bayyinaat

Published time: 08 ,April ,2018      15:33:33
Tabbas musulmin farko da suka yi zamani da annabi (s.a.w) suna da nasu matsayin rigo da imani da daukar nauyin sakon annabin rahama (s.a.w) zuwa ga duniya lamarin da yake falala da daukaka ne mai girma, sai dai wannan ba ya nufin cewa duk musulmin da ya yi zamani da annabi (s.a.w) adali ne. Akwai bambanci tsakanin girmama al'umma sakamakon a cikinta akwai mutanen da suke tarihi ya yi sheda da daukakarsu da himmarsu da sadaukarwarsu da kuma hukuncin daidaikun mutanen da suke cikin wannan al'ummar.
Lambar Labari: 98
SAHABBAI GUN MUSULMI
Tabbas musulmin farko da suka yi zamani da annabi (s.a.w) suna da nasu matsayin rigo da imani da daukar nauyin sakon annabin rahama (s.a.w) zuwa ga duniya lamarin da yake falala da daukaka ne mai girma, sai dai wannan ba ya nufin cewa duk musulmin da ya yi zamani da annabi (s.a.w) adali ne. Akwai bambanci tsakanin girmama al'umma sakamakon a cikinta akwai mutanen da suke tarihi ya yi sheda da daukakarsu da himmarsu da sadaukarwarsu da kuma hukuncin daidaikun mutanen da suke cikin wannan al'ummar.
Idan muka ce mutanen gari kaza suna da girmama baki, wannan ba ya nufin cewa a cikinsu akwai wanda ba ya girmama baki ko ba ya ma son baki. Kamar fadinmu ne cewa mutanen Nigeria suna da arziki sai dai wannan ba yana nufin a hukuncin daidaikun mutanen kasar a samu talakawa ba, hasali ma talakawa sun fi yawaita da tazara mai yawan gaske. Idan mun duba yaren da mutane suke amfani da shi zamu ga ya ginu a kan irin wannan mas'ala "muhmala" ce ba "mahsura" ba kamar yadda yake a ilimin Mantik.
Imam Ali (a.s) yana gaya wa wasu daga sahabbansa da wasu daga cikinsu ma sahabban annabi (s.a.w) ne falalar sahabbai da suke da imani da aiki na gari fiye da sauran, yana mai cewa:
 "Ni na ga sahabban Muhammad (s.a.w) babu wani mutum daga cikinku da ya yi kama da su, sun kasance masu tsayuwa da kama mai jirkita suna masu kura, masu kwana sujada da tsayuwa". [Nahjul-balaga: Subhi Salih; sh 91].
A wani wurin yana cewa:
"Ina 'yan'uwana da suka hau hanya suka wuce bisa gaskiya?! Ina Ammar! Ina Ibnut Taiyihan! Ina Zus shahadatain! Ina tsararrakinsu daga abokansu da suka karanta Kur'ani, sai suka kiyaye shi, suka lura da umarninsa sai suka aiwatar, suka raya sunna, suka kashe bidi'a, an kira su zuwa jihadi sai suka amsa, suka aminta da jagora sai suka bi shi. [Nahjul-balaga: Subhi Salih; sh 264, Khutba 182].
Har zuwa yau musulmi a aikace ba su yi imani da cewa duk wani wanda ya yi zamani da annabi (s.a.w) to adali ne. Hatta da masu fadin cewa: "Duk wani sahabi adali ne" amma a aikace fa ba su yi aiki da hakan ba kuma ba su yarda da dokar ba. Ba na mantawa ina juya tashoshi sai na ga wata tasha ta wata kungiyar ahlussunna mai suna Africa tb3, a ranar 13-2-2016, kusan magariba zuwa issha lokacin Nigeria sun gayyaci wani bako mai suna Sheikh Abdulwahab Abdullah, yana ba da labarin wata mata da annabi (s.a.w) ya hana ta zuwa wani wuri ita kadai gudun ka da wasu su yi mata fyade, har yake kara wa da cewa ai sahabbai suna sabo ba ma'asumai ba ne, sai dai alherinsu ya fi sharrinsu!.
Abin mamaki ga mutanen da suke sukan shi'awa da cewa suna zagin sahabbai saboda sun yi riko da Kur'ani da Sunna kan cewa "Ba duk mutanen da suka rayu tare da annabi (s.a.w) ne adalai ba" sai ga shi suna tabbatarwa da bakunansu. A yanzu ke nan malamin kungiyar ahlussunna da ya fadi wannan maganar shi ma ya zagi sahabbai ke nan saboda yana ganin cewa a wannan lokacin zasu iya yi wa wannan matar fyade!?.

SAHABBAI GUN SAHABBAI
Idan muka duba tarihin alakar da ke tsakanin musulmin farko zamu ga ba su yarda da cewa duk al'ummar annabi (s.a.w) adalai ba ne, sun kasance suna musun duk wani mummunan abu da ya faru daga wasu daga cikinsu har ma suna zartar da hukuncin shari'a a kansu. Ba mu samu wani mutum ya yi karya ko zina ko shan giya a wannan zamanin sai annabi (s.a.w) ko wani daga musulmi ya kyautata aikinsa ko ya kira shi da adali ba.
 A nan ne tambaya zata iya tasowa cewar idan annabi (s.a.w) ko wani musulmi [sahabi] ya kalli wani sahabi da ya yi laifi ko wani zunubi mai girma a matsayin ba adali ba ne shin ya zage shi ke nan!?. Mu duba mu ga tarihi yadda sahabbai suka yi mu'amala da sahabin da ya yi wani laifi musamman ma idan ya girmama;
A lokacin da Khalid bn Walid ya kashe Malik bn Nuwaira tare da musulmi kusan 300 bayan aminci mai karfi da alkawarin Allah da ya ba su, kuma a wannan daren ya kwanta da matar Malik bn Nuwaira, sannan ya sare kawukan musulmi ya sanya su duwatsun murhun dahuwar abinci, zamu ga Umar dan Khaddabi ya la'ance shi. [Tabari: j 3, sh 241]. Har abada Umar bai taba cewa tun da ya ga annabi to shi ke nan abin da ya yi ya kyauta, sannan babu wani musulmi a tarihi da ya ce Umar ya zagi sahabi kan matakin da ya dauka.
Kuma ya la'anci Muhammad bn Talha kuma ya la'anci Abdullahi bn Zubair [Alkamil fit Tarikh; j 3, sh 358-359]. Haka nan Imam Ali (a.s) ya la'anci Abdullah bn Zubair [Murujuz Zahab: j 2, sh 54]. Bai ce wannan sahabi ba ne kan abin da ya yi na sakaci har aka kashe halifan musulmi. Babu wani wanda ya ke ganin hakan ya zama laifi ga Umar ko Ali ko sun zagi sahabi kan matakan da suka dauka.
Tarihin musulmin farko cike yake da abubuwan da ba su da dadin ji ga wanda ya koma masa saboda abin da ya faru na kauce wa wasiyyar annabi (s.a.w) ta biyayya ga Kur'ani da alayensa (a.s) bayansa. Wannan wani kuskure ne babba wanda ya faru da yake nuni da cewa al'ummar musumi da ta yi zamani da annabi (s.a.w) tana iya saba wa umarninsa bayansa kamar yadda ta saba masa a wurare masu yawa a lokacin rayuwarsa, lamarin da kai tsaye ya kore cewa duk musulmin da ya yi zamani da annabi (s.a.w) adali ne. kuma sahabban da ba su yarda da wannan sabawar ba sun nuna rashin yardarsu har wannan lamarin ya jawo wa al'ummar musulmi rabuwa gida biyu tun wannan lokaci tsakanin shi'awan alayen annabin tsira (a.s) ['yan shi'a] da shi'awan masu sabani da su [a dunkule ana kiran su 'yan sunna].
Wannan wani lamari ne da aka sallama masa cewa a lokacin annabi (s.a.w) akwai mutane iri-iri a jama'arsa, akwai masu adalci da kololuwar imani da masu raunin imani da ma munafukai, a wannan yanayin babu yadda za a iya amintuwa da cewa duk wani wanda ya hadu da annabi (s.a.w) ko da kuwa na minti daya ne to adali ne.

SAHABBAI A RUWAYA:
Kamar yadda muka yi nuni cewa a kowace al'umma ana samun na gari da waninsu, kuma sau tari a kan samu masu kololuwar imani kadan a cikin al'umma, sai kuma masu raunin imani da suka fi yawa a al'umma, sai kuma matsakaita wadanda suke dafa wa masu imani baya wurin ganin an samu daidaiton lamura. Idan mun duba zamu ga sahabbai masu karfin imani da lizimtar umarnin annabi (s.a.w) yawancinsu sun zama masu biyaiya ga wasiiyarsa da biyayya ga alayensa bayansa har ma Allah a littafinsa a surar Bayyina ya kira su da Khairul Bariyya [fiyayyun al'umma]. 
Sai dai akwai da yawa da suka saba musu kan wannan lamarin har ma suka takura su, sai da ta kai ga wasu daga cikinsu sun gama da rayuwarsu da kisa saboda imaninsu. Amma da yake muna son nuni da waccan dokar da aka sanya cewa "Duk wani musulmi da ya hadu da annabi (a.s) adali ne" da muke magana a kai, ba zamu fadada rayuwar wadannan bayin Allah masu imani da daraja ba. Zamu juya kan maganar masu raunin imani daga cikinsu wadanda ko dai suna saba wa Allah da manzonsa (s.a.w) da gangan, ko kuma imani bai ma shiga zukatansu.
Ruwayoyi masu yawa ne suka zo suna masu nuni da abubuwa da ba sa kirguwa da zamu kawo wasu misalai daga ciki. Ruwayar sahihul Buhari ta yi nuni da cewa akwai sahabbai da 'yar manzon Allah (s.a.w) ta yi fushi da su bayan shedawarsu da cewa fushinta shi ne fushin Allah!. [Buhari: j 2, sh 115. Buhari J 3, sh 35]. Ruwayoyi sun nuna fushinta ga mutane masu yawa daga mutanen Madina da na Makka daga cikin Muhajirai da Ansarawa kan abububuwan da suka faru bayan wafatin annabin rahama (s.a.w).
Haka nan sahihul Buhari ya ruwaito cewa a ranar lahira za a kora wasu mutane daga sahabbai da sun san ni na san su sai a shiga tsakanina da su, sai in ce ya Allah sahabbaina! Sahabbaina!. Sai a ce: Ba ka san abin da suka yi bayanka ba. Abin da ya fi jan hanakli shi ne yadda Buhari yake karfafa cewa babu wadanda zasu tsira daga cikinsu sai 'yan kadan. Litattafai masu yawa kuma ingantattu na ahlussunna sun ruwaito wannan ruwayar daga ciki akwai [Masnad Ahmad bn Hambal j 5, sh 50. Da: j 3, sh 281. Da: j 1, sh 225]. [Majma'uz Zawai'id: j 9, sh 367].
Kamar yadda ruwayoyi masu yawa ne suka kawo mas'aloli iri-iri da suka shafi sabawar musulmi ga umarnin annabi (s.a.w) a wancan zamanin. Akwai wadanda annabi (s.a.w) ya yi musu sheda da wuta kamar Kazman bayan ya yi yaki a Uhud har an ji masa rauni amma annabi (s.a.w) ya ce dan wuta ne [Al'isaba: j 3, sh 235].
Akwai Zussudayya wanda annabi ya aiki Abubakar ya kashe shi ya dawo bai kashe shi ba, ya aiki Umar ya kashe shi ya dawo bai kashe shi, duk suna cewa annabi yana salla ne. Daga karshe annabi (s.a.w) ya aiki Ali ya kashe shi sai ya tarar ya gudu [Al'isaba: j 1, sh 484, L 2446][Fathul-bari: j 6, sh 617, h 3610]. A nan akwai nuni da cewa musulmi suna saba umarnin annabi (s.a.w).
Haka nan ruwayoyi mutawatirai ne suka zo kan cewa annabi (s.a.w) ya yi wa Imam Ali (a.s) umarnin yakar nakisawa [jama'ar yakin Jamal] da kasitawa [jama'ar Mu'awiya] da marikawa [jama'ar Khawarijawa]. Haka nan annabi (s.a.w) ya yi wa wasu haddi saboda shan giya, wasu saboda zina, wasu saboda kazafi, wasu saboda kashe wasu. A irin wannan al'ummar akwai karo da gaskiya ya zama wata doka tana cewa "Duk wanda ya hadu da annabi ko ya gan shi yana mai imani da shi to adali ne"!. A yanzu annabi (s.a.w) zai yi umarni da yakar adali?! Me ya sa kuke hukunta hakan!.

SAHABBAI A KUR'ANI
Abin da ya zo a littafin Allah ba shi da bambancin da abin da yake cikin Tarihi da Sunna, Kur'ani ya yi nuni da al'ummar musulmi a zamanin annabin rahama kuma ya kasa ta gida-gida bisa darajoji. Dokar cewa duka adalai ne ya saba da Kur'ani kai tsaye. Allah yana ganin duk mutane tun annabi Adam (a.s) har zuwa mutum na karshe ba su da bambanci, darajarsu tana doruwa ne bisa tsoronsa kawai.
Akwai masu rigo a imani, da masu bai'a karkashin bishiya, da ma'abota budin Maka, da sauransu. Sai dai ya sifanta musulmin baki daya zuwa muminai masu karfin imani, da munafukai, da masu raunin imani. Sai ya kawo sifofi masu yawan gaske kan mutanen da suke masu raunin imani da kuma munafukai da yadda za a gane su zuwa masu ciwo a zuci, da masu jin fitina, da masu cakuda mummuna da kyakkyawa, da masu yin ridda, da masu karyar imani don bai ma shiga zuciyarsu ba, da masu hada kai da kafirai, da masu yin masallaci don raba kan al'ummar musulmin da shirin kashe annabi (s.a.w) a cikinsa.
Saboda haka al'ummar musulmi a lokacin annabi (s.a.w) ta kunshi mutane kala-kala, wannan kuwa ya saba wa dokar da aka kirkiro wacce wanda ya saba mata yake fuskantar zargin yana zagin sahabbai. Idan kuwa saba wa wannan dokar ya zama zagin sahabbai to lallai sai su tuhumi Kur'ani da cewa yana zagin sahabbai.

SAHABBAN ANNABAWA
Kur'ani ya kawo sahabban annabawan da suka gabata da yadda ya nuna cewa kusanci ko zamani ko zama wuri daya ba shi ne ma'aunin nasara da tsira ba, imani shi ne ma'auni a kowane zamani. Ya kawo mutane kamar matar annabi Nuhu (a.s) da dansa, Matar annabi Lut (a.s), sahabban Musa da Harun (a.s), sahabban Yusha' (a.s), matar Musa (a.s), sahabban Isa (a.s). Sannan manzon Allah (s.a.w) ya yi nuni da cewa shi ne ya fi kowane annabi (s.a.w) daga cikin wadannan shan wahalar mutanensa. Wannan yana nuna cewa adalin mutum ba zai ba wa annabi (s.a.w) wahala ba, lamarin da yake nuna cewa ba kowane mutum ba ne da ya yi zamani da annabi (s.a.w) yake adali.

HUKUNCIN ZAGIN SAHABI
Da wannan ne zamu fahimci cewa irin dokokin da suka sanya da sunan hukuncin wanda ya zagi sahabin annabi (s.a.w) [kora ce, tsarewa ce, bulala ce, da sauransu] bayan sun sauwara wata doka da sunan adalcin duk sahabbai da Allah da manzonsa ba su san da ita ba, duk ya zama shaci fadi da son rai don kawai ganin bayan mutane da suke riko da koyarwar Kur'ani da sunnar annabin rahama (s.a.w).
Masoya Ahlul-baiti (a.s) kuma mabiyansu shi'awansu ba su san da wani abu zagi ba hatta da zagin wanda suke bauta wa wanin Allah balle zagin sahabbai masu daraja da suka dauki nauyin musulunci a kafadunsu har ya kawo zuwa gare mu.
Ba abin da zai ba mu mamaki irin yadda masu sukan shi'a da zagin sahabbai suka ruwaito cewa ana zagin Abubakar a gaban annabi (s.a.w) sai ya rika dariya, amma da Abubakar ya rama sai ya nuna bacin rai. Me suke nufi da irin wadannan ruwayoyi da ire-irensu, shin suna nufin idan ana zagin sahabai ke nan a sunna dariya ake yi? Idan haka ne me suke nufi kuma da cewa wanda ya zagi sahabi fasiki ne ko kafiri?!.
Sai dai a daya bangaren ba zamu kore samuwar tashoshin kafofin sadarwar masu aiki ga kafircin yammacin duniya masu neman raba kan al'ummar musulmi, da suke batanci ga wasu daga musulmin da suka yi zamani da annabin rahama (s.a.w) don su jawo rikici da rarraba kai a cikin al'ummar musulmi, da babu mai iya rashin fahimtar haka a wannan zamani sai wanda zuciyarsa ta makance. Wannan makircin ya ba wa 'yan kafirta musulmi umayyawan wannan zamanin damar yin aikin ta'addanci kan masoya kuma mabiya alayen annabin rahama [shi'awa], da ba su da wani laifi sai imaninsu da Allah da manzonsa (s.a.w) da riko da Kur'ani da tafarkin alayen annabi (a.s).

NATIJAR WANNAN MAS’ALA
Duk lokacin da aka samu wata doka sabanin hankali ko Kur'ani mai daraja sai an samu natijoji masu tasiri a kowane lokon shari'a da zai iya haifar da sakamako maras kyau a dokokin da zasu haifar. A sakamakon wannan dokar zamu ga an samu wadannan mas'aloli a cikin al'ummar musulmi:
a) Nisantar ka'idar Kur'ani kan mas'alolin da suka shafi tarihin al'ummu da al'adunsu da siyasarsu da duk wani abu da ya shafe su, lamarin ya kai ga ana iya cire sunan sahabin da wata aya ta zarga a sanya sunan annabin rahama (s.a.w) a mahallinsa, kuma duk sa'adda aka samu sabani tsakanin annabi (s.a.w) da wani sahabi to sai Allah ya goyi bayan wancan sahabin ya soki annabinsa!.
b) Nisantar sunnar annabin tsira (a.s) a duk inda ta ci karo da sunnar sahabi, kuma sahabi yana iya rushe sunnar annabi (s.a.w) kuma a dauki tasa a watsar da ta annabin rahama a kwandon shara. A sakamakon haka ne duk sa'adda wani sahabi ya saba wa sunnar annabi (s.a.w) to sai a yi tawilin wannan abin da ya yi ko kuma a kirkiro ruwayar da zata taimaka wa abin da ya yi, ko a lankwasa ayar Kur'ani don ta yi daidai da abin da ya aiwatar.
c) Nisantar Ahlul-baiti (a.s) a matsayin wasiyyar da annabin rahama (s.a.w) ya yi wa al'ummarsa, sai ya zama duk wani abu da ya zo daga Ahlul-baiti (a.s) siyasa ta sanya nisantarsa, kamar dai ma laifi ne ka yi riko da mazhabin Ahlul-baiti (shi'anci) a lokacin da kowa yake da ikon ya riki duk abin da ya so wanda ya fito daga hannun wani sahabi hatta ma daga tabi'ai.
d) Nisantar hankali a lamarin da ya faru na tarihi a cikin al'ummar musulmi, ta yadda mai sabo da maras sabo, da adali da fasiki, da malami da jahili, da mai yada barna a bayan kasa da mai shiryar da mutane, da sahabin da ya sha wahala tare da annabi (s.a.w) da wanda ya kashe shi saboda imaninsa da abin da annabi (s.a.w) ya zo da shi, duk sai suka zama hukunci daya, babu wani hakkin nakadi da raddin abin da wani mai barna zai yi komai tsananinta da girmanta!.
e) Gyara duk wata barna da wani musulmi ya yi da da'awar cewar ai ya yi zamani da annabi, da tilasta samar mata da wata mafita ko tawili ta kowane hali ne, da kirkiro hadisai wani lokacin don ba ta kariya. An yi tawilin duk wani abu da ya faru na kuskure da barna da ma abin da tsikar jikin mai sauraro ke tashi saboda muninsa; An yi tawilin warware bai'ar da aka yi wa Ali (a.s) bayan wafatin annabi (s.a.w), da kwace gonar 'yar annabi (a.s), da hana ta gadonta, da kona hadisan annabi (s.a.w) bayan wafatinsa, da hana rubuta hadisansa ko bayar da su, da kashe muminai, da kwanciya da matansu bayan kashe su, da daruruwan abubuwa da suka faru a tarihin musulmi.
 
MUSULMI A YAU
Idan mun duba yadda musulmi suka samu kansu a yau sakamakon wannan dokar da aka dora musu zamu ga an samu jahiltar addini ya yawaita cikin al'ummar musulmi ta yadda musulmi ba ya gane sunnar annabi da wacce ba ta annabi ba, wannan kuwa sakamakon cewa sunnar sahabi a aikace tana shafe ta annabi, sannan sunna tana shafe Kur'ani, har sai da Imam Ali ya rasa halifanci saboda ya ki karbar sunnar sahabi sai ta annabi kawai!.
Sai sahabi ya kasance shi ne addini baki dayansa maimakon Ahlul-baiti (a.s) da Allah da manzonsa suka sanya su makomar al'umma bayan annabi (s.a.w)!. Lamarin bai tsaya kan fifita sunnar sahabi a kan ta annabi ba, ya zarce nan yakai ga sanya Annabi (s.a.w) kasan sahabi, misali annabin tsira yana da shedan da yake hana shi salla ya dame shi ba don ya ci sa'a ya musulunta ba amma akwai sahabin da idan ma ya bi hanya to fa shedan ba ya iya bin ta!.
Mas'alar ta kai ga rarraba kan al'ummar musulmi, da haifar da fitintinu a cikinsu, da riko da mazhaba ko ra'ayi a makance ba tare da wani hasken ilimi ba, lamarin ya kai ga yin ta'addanci da kafa hujja da aikin sahabi!. An rushe sunnar annabi mai yawan gaske da ijtihadodin da suka saba wa nassin shari'a da hujjar cewa sahabi bai yi ba ko ya saba hakan, tun daga mas'alar kiran salla, salla, shafa kafa, auren mutu'a, mas'alolin gado, mas'alolin saki, yin kabalu, sallar asham, jam'in salloli, da sauran rassa a addini. Idan muka waiwayi asasin addini kuwa zamu ga ya kunshi; tilasci a aiyukan bayi, kaddarawa, sanya jiki ga Allah, kamanta Allah da bayinsa, jahiltar sifofinsa. A annabci zamu ga cire wa annabawan Allah isma da kariya daga laifuka. Idan muka waiwayi jagoranci da imamanci da halifanci zamu ga an jefar da halifancin hashimawa, da rushe makomar al'umma zuwa ga alayen annabin rahama (a.s), da kiyaiya da su, da kyamatar wa al'umma su don su guji mazhabinsu, da makirci gare su da mabiyansu.
Wannan shi ne halin al'ummar musulmi a yau sakamako wannan doka da ire-irenta da suka assasa ba tare da wani madogara ta Kur'ani ko sunnar annabi (s.a.w) ba!.


Hafiz Muhammad Sa'id
hfazah@yahoo.com
www.haidarcenter.com
+234 803 215 6884 [Tedt, Telegram, Biber, Whatsapp, Line, Tango, Wechat] Only.
HAIDAR CENTER
Tuesday, June 21, 2016
comments Masu kallo
Suna:
Adireshin Email:
* ra'ayi: