bayyinaat

Published time: 08 ,April ,2018      15:10:57
SAHABI: Sahabi kalmar larabci ce da a kan kalle ta a lokuna da wasu fuskoki: Na farko duban kalmar a Luga da abin da take nufi; 1. Wanda ya lizimci abu kamar idan ya saba da yawo da wata riga da ta zama ana tuna shi da ita. Ko ya saba da kiwon shanu da in an gan shi ana tambayarsa shanun. 2. Ko mai mallakar abu, kamar mai gida, mai littafi da sauransu. Ko mai mallakar tasarrufi da abu.
Lambar Labari: 97
SHIN DA GASKE ‘YAN SHI’A SUNA ZAGIN SAHABBAI?

DA SUNAN ALLAH MAI RAHAM AMAI JIN KAI
AMINCINSA YA TABBATA GA ANNABISA DA ALAYEN DA MASU BIYAYYA GARE SU DA SHIRIYA

KALMAR: SAHABI, ADALCI, ZAGI, LA’ANA.

SAHABI: Sahabi kalmar larabci ce da a kan kalle ta a lokuna da wasu fuskoki: Na farko duban kalmar a Luga da abin da take nufi;
1. Wanda ya lizimci abu kamar idan ya saba da yawo da wata riga da ta zama ana tuna shi da ita. Ko ya saba da kiwon shanu da in an gan shi ana tambayarsa shanun.
2. Ko mai mallakar abu, kamar mai gida, mai littafi da sauransu. Ko mai mallakar tasarrufi da abu.
Abu ba ya iya zama sahibin abu sai idan ya zama ya lizimce shi muddar da za a iya kiran sa da sahibinsa ne. Ko kuma lamari ne da ya shahara da shi har ya zama ana buga misali da shi kamar sahibin kifi ga annabi Yunsu (a.s).
Arragib Esfahani yana cewa: "Sahibi shi ne mai lizimta ... ba bambanci ta kansace da jiki don shi ne asali kuma ya fi yawa, ko ta kasance da wani la'akari. Ana cewa da mai abu sahibinsa ne, haka nan wanda yake mallakar tasarrufi da shi”. [Mufradatu Alfazil Kur’anil Karim; Arragib Al’esfahani: 275].
Na biyu: Idan mun duba a istilahi kuwa an samu bayanai daga malamai, sai dai zamu zabi wanda ya fi shahara na Ibn Hajar Al’askalani Asshafi’i saboda shi ne mafi ingancin bayanin shahabi gun manyan malaman Sunna kamar Buhari da malaminsa Ahmad bn Hambal da mabiyansu. Ya zo kamar haka cewa: "Sahabi shi ne wanda ya hadu da Annabi (s.a.w) yana mai imani da shi kuma ya mutu a kan musulunci”. [Al’isaba fi Tamyizis Sahaba; Ibn Hajar: sh 10]. Malamai sun fadada sharudan zama sahabi bisa wannan Bayani kan cewa:
a. Zamansa da shi ya tsawaita ko ya gajarta.
b. Ya ruwaito daga gare shi ko bai yi ba.
c. Ya yi yaki tare da shi ko bai yi ba?
d. Bai gan shi ba saboda wani dalili kamar makanta ko ya gan shi.
e. Yana mai imani da shi  ba da waninsa ba.
A nan ne zamu ga suna da sabani kan wasu mas’aloli da suka shafi hakan kamar cewa idan ya yi imani a lokacin annabi (s.a.w) sai ya yi ridda, sannan sai ya dawo bayan wafatin annabi (s.a.w)! shin yana nan a sahabi ko tabi’i ne. Ko kuma batun cewa imanin zahiri ya wadatar ba dole ne ba ne imaninsa ya zama na gaskiya saboda babu wanda ya san gaibi saI Allah. Da wanan ne da yawa daga cikin munafukai da masu raunin imami zasu shiga cikin sahabanci [Tabakat; Ibn Sa’ad: j 2, sh 56][Al’ma’arif; Ibn Kutaiba: sh 54, 131, 142].
Haka nan game da gani kansa shin sai ya zama yaro mai ganewa [mumayyazi] ko kuwa ko da karami ne sosai. Shin sai ya yi imani da shi ko kuwa ya isa ya san cewa annabi ne da zai zo nan gaba sai ya mutu kafin aiko annabi [kamar Bahira]. A cikin wannan mas’alar akwai bayanai masu yawa da magana kansu tsawaitawa ne.
Sai dai idan mun koma tarihin musulunci zamu ga bayanin sahabi da wadannan malamai ya samo asali ne daga kallon tarihi ba daga ainihin ma’anar sahabi ba. Musulunci bai zo da wani Istilahi kan kalmar sahabi ba da ya wuce na Luga. Duk wani abu da muke gani a Istihali to daga su kansu musulmi ne bisa ijtihadodinsu da suka dogara a kansa ba tare da koma wa Kur'ani ko ruwaya ba.
A dunkule: Duk wani musulmi a bisa wannan bayanin zai shiga cikin sahabbai don haka daular manzon Allah (s.a.w) baki daya tana kunshe ne da sahabbai sai wanda bai hadu da shi ba. Wannan yana nufin ke nan akwai mutane 120 000 ko sama da haka da zamu kira su sahabbai saboda sun hadu da annabi (s.a.w).
Bayanin Kur'ani: Kur'ani yana ganin sahibanci kamar yadda take a luga ne, sakamakon haka ne zamu ga ya zo da sahibanci tsakanin muminai [Kahfi 26], tsakanin kafiri da mumini [Kahfi 34-37], tsakanin da da uba [Lukman 15], tsakanin kafirai biyu [Kamar 29], tsakanin annabi da al’ummarsa [Takwir 22], tsakanin dabba da mutum [Kalam 48], da tsakanin mutum da wuri [Kalam 17].
A nan ne zata bayyana gare mu a fili cewa akwai bambanci tsakanin Kur'ani da musulmai a kan mas’alar sahabbai tun daga marhalar bayanin waye sahabi. Idan muka bi diddigin wannan kalma ta sahabi da ta zo sau 98 a Kur'ani mai girma zamu ga ba ta kawo wasu sharuda daga cikin sharudan da su mutasharri’a [musulmai] suka bayar ba. Sannan suhba ba ta ba da wani matsayi ita kanta idan ba ta hadu da aiyuka na gari ba kamar yadda zai baiyana a bahasosi masu zuwa [sabanin yadda maso dokar "Adalcin duk wani Musulmin zamanin Annabi" suka sauwara].


ADALCI
An yi bayanin adalci a takaice da cewa: Adalci shi ne mallakar kai [hali ne da ya kafu a rai] da yake sanya mutum lizimtar tsoron Allah; na barin duk wani haram da yin duk wani wajibi [Tahrirul Wasila; Al'ijtihad wat Taklid: m 28].

ZAGI
Zagi shi ne ka shifanta abu ko wani mutum da kaskantarwa ko tauye daraja da kimarsa. Haka nan zagi ne a muzanta wani mutum ko wani abu a magana amma ba tare da kazafi ba. [Almufradat: 255][Majma’ul Bahrain: 2; 80. 6; 98][Lisanul Arab: 1; 455. 12; 318][Assihah: 1; 144].
 Sakamakon haka idan ka sifanta abu da yadda yake kamar yadda yake a nan ba ka zage shi ba. Don haka ne ma idan aka hakaito wani abu da ya faru game da wasu mutane bisa yadda lamarin yake da ya kunshi wasu kurakurai da suka yi hakan ba a kiran sa zagi. Haka nan ma raddi ko nakadin wani abu da mutum ya yi ba a kiran sa zagi. Da wannan zagi ne ke nan da Kur'ani ya cika da zagin mutanen farko!.

LA’ANA
La’ana daga Allah (s.w.t) shi ne ya kore wani daga rahamarsa, amma idan aka ce wani mutum ya yi la’ana; yana nufin ya yi addu’a Allah ya kore wanda ya la’ana daga rahamarsa. Haka nan idan aka la’anci wani abu to ana addu’ar Allah ya cire albarka da rahama daga gare shi. Kuma abin da yake lizimtar haka shi ne; abin da aka la’anta ya shiga karkashin fushin Allah madaukaki ke nan. [Almufradat: 471][Majma’ul Bahrain: 6; 309][Annihaya: 4; 255][Assihah: 4; 2197].
Sakamakon haka ne zamu ga duk wanda ya yi la’ana to ya yi addu’a ne Allah ya nisantar da abin la’anarsa daga rahama. Idan wancan ya cancanci nisanta daga rahama to addu’ar karfafawa ne da neman hakan daga Allah, amma idan bai cancanci la’ana ba to wannan addu’ar ba ta karbuwa.

ASALIN MAS’ALAR
Mas’alar zagin sahabbai da ake yarfe da ita ga shi’awa mabiya Ahlul-baiti (a.s) mas’ala ce ta siyasa da tarihi yayin da sarakunan umayyawa da abbasawa suka ga cewa masoya Ahlul-baiti (a.s) suna da yawaita abin da suke gani a matsayin tonon asiri ga mulkinsu da bai doru bisa ingantacciyar hujja ba sakamakon cewa manzon Allah (s.a.w) ya yi wasiyya ga al’umma da biyayya ga alayensa (a.s), sai dai al’umma ba ta yi aiki da wasiyyar ba, kuma idan dai alayensa suka samu karfi to wannan yana nufin ke nan kai tsaye wata rana za a samu juyin da zai kai su ga rike ragamar jagorancin al’umma. [Al’imamul Sadik wal Mazahibul Arba’a: 4; 614-623][d.s.s].
 Kuma tare da cewa lokacin ya tsawaita daga wancan zamanin da ya gabata, sai dai mutanen da suka sha daga farfagandar malaman fadar wadannan sarakuna har zuwa yau musamman wadanda suka doru kan koyarwar umayyawa har zuwa yau suna maimaita wannan kagen da yarfen kan mabiya alayen annabin rahama da aka fi sani a shi’awa.
Da yawa dokokin da sarakunan umayyawa ko abbasawa suka assasa da suke da karfi har yanzu a duniyar musulmi suka koma makoma da aka sallama da su kamar dai wahayin Kur'ani ko Sunna, kai sun fi Kur'ani da Sunna ma karfi. Kur'ani da Sunna suna kunshe da musuluncin gaskiya wanda musulmi suka yi ittifaki a kansu, amma mas’alolin da suka zo daga baya mas’aloli ne na ijtihadi da ana iya sabani a kai, sai dai mas’alar cewa "Duk musulman da suka yi zamani da annabin rahama adalai ne” mas’ala ce da ta zama doka a daulolin umayyawa da abbasawa da turakawa da ta ci karo da Kur'ani da Sunna amma kuma ta shafe su, har sai aikin da yawan musulmi musamman masu tsananin kariya ga umayyawa suka zamo a kanta suke ba a kan Kur'ani da Sunna ba, kuma sakamakon dokar [ka'idar] ta samu cin karon da Kur'ani da Sunna da Tarihi sai aka yi wurgi da su.
Mas’alar cewa "Duk sahabbai adalai ne” da sarakuna suka kirkiro ta zama wata joka da duk mai son tsananta wa wanda ya yi riko da Kur'ani da Tarihi kan mas’alolin da suka faru game da musulmin farko da suka yi zamani da annabin tsira (s.a.w) ke amfani da ita. Mummunan abu shi ne ganin wanda ya saba wa wannan dokar a matsayin wanda ya zagi sahabi. Mafi muni abu a gun umayyawan wannan zamani shi ne dokar ta haura ta wuce kuma ta zarce zuwa matakin ganin fadin cewa "ba duk sahabai ne hujja ba" shi ma a matsayin tuhuma da zagin sahabai alhalin mas'aloli ne biyu mabambanta masu zaman kansu [wato mas'alar adalcin duk wani sahabi da hujjar magana ko aikin duk wani sahabi]. 
Sabawar dokar ga Kur'ani da Sunna da Hankali da Tarihi ne ya sanya wasu daga malamai suka ga ya kamata a sanya mata wani salo da usulubi don yanke lamarin baki daya sakamakon cewa ya saba wa gaskiyar addini. Sai suka bayar da fatawar yin shiru kan abin da ya faru cikin al’ummar musulmi ta farko kamar yadda zamu gani daga wasu manyan malamai irin su Albasari da Abuhanifa da Ibn Hambal.

HADAFIN SANYA DOKAR
Idan muka yi bincike a Tarihin musulmi zamu ga akwai sabuban kirkiro wannan dokar da ba ya buya ga wanda ya yi zurfi a tarihin musulunci kamar haka:
1. Kiyayya ga alayen annabi (s.a.w) da mabiyansu domin kange mutane daga fahimtar gaskiyar da suke kai.
2. Kariya ga sarakuna da ba su matsayin wakilan Allah (s.w.t) na gaskiya a kan mutane.
3. Rufe barna da fasadin sarakuna da zalunci da mugunta da ketar da kisa da suke aiwatarwa a kan al’ummar musulmi.
4. Hassada ga annabin rahama (s.a.w) da alayensa sakamakon tsarkin da Allah madaukaki ya yi musu falala da shi.
Sakamakon haka ne aka kara duk wani musulmi da ya yi zamani da annabin shiriya (s.a.w) [sahabi] a wannan sifa mai daraja. Ta yadda duk wata falala ta su sai da aka sanya kowa a ciki hatta a salati!.
5. Kare duk wani mugun kuduri da sharri da mummunan nufi na sarakuna da sunan kare sahabbai.
6. Sanya makomar al’umma a jagoranci da ilimi da addini da riko da igiyar wilaya ka da ta kebanta da alayen annabi (a.s) da ya yi wasiyya da biyaiya gare su hade da Kur'ani.
Annabi (s.a.w) ya yi wasiyya ga wannan al’umma da biyaiya ga Kur'ani da Ahlul-baiti (a.s) bayansa. Sanya wannan dokar yana nufin rushe wannan makoma da annabin shiriya ya sanya wa al’umma a matsayin makoma ta yadda zai bude kofar cewa duk musulmai daya suke, kuma kowanne ka rika zaka tsira. Kai tsaye suna son su nuna cewar wasiyyar da Allah da manzonsa suka sanya ta riko da littafin Allah da alayen annabinsa (s.a.w) ba abin la’akari ba ce.
7. Kautar da musulmi daga hakikanin musuluncin asali da rusa koyarwar annabin daraja (s.a.w) mai inganci, da batar da wasiyyar annabin daukaka (s.a.w).
Wadannan suna daga cikin hadafofin da suka sanya umayyawa da abbasawa karfafa wannan dokar da suka kirkira don cimma hadafofinsu. Kuma da sannun wannan zai baiyana gare ku dalla-dalla a cikin bahasosi mazu zuwa.


HANYOYIN KARE DOKAR
A lokacin da malaman Fada suka tabbatar da cewa wannan dokar ba zata iya nuna wa al’umma gaskiya ba saboda karo da juna da ke cikinta da Kur'ani mai girma da ya zargi wasu musulmai, ya soki wasu, ya la’anci ma wasu, ya muzanta wasu, ya yabi wasu, ya daukaka wasu, lamarin da yake nuna mana cewa ba duk musulmi da ya yi zama da manzon Allah (s.a.w) ne adali mai takawa da tsoron Allah ba, hasali ma akwai mai zumden annabi, da mai ganin ba ya adalci, da mai yi masa karya, da mai sukan matarsa Safiya da yi mata kazafi, da munafukai da suka kware kan munafunci, da sauransu, sai masu wannan dokar suka yi:
1.,2. Kokarin yin tawilin wannan dokar da tawiloli masu rauni matukar gaske, wani lokaci suna tawilin Kur'ani ne, wani lokaci kuma Sunna, wani lokaci kuma suka yi kiren karya ga annabin kamala kan wasu mas’aloli da nan gaba wasu daga cikin irin wadannan mas’aloli zasu baiyana idan mun zurfafa bayani.
3. Rusa dokar Kur'ani da ke cewa babu wani mai daraja a wurin Allah sai mai takawa, da Sunna mai nuni zuwa ga cewa mutane duka a wurin Allah daya suke ba tare da bambanci ba sai dai da tsoron Allah madaukaki. Allah ba shi da wani wanda yake karkata zuwa gare shi don kusanci domin babu shi, duk bayinsa ne abin mallakarsa. Kuma ko da annabinsa ne ya kauce hanya to ba shi da wani matsayi a wurinsa kamar yadda Kur'ani ya yi nuni da hakan.
Sai suka sanya zamani da wuri shi ne ma’aunin daraja da daukaka. Matukar wani ya yi zamani daya da annabi (s.a.w) ya hadu da shi ko ya zauna da shi wuri daya, balle kuma a samu surukuta ko auratayya to fa wannan shi ne ma’aunin matsayi a wurin masu kafa wannan dokar suna masu fancakali da watsi da Kur'ani, suna masu jefar da sunnar annabi (s.a.w) a kwandon shara.
3. Kokarin rusa duk wani wanda bai yarda da wannan ka’idar dokar ta umayyawa da abbasawa ba; kuma tun da shi’a ba zasu taba yarda da wani abu da ya saba wa Kur'ani da Ahlul-baiti (a.s) ba, to bisa yanayin abin da zai faru ke nan su ne tsautsayi zai fadawa. Da shi’a zasu yi wurgi da Kur'ani da Ahlul-baiti (a.s) to da an daga musu kafa, da sun samu lumfasawa da samun sukuni, sai dai sun rike su kam, sun yi alkawarin duk wahala zasu riki Kur'ani da Ahlul-baiti (a.s) a matsayin wasiyyar da annabin rahama (s.a.w) ya yi wa al’ummarsa.
A daya bangaren masu biyaiya ga koyarwar umayyawa da abbasawa sun sha alwashin sai sun fasikantar ko sun kafirta duk wani dan shi’a ko dan darika da ya yi riko da matsayin Kur'ani da Sunna kan wannan mas’alar ta rashin "Adalcin Duk Wani Sahabi”!.



TASIRIN MAS’ALAR
Sakamakon dokar "Adalcin Duk Wani Sahabi” da mahukunta suka gina har ta yi karfi a cikin marubuta da masana sai da ta yi jijiyoyi masu karfi ta yi rassa da ganye har ta yi fure da ‘ya’ya. Sai aka samu shigar mas’alar cikin duk wani lamari da wata mas’ala ta akida da fikihu da siyasa da duk wani fage a cikin al’ummar musulmi.
1. Duba bahasin sanadin ruwayoyi da ma'aunin gaskiyar ruwaya tana hannun makomar su waye mazajen ruwayar, sai dai kuma bahasin ruwayar yana da iyaka domin ba ya shafar sahabi. Da an ce a binciki mazajen ruwaya to fa ban da sahabin da ke ciki, domin Kalmar sahabi ta riga ta zaba daidai da adali. Da wannan ne Kalmar Sahibanci ta zama daidai da Adalci.
2. A sakamakon wannan dokar da suka sanya; sai Ali (a.s) da ya girma a hannun manzon Allah (s.a.w) ya sha daga iliminsa ya san komai na addinin musulunci, addini ya tsayu da kokarinsa da takobinsa, sai ya zama daidai yake da Abuhuraira [da Umar ya  yi masa bulala ya haramta hadisansa ya kira shi mai karya ga annabi] da bai zauna da annabi (s.a.w) ba sai shekara daya da ‘yan watanni a rayuwarsa, kuma annabi (a.s) ya aika shi Bahrain mai hidima ga gwamnansa bai sake dawo ba har annabi ya yi wafati sai lokacin halifancin Umar!.
A bisa wannan dokar sai Ali (a.s) da ya girma a hannun manzon Allah (s.a.w) ya sha daga iliminsa ya san komai na addinin musulunci, addini ya tsayu da takobinsa, sai ya zama daidai yake da Mu’awiya da ya rayu baki daya da shi da babansa da babarsa suna kiyayya da gaba da annabin rahama (s.a.w) ba su musulunta ba sai da suka tabbatar da takobi zata hau wuyansu, kuma a shekarar annabi (s.a.w) ta karshe babansa Abusufyan ya nemi annabin tsira (s.a.w) ya sanya dansa Mu’awiya cikin marubutansa. [masana suna cewa ya yi hakan ne don cimma wasu hadafofi kamar sanin sirrin annabi].
3. Da wannan lamari da ire-irensa ne sai ya zama al’ummar ba ta damuwa da karbar wani abu daga kowa ya fito, hasali ma ba ta san karba daga Ahlul-baiti (a.s) ba.  Duk wani wanda ya hadu da annabi (s.a.w) yana da ‘yancin ya kafa ra’ayi da nazari da ya so kuma kowa yana da zabin ya karba komai gabarsa da annabi (s.a.w) da alayen (a.s) kuwa!.
Daga karshe ma lamarin ya juya ga yanayi mafi muni cewar duk wani mutum yana da ikon kafa mazhaba ya lumfasa amma mazhabar alayen gidan annabi (s.a.w) ba karbabba ba ce. Duk wata shara da tuhuma da kage da kazafi da yarfe to bai halatta a dora su kan kowace mazhaba ba sai dai ana iya dora su kan mazhabar alayen Muhammad (s.a.w)!. Wannan ita ce makomar musulmai har zuwa yau!.
4. A bisa wannan dokar ne ya zama babu yadda za ka ki karbar ruwaya ko wani hukunci daga wanda ya kashe musulmai ya yi musu wulakanci ya keta hurumin Allah (s.w.t) da manzonsa (s.a.w), ya yi gaba da alayen manzon Allah (s.a.w), ya zo da bidi’o’i iri-iri a cikin musulunci, tun da ya hadu da annabin rahama (s.a.w)!.
Hatta da mutanen da manzon Allah (s.a.w) ya yi wasiyya ga Ali cewa zai yake su na daga masu warware alkawarin bai’arsa da suka yi hari kan musulmin Basara su ka yaudare su suka sare kawukansu bisa yaudara. Suka sabbaba kashe kusan sama da musulmai 17000 ko sama da hakan. Amma ba ka da hakkin ka yi raddin maganarsu cewa ba zata zama karbabbiya gun ka ba ko mai kuwa suka yi saboda sun hadu da annabi ko sun rayu da shi!. Haka nan lamarin yake game da marikawan Hawarijawa, da kuma Kasiteen albageen da manzon Allah (s.a.w) ya kira ta jama’a azzaluma.

MATSAYIN DOKAR
Kowace mas'ala da ake bincike a ilmance tana da lunguna da kwanoni masu yawan gaske da ta kowane loko za a iya kallonta, misali a wannan mas'alar muna iya yin tambayoyi masu yawan gaske kan cewa; shin mas'alar nan doka ce kawai a kwakwala ko tana kallon abin da ya faru a waje ne, jauharin addini ce ko kuwa abu ne ba na asasinsa ba, ma'ala ce ta nazariyya ko ta imani.
Idan mun duba sosai ta fuskar karshe da muka kawo a misali zamu ga wannan mas'alar a bisa dokar Kur'ani mai daraja mas'ala ce nazariyya ba imaniyya ba. Da wani bayani budadde dalla-dalla idan mutum ya mutu bai yi imani da cewa "Duk wani musulmi da ya hadu da annabi (s.a.w) adali ne" ba, babu wani abu da zai cutar da imaninsa ko samar masa matsala, hasali ma shi ne ya yi riko da koyarwar Kur'ani mai tsarki. Da wannan ne zai fito fili cewa mas'ala ce ta nazari ba ta imani ba, sai dai masu neman kare wannan mas'ala sun sanya ta sama da mas'alar imani ta yadda suke fasikantar da kafirta wanda ya yi riko da koyarwar Kur'ani kan wannan mas'alar.
Wane hankali ne zai yarda cewa an samu al'umma sama da 120000 a mafi karancin takadiri amma duk adalai ne masu takawa babu mai saba wa Allah ko daya a cikinsu!.
Don haka wasu daga malaman musulmi da suka yi riko da wannan dokar sai suka samu dabarbarcewa, a daya bangaren dokar ta rushe Kur'ani mai girma a lokaci daya kuma ana son riko da ita. Kur'ani yana kallon mutane daya ne sai da takawa babu ruwansa da cewa wannan ya yi zamani da annabi (s.a.w) ko kuwa? Dokar tana cewa Allah ya kalli mutane da bambanci da wasu har ya fifita wasu saboda zamani da wurin da aka haife su!.
Amma Ahlul-baiti (a.s) da mabiyansu shi'a ba su saba wa dokar Kur'ani ba sai suka zama sun yi laifi gun sarakunan umayyawa da abbasawa da malaman fada da suka gaji dakon wannan dokar mai rushe Kur'ani da Sunna. Sai dai kuma riko da Kur'anin ya jawo musu bakin jini da ba shi da misali ta yadda kullum suke shan yarfe da kage da sharrin cewa suna zagin sahabbai. Har ma wani malami a Kaduna daga cikin masu dakon koyarwar Banu Umayya da Wani sarki a arewacin Nigeria a watan December da ya gabata sun yi kira da maganin abin da suka kira zagin sahabbai!.
A daidai lokacin da masu dokar suke karfafa cewa ba su yarda da Ismar annabawa (a.s) a kowane fage ba sai a isar da sako kawai, har suka jingina wa annabawa sabo iri-iri, amma a daya bangaren suna karfafa cewa musulmin da ya yi zamani da annabi (s.a.w) shi yana da kariya daga sabo a inda hatta da annabawan Allah (s.w.t) ba su ba su kariya daga sabo a fagen ba. Haka nan ne malaman fadar umayyawa suka ci gaba da dakon wannan dokar da sanya al'ummar musulunci yin watsi da koyarwar Kur'ani da Hankali!.
Amma idan muka koma mas'alar zagi sai mu ga babu wani malamin shi'a ko daya da halatta zagin wani mutum balle kuma wani musulmi da ya yi zamani da annabi (s.a.w). Shi'a suna ganin cewa bai halatta ba ka zagi wani balle wani da wasu mutane suke girmamawa, bahasin ilimi don sanin waye za a karbi addini daga gare shi da kafa dalilin Kur'ani ko Ruwaya ko Tarihi kan hakan ba zai taba zama zagin wani sahabi ba!. 

"… a biyo mu ci gaban wannan bahasi a fitowa ta gaba ..."

Hafiz Muhammad Sa'id
hfazah@hotmail.com
+234 803 215 6884 [Tedt, Telegram, Biber, Whatsapp, Line, Tango, Wechat] Only.
HAIDAR CENTER
Friday, June 10, 2016
comments Masu kallo
Suna:
Adireshin Email:
* ra'ayi: