bayyinaat

Published time: 08 ,April ,2018      15:39:45
Imam Sadik (a.s) karni daya da rabi ya wuce ya shude bayan bayyanar muslunci, karni guda ciki ya kasance ya shagaltu da futuhat din muslunci ta yadda ya yi shahada a shekara ta 148 da hijra, cikin wannan lokaci wasu al’umma biyu ko kuma muce uku daga musulmai suka kara bayyana suka fara ayyukansu daga tarjama hankali daga cikinsu akwai masu barazana ga al’ummar musulmi ta yadda cikinsu zindikai suka bayyana wadanda sune wadanda suka tafi kan wanzuwar zamani haka ma mulhidai masu inkarin samuwar Allah,
Lambar Labari: 99
Waiwayen Tarihin Musulunci

Hukumar umayyawa ta yi rusau mai fadin gaske cikin ginin zamantakewar al’ummar musulmi ta kasance tana rainon kungiyoyin bata da karkacewa daga kan hanyar gaskiya wanda suke harin kwakwalen musulmai da fahimtarsu suka zama silar haifar da bakuwar sakafa cikin musuluci, daga baya kuma sai hukumar abbasiyawa ta dare karagar mulki domin ita ma ta kammala wannan rusau da umayyawa suka fara, sau da yawa da wasu sabbin uslubai, babban abin da ke gaban hakan ma shi ne rushewar zamantakewa da karkatar tunani da na suluki mai girma, Imam Sadik (a.s) ya kasance yana da babbar rawar da ya taka cikin yakar wannan barna ta hanyar assasa makarantun ilimi da samar da alakokin zamantakewa domin sake karfa ginin muslunci da zamantakewar da ya karbo daga babansa da kakanninsa tsarkaka.

Imam Sadik (a.s) karni daya da rabi ya wuce ya shude bayan bayyanar muslunci, karni guda ciki ya kasance ya shagaltu da futuhat din muslunci ta yadda ya yi shahada a shekara ta 148 da hijra, cikin wannan lokaci wasu al’umma biyu ko kuma muce uku daga musulmai suka kara bayyana suka fara ayyukansu daga tarjama hankali daga cikinsu akwai masu barazana ga al’ummar musulmi ta yadda cikinsu zindikai suka bayyana wadanda sune wadanda suka tafi kan wanzuwar zamani  haka ma mulhidai masu inkarin samuwar Allah, kamar yadda wasu adadi daga masana fikihu suma suka bayyana kan wani sabon asasi misalin tafiya kan ra’ayi da kiyasi da wasunsu  da ayyukan (kalamiyun) masu tattaunawa kan tauhidi wsu lokutan sukanyi tarayya da juna wasu lokutan kuma su sassaba, cikin wannan lokaci da aka samu lafawar siyasa  wadda Imam Sadik ya rayuwa cikinsa wani `dan mikdari lokaci,Imam Sadik (a.s) ya samu yanayi dacacce da zai bayyana kawo sauyinsa na ilimin musluncin ingantacce  cikin assasa makarantu da hauzozin ilimi da yada hadisi da sunnar Manzon Allah (s.a.w) domin raya musluncin asali, daga ka’idar (adamul tarkil aula) wacce a’imma (a.s) suka lazimceta, Imam Sadik (a.s) ya zabi yin saura ta ilimi bai zabi hanyar fito na fito da mahukunta ba, sai ya kifu kan haka domin sauke sakonsa cikin sabunta musulunci ta inganta karkace-karkace da gyarasu da samar da wasu malamai masana shari’a da sha’anin zamaninta, wannan shi ne abin da tarihin Imam Sadik (a.s) ya yi dako  cikin yalwatar tanadar dalibansa wadanda ake kadddara adadinsu da mutum dubu hudu koma fiye da haka, cikinsu akwai manya-manya wadanda suke da kwarewa da gogewa cikin sha’anunnuka da daban-daban zuwa ga janibin dawwana litattafai da zantuttukan ilimi masu tarin yawa, haka ayyukansa cikin munazarorin ilimi daban-daban, yanayin ya kasance yana hukunta yin hakan, cikin dukkanin hakan Imam (a.s) bai kasa agwiwa ba cikin aikinsa na kawo gyara.
A gaban wadannan kungiyoyi daban-daban kamar misalin kalamiyun da fakihai da kurra’u (masana kira’a) da sufaye da kawarijawa da murji’a da `yan jabariya da mu’utazila da kadariyyin masu kore kaddara kai hatta zindikai da sauransu, Imam Sadik (a.s) ya kasance ya yi buga da dukkaninsu saboda dalili guda biyu:
1-kiyaye shari’a da kareta daga karkata.
kare zamantakewa da jama’arta ta gari daga hadarurruka da kalubale.
Imam Sadik (a.s) ya kasance yana yin wadannan muhimman ayyuka da muka zayyana da kankin kansa ta hanyar munazarori da bada amsoshin tambayoyi ko kuma ta hanyar almajiransa ta yadda mukai ishara kan haka acikin bahasinmu, daga cikin abin da ya taImamkawa Imam cikin tabbatuwar hakan shi ne kasantuwar ya rayu har tsawon shekaru saba’in cikin inuwar yanayin siyasar zamaninsa.
Imam (a.s) karkashin saurarsa ta ilimi da kawo gyara wadda ya yi gogegeniya da shi cikin dukkanin matakai da hakan ya bashi damar kiyaye jama’a saliha ta gari daga hadarurruka da kalubale, ya kuma samu damar rainon kwakwale da zasu iya ta’ammuli da wadannan kalubale, makarantar Imam Sadik (a.s) ta fifita da nauyaya da ilimi da `yantuwa daga jumudin kwakwale da girmama hankali  da dandake nassoshi, wannan dalilai ne da suka taImamkawa wannan makaranta kan kiyaye mutane salihai wadda ita wannan makaranta ita ce iri na samar da mutane nagargaru.
Imam Sadik (a.s) ya yi amfani da uslubi biyu da sukai zamani daya da juna da yake ruguje waccan bata da karkata da karkade tunaninta da wawaitar da akidunta, a daya bangaren kuma yana amfani da uslubin gini ta hanyar yada mafahim din akida da hukunce-hukuncen shari’a da sanya masallacin annabi mahallin karatu cikin dukkanin fannoni da ilimummuka, a matakain gina mutane nagargaru Imam Sadik (a.s) ya kasance yana umartar mabiyansa da kauracewa sarki ta yadda yake ce musu: 
  
(إياكم أن يخاصم بعضكم بعضاً الى أهل الجور.

Kada ku sake ba’arinku ya kai ba’ari kara gaban sarakunan zalunci.

Imam (a.s) ya kasance yana karfafa mabiyansa da yin takiyya da kiyaye sirri domin kire aminci da lafiyarsu ya zo cikin wasiyyarsa ga Muhammad ibn Nu’umanu ah’wal yana ce masa: 

يا ابن النعمان إن المذيع ليس كقاتلنا بسيفه بل هو أعظم وزراً، بل هو أعظم وزراً، بل هو أعظم وزراً... فهو الله لقد قرب هذا الأمر ثلاث مرات فأذعتموه، فأخّره الله، والله ما لكم سرّ إلا وعدوكم أعلم به منكم)

Ya nu’umanu lallai mai yada sirri ba kamar mai kashe mu bane bari dai shi ya fi girmam laifi daga mai kashe mu … lallai Allah ya kusanto da wannan al’amari karo uku sai kuka yada shi sai Allah ya jinkirta shi, wallahi baku da wani sirri face makiyinku ya fiku saninsa.
Imam (a.s) bai kokwanto ba tare da zabinsa na bin uslubin isar da sako ba kai tsaye ba nutsatstse domin gina al’umma ta gari tare da duban yadda yanayi ya hukunta- cikin goyon bayansa ga motsi mai ikhlasi, Imam (a.s) ya kasance yana tausayawa baffansa shahid zaidu ibn ali lokacin da yake cewa:

 (رحم الله عمي زيداً انه دعا الى الرضا من آل محمد ولو ظفر لوفى لله في ذلك)
Allah ya jikan baffana zaidu tabbas shi ya yi kira zuwa ga yarda  na daga iyalan muhammadu lallai d ya samu nasara da cika alkawalin da ya yi.
Imam ya kasance yana cewa:
 (ولوددت أن الخارجي من آل محمد خرج وعليّ نفقة عياله)
Nayi burin ace wani mai fita daga iyalan Muhammad ya fito ni zan dauke masa nauyin ciyar da iyalinsa.
Imam (a.s) ya sha kuka ya sha radadi lokacin da ya ji labari anci iyalan Hassan (a.s) da yaki wanda Imam (a.s) adadai wannan lokaci ya yi watsi da motsi mara hadafi mara ikhlasi bai bashi goyon baya ba, lokacin da `dan aiken abu salma khalal ya zo wajensa da wasika yana shelanta barrantarsa ga banul abbas yana kuma gayyatar Imam (a.s) sai  ya bashi amsa da cewa: ba ni ne  abu salma ba, abu salma shi’ar wani na ne, sannan ya dauki wasikar ya sanya kan fitilar wuta har sai da ta kone sannan ya cewa `dan aiken ka gayawa mai gidanka abin da ka gani da idonka.
Karkashin dukkanin wannan da banbantar masu tsayuwa kan wadancan da’awowi na siyasa zamu ga fayya cewar Imam (a.s) ta bayyanar mana a sarari


 ga wadanacan yanayi da shubuhohi da kuma hikImamr zabinsa da uslubin da yabi.
  
Usulubin Imam Sadik (a.s) cikin gini:

Zamanin Imam Sadik (a.s) ya fifita da samun lafawar rigimgimun siyasa karkashin tsufan hukumar umayyawa da rarrauwar sabuwar hukumar abbasiyawa da shagaltuwar sashensu ga sashe, sai Imam (a.s) ya sabi hanya ya maida hankali kan tafiyarsa ya himmatu kan abin da ya sanya a gaba daga sadaukarwa cikin assasa jama’ar ilimi lafiyayya a cikin mabanbanta ilimummuka da fannoni, ilimummukan Imam sun kasance daya daga cikin usluban gina al’umma.

Uslubi na farko: batun ilimi: muna iya bayyana shi da tsinkayarshi karkashin:
1- litattafan ilimi.
2- yawan almajirai dalibai.
3- munazarori.
4- bangaren kawo gyara da yake cikin wannan bayyanannen al’amari.

Zai iya yiwuwa mu dauki daidaikun wannan bayyanannen al’amari muyi ishara ga mafi bayyanar abin da ke fayya ce su.
Me ya kawo rashin dawwana ilimi da rubuta shi:
Zai iya yiwuwa mu kalli batun ilimi cikin makarantar Imam Sadik (a.s) da mafi bayyanar matsayinta  da kufenta karkashin sanin hanya da minhajar hana rubuta hadisin Manzon Allah (s.a.w) wanda hakan ba zai taba yiwuwa a wanke shi ba aba shi dalili, wannan wani tsari ne da ya haramtawa al’umma taskokin sunna madaukakiya wanda hakan ta’addanci kan wancan amana ta ilimi da shar’anta ga Manzon Allah (s.a.w) samsam Manzon Allah (s.a.w) bai ta hana rubuta hadisi ba bari ma dai muna tarin litattafai da wasiku da suka zo da aka rubuta su daga gareshi da kwadaitarwarsa kan rubutu. Kadai dai batun hana rubuta hadisi ya faru ne bayan wafatinsa bari dai shi Manzon Allah (s.a.w) ya yi bankwana da al’ummarsa daidai lokacin da aka hana shi rubuta zancensa madaukaki ta hanyar kin kawo masa tawada da takardar rubutu har lamarin ya kai ga hana rubutu ya juya ya zama a nakalce da riwayance aka maye gurbinsa da bude kofar karya ga Manzon Allah (s.a.w) musammam ma siyasar banu umayya wadanda suka jirkita hadisin Manzon rahama ta hanyar cusa karya da kagar sabbin hadisai, hakika tsarin hana rubutu ya samu assasuwa tun zamani halifofi uku  kamar yadda shamsud dini zahabi ya ambci hakan cikin littafinsa mai suna tazkiratul huffaz

وروي عن أبي هريرة انه قال: (ما كنا نستطيع ان نقول: قال رسول الله| حتى قبض عمر)

An rawaito daga abu huraira ya ce: bamu kasance muna samun damar fadin: Manzon Allah (s.a.w) ya ce ba har sai da Allah ya karbi ran umar.

Sannan gwamnatin umayyawa ta zo ta dare kan karagar mulki ta cigaba kan wannan tsari na hana rubuta hadisi, hakika mu’awiya ibn abu sufyanu ya hana rubuta hadisi cikin fadinsa:

 (لا تحدثوا عن رسول الله).
Ka da ku sake ku zantar da hadisin Manzon Allah (s.a.w).
Haka ma an rawaito cewa mu’awiya yana ya ce: ni na barrantar da zimma daga wanda ya rawaito hadisi gameda falalar abu turab da iyalan gidansa, umayyawa sun cigaba kan wannan tsari na hana rubuta hadisi.
Sai dai cewa marja’iyyar ahlul-baiti (a.s) sun tashi tsaye wajen rubutu sannan an samu rubuce –rubuce da litattafaim masu tarin yawa daga Imam Sadik (a.s) misalin littafi kan ulumul kur’an na Imam ali (a.s) da littafin sunnoni da kaziyoyi da hukunce-hukunce wanda Imam ya sallama shi ga almajirinsa malik ashtar da ta’alikinsa cikin ilimin nahawu da sahifa da littafin jafaru da wasunsu. Haka a’imma suka himmatu da rubuta sunna madaukakiya.

Menene abin da Imam Sadik (a.s) ya aikata:

Hakika Imam Sadik (a.s) ya kwadaitar kan rubutu ta yadda ya ce:
 (القلب يتكل على الكتاب)
Ita zuciya ta dogara ne da rubutu.
A wani wajen kuma ya ce:
 (احتفظوا بكتبكم فأنكم سوف تحتاجون اليها)
Ku kiyaye litattafanku da sannu zaku bukace su.

Hakika an rawaito wallafe-wallafe masu tarin yawa daga gareshi daga cikinsu akwai littafin tauhidi da ya shiftawa mufaddal ibn umar da risalatul ahwaziya da jafariyat da kitabul hajji da wasunsu daga wallafe-wallafe masu tarin yawa.
Hakika almajiransa sun tafi kan tsarinsa sai suka rubuta abubuwa masu tarin yawa cikin ilimummukan kur’ani da hadisi da fikihu da lugga da tarihi da jafariyya da ilimin lissafi da kimiyya da sauransu.

Motsawar ilimi ga Imam Sadik (a.s):

Ta yadda ya kasance yana karfafa bijiro da riwaya kan kur’ani idan kur’an ya dace da riwayar sai a karbeta idan kuma ta sabawa kur’ani sai ai wasti da ita bango a kyaleta. Da wannan Imam (a.s) ya samu damar sanya ka’ida domin hana cigaba da yada karairayi hakika ya `yantar da hadisai ya tace daga abin da aka lakaya musu daga tatsuniyoyin isra’iliyat da kagaggun hadisai da ayyukan siyasa da aka kirkira bayan Manzon Allah (s.a.w), kamalar rubutu tana bayyana cikin makarantar Ahlul-baiti (a.s) karkashin wancan hanawa ta ta’addanci da wasu sukai kan ilimi da hankali da sunna madaukakiya.

Game da almajiran Imam Sadik (a.s):

su wanene wadannan fitattun wadanda suka kwankawada daga iliminsa (a.s):
*abanu ibn taglib ta yadda ya umarce shi da yiwa mutane fatawa cikin masallaci.
*zuraratu ibn a’ayuni cikin fikihu.
* hisham ibn hakam muminil `dak da hisham ibnn salim cikin ilimin kalam (tauhidi)
*himranu ibn a’ayuni cikin ulumul kur’an.
*jabir ibn hayyanu kufi cikin ilimin kimiyya.
Da wasunsu masu tarin yawa, wannan yana nuni kan irin himmatuwar Imam Sadik (a.s) kan ilimi da yada wannan al’amari domin nau’antar da shi dukkanin wadannan amlajirai nasa da muka kawo sun kwankwada daga iliminsa kuma suna komawa gareshi.
Manya-manyan malaman sunna da suka debi ilimi daga Imam Sadik (a.s)
 
1-Abu hanifa nu’umanu ibn sabit wanda ya yi wafati a shekara ta 150 hijri, wanda shi ne yake cewa (ba da ban shekaru biyu da nu’umanu ya halaka) wacce cikin wannan shekaru ne ya sahibanci Imam Sadik (a.s) domin diban ilimi.

2- malik ibn anas madani wanda ya yi wafati hijra na shekara 179 shImam ya karbi ilimi daga Imam Sadik (a.s) nawawi ya kawo shi cikin littafin tahzib, shabalanji ya kawo cikin littafin nurul absar, shafi’i cikin littafin madalib da wasunsu.

3- sufyanu sauri wanda ya yi wafati hijra na da shekara 161 ya rawaito daga Imam Sadik (a.s) ya kuma yi masa wasiyya da wasu al’amurra ya yi munazara da shi cikin zuhudu.

4- sufyanu ibn uyaina wanda ya yi wafati hijra tanada shekara 198.

5- yahaya ibn said Ansari ya yi wafati hijra tanada shekara 143.

6- ibn jarihi  abdul-malik makki ya yi wafati hijra tanada shekara 149 

7- kittanu abu said albasari ya yi wafati hijra tanada shekara 198.

8- muhammadu ibn is'hak mai littafin magazi ya yi wafati hijra tanada shekara 151.

9- shu’ubatu ibn hajjaju azdi.

10- ayyubul sujustani ya yi wafati hijra tanada shekara 131 da wasunsu masu tarin yawa 

hadin kan muslunci: 

wannan al’amari na yaye hadin kai fuskanin wurin Imam Sadik (a.s) cikin gina wani tsani da matattakala ta ilimi ga al’umma wanda wadannan manyan malamai da muka Ambato duka sun kwankwanda daga gareshi wadanda suna shakkala mafi bayannar da gabban kungiyoyin muslunci. Wannan wani abin alfahari ne ga Imam Sadik (a.s) da tarihi ke ambata tare da girmamawa bai buya ga kowa ba cewa shafi’i wanda ya yi wafati hijra na da shekara 241 ya kasance daga almajiran Imam Sadik (a.s).

Munazarori: 
Ita ma daya daga cikin abubuwa ne masu tarin yawa a wancan zamani da ta bayyanar da sabbin tunanunnuka masu ban mamaki ta kasance tana barazana ga kalubale lafiyar mutane da tsiransu, sai Imam (a.s) ya mike ya tashi tsaye wajen munazara da tattaunawa ta ilimi tare da mulhidai masu inkarin samuwar Allah da zindikai, kamar yadda munazara ta kasance tare da shi da nu’umanu ibn sabit abu hanifa kan batun Imamanci da kiyasi da saurasu haka tare da abu yusuf  haka ma tare da dabibul hindi haka ma tare da malaman mu’utazilawa da kuma tare da harun Rashid da mahadi abbasi da fadalu ibn rabi’i, haka ya yi munazarori mai tarin yawa tare da malaman yahudawa da nasara wacce litattafan riwaya suka dawwana su. 

Usulul arba’mi’a da kutubul arba’a:

Almajiran Imam Sadik da Imam alkazim (a.s) sun dawwana uslul arba'a mi'a wanda hadisai ne da aka dawwana su aka rubuta su, cikinsu akwai abin da shi ma'abocin littafinya ji da kunnuwansa kai tsaye daga Imami ma'asumi (a.s) da kuma wadanda yaji daga wanda ya joyo hadisan kai tsaye daga Imami.
Amma kutubul arba'a wadanada sune suka tattaro riawayoyin da suke daga usulul arba'a mi'a to sune kamar haka:

1-usulul kafi na shaik muhammadu ibn yakub kulaini wanda ya yi wafati 329 hijri.

2- manla yahaduruhul fakihu na shaik saduk wafati 381 hijri.

3- tahzibul ahkam na shaik dusi wafati 460 hijri.

4- al'istibsar na shaik dusi wafati 460 hijri. 

5- tu nasa mai albarka ba.
comments Masu kallo
Suna:
Adireshin Email:
* ra'ayi: