bayyinaat

Taska
Littafi
Alakar Iyaye da 'Ya'yansu
Wannan littafin yana bincike ne kan hakkin yara a kan iyayensu da akasin hakan. Ya kasance wata matashiya ce kan wadannan bincike-bincike domin iyaye su san makamar renon yara da tarbiyyarsu. A daya bangaren kuma su ma yara su san hakkin iyayensu da yadda zasu girmama su kuma su kiyaye biyayya gare su. A cikin littafin akwai wasiyyar nan mai muhimmanci ta Luqman (a.s) ga dansa.
Rayuwar Ma'aurata
Littafi ne mai muhimmanci matukar gaske wurin zana mana yadda ya kamata rayuwarmu ta aure ta kasance. Ya fara da bincike kan halittar namiji da mace, sai kuma bahasin rayuwar mata a al'ummu, da kuma bincike kan auren mace sama da daya a al'ummu da addinai, sannan ya gangaro zuwa rayuwar samartaka da zabar abokan rayuwar aure. Sai shafin rayuwarmu mai muhimmanci da ya hada rayuwar zaman aure, siffofin ma'aurata, hukunce-hukunce, da sauransu. Daga karshe ya rufe da bahasosin sabanin ma'aurata da rabuwarsu.
Hijabi Lullubin Musulunci
Hijabi sirri ne daga cikin sirrukan mata da ya zama kamala mai darjanta mace da ba ta kimarta a cikin al'umma. Hijabi yana nuna darajar mace da kimarta a cikin al'umma kuma a sakamakon haka ne zamu ga mata masu daraja tun daga Maryam, Asia, da Hadija, da Fatima (a.s) duk sun zama wani alami na lullubi a cikin al'ummun da suka biyo bayansu. Darajar mace ce ta sanya Allah madaukaki ya girmama ta da lullubi domin a fahimci kimarata a cikin al'ummu ita ma ta fahimci darajarta da kimarta.
Rayuwar Addini
Wannan littafin ya kunshi muhimmiyar koyarwar addini bisa koyarwar Ahlul-baiti masu daraja (a.s). A cikin littafin akwai ruwayoyi masu muhimmanci da suke koyar da darussa a fagage daban-daban da suka shafi fagen; al'umma, siyasa, tarihi, aqida, fiqihu, al'adu, ilmi, tarbiyya, da sauran fagage masu muhimmancin gaske a rayuwar mutum da zata kai shi tsiran duniya da na lahira.
Mai Sako, Dan Sako, da Sako
Littafi ne da shahid Sadar ya wallafa shi wanda yake da muhimmanci matukar gaske wurin tabbatar da samuwar Allah da manzancin annabin rahama da kuma ranar lahira. Ya bi hanyar nan ta Istiqra'i da ya shahara da ita a Mantiq dinsa domin ta zama hujja kan yammacin duniya da gabascinta, sakamakon cewa hanya ce da suka hadu kanta a matsayin hujjar bincike ta ilimi.
Alkar Iyaye da 'Ya'yansu
Wannan littafin yana bincike ne kan hakkin yara a kan iyayensu da akasin hakan. Ya kasance wata matashiya ce kan wadannan bincike-bincike domin iyaye su san makamar renon yara da tarbiyyarsu. A daya bangaren kuma su ma yara su san hakkin iyayensu da yadda zasu girmama su kuma su kiyaye biyayya gare su. A cikin littafin akwai wasiyyar nan mai muhimmanci ta Luqman (a.s) ga dansa.
2