi ba sai manzon Allah (s.a.w), don haka muna iya ganin cewa; wadanda suka haramta Auren Mutu'a sun yi riko da umarnin Umar ne, wadanda kuwa suka halatta sun yi riko da umarnin Allah da manzonsa ne!.
Don haka ne Shi'a a matsayinsu na masu biyayya ga kawai abin da manzon Allah (s.a.w) ya zo da shi, da raddin duk wani abu ko daga wa yake kuwa, sun yi riko da wannan halaccin na Allah da manzonsa (s.a.w) har abada.
Auren Mutu'a shi ne abin da Ahlul-baiti (a.s) ba su taba yin boyon halaccinsa ba a cikin umarnin Allah da manzonsa a kowane hali, ba su taba kuma yin takiyya a kansa ba. Domin neman albarkar masu albarka, imaman shiriya da rahama, bari mu kawo tattaunawar Imam Muhammad Bakir (a.s) wasiyyin manzon Allah (s.a.w) na biyar, wato halifansa na biyar cikin alayensa Ahlul-baiti (a.s), mu ga yadda ta kasance da shi da wani mutum Allaisi wanda ba ya daga cikin mabiya tafarkinsu;
Al’abi ya ce: A cikin littafin Nasruddurar: An rawaito daga Abdullahi dan Mu’ammar Allaisi ya ce da Abi Ja’afar (a.s): Labari ya zo mini cewa kai kana bayar da fatawa da yin auren mutu’a? sai Imam Bakir (a.s) ya ce: Allah ya halatta a littafinsa kuma Manzon Allah (s.aw) ya sunnanta, sannan sahabbansa sun yi aiki da ita, sai Abdullah ya ce: Ai Umar ya hana yin ta. Sai Imam Bakir (a.s) ya ce: Kai kana kan maganar sahibinka (Umar), ni kuma ina kan maganar Manzon Allah (s.a.w). Sai Abdullah ya ce: Shin zai faranta maka rai (‘ya’yan) matanka su aikata haka? Sai Abu Ja’afar (Imam Bakir) (a.s) ya ce: Kai wawa? Wannan da ya halatta a littafinsa, kuma ya halatta ga bayinsa ya fi ka kishi, da kai da wanda ya hana, yana mai dora wa kansa nauyi, a yanzu zai faranta maka rai cewa ‘yarka tana karkashin auren wani masaki daga masakan garin Yasrib (Madina)? Sai ya ce: A’a. Sai Imam Muhammad Bakir (a.s) ya ce: Me yasa kake haramta abin da Allah ya halatta? Sai ya ce: Ba na haramtawa, amma dai masaki ba tsarana ba ne. Sai ya ce: Ai hakika Allah ya yarda da aikinsa ya so shi, ya aura masa Hurul-i’n, a yanzu kana kin wanda Allah yake son sa? Kana kin wanda yake tsara na Hurul-i’n din aljanna saboda shisshigi da girman kai? Sai Abdullah ya yi dariya ya ce: Wallahi ba na ganin kirazanku (zukatanku) sai mabubbugar ilimi, sai ‘ya’yan itacensa suka zama a hannunku, ganye kuwa ya rage a hannun mutane .
Muna ganin yadda Abu Ja'afar Imam Muhammad Bakir (a.s) ya yi magana kan auren mutu'a da halaccinta, da kuma cewa; a aure babu bambanci tsakanin ma'abota sana'o'i ko kabilu. Yana mai kawar da jahiliyyar nuna fifiko tsakanin mutane da kabilu kan aure, wacce aka raya a cikin musulunci bayan wafatin manzon Allah (s.a.w).

Hafiz Muhammad Sa'id
Haidar Center for Islamic Propagation
+234 803 215 6884 (Text only or (Line, Tango, Viber, Whatsapp, Telegram)
(hfazah@yahoo.com) (hfazah@hotmail.com)
Tuesday, October 13, 2009 - Shawwal 24, 1430 - Mihir 21, 1388

comments Masu kallo
Suna:
Adireshin Email:
* ra'ayi: