bayyinaat

Shari'a
Halaye
Kyawawan Halaye
Lalle a wannan rayuwa kowane mutum yana nema wa kansa alheri ne da kwanciyar hankali. Kuma yana aiki tukuru dare da rana a fagen rayuwa domin ya sami wannan kwanciyar hankali. Domin da'iman yana ci gaba ne da kokarinsa a wannan fage na gwagwarmaya wanda ya yi kama kwarai da fagen yaki. Yana kutawa cikin wannan fage har ta kai shi ga sadaukar da ransa. Duk wannan don tsammanin ko tsuntsun alheri zai bude fukafukansa a kansa, har ya samu ya karasa 'yar gajeruwar rayuwarsa a karkashin inuwarsa, nesa da kunci da damuwa.
4