Al umma
Alakar Addini
Kawo gyara wani juzu'I ne da bai yiwuwa a cireshi daga gundarin harkar ilimi da imam sadik (as) ya mike kanta.
na yi mamakin wanda ya ke neman bataccen abinshi alhali ya batar da kanshi kuma ba ya nemanshi .
Kadai masu tsoran daga bayinsa sune malamai. Abinda ake nufi da malamai a nan su ne wadanda aikinsu ya gasgatar da zancensu, da misali wadannan malaman ne ake cewa idan malami ya gyaru baki dayan duniya zata kasance cikin albarka.
1-Kadaitaka A Cikin Zati. 2-Kadaitaka A Cikin Ayyuka. 3-Kadaitaka A Cikin Halittawa. 4-Kadaitaka A Cikin Ibada. 5-Kadaitaka A Cikin Siffofi. 6-Siffofi Tabbatattu (Subutiyya). 7-Siffofi Korarru (Salbiyya). 8-Sakamakon Bincike.
Muhimmancin bahasi kan akidar musulunci yana kafuwa ne a kan asasin da samuwar musulumi take doruwa a kansa ne, sakamakon haka ne ya sanya zamu ga kur’ani ya sanya akida ita ce kashin bayan kaiwa zuwa ga Allah (s.w.t).
Madaukaki ya ce: “Zuwa gare shi ne kalma mai tsarki take hawa kuma yana daukaka aiki na gari”[2].