bayyinaat

Sīrāh
Imamai Sha Biyu
Siffofin Jagora (a.s)
Ya zama dole ne ga wanda jagorancin al’umma ya san addini a dukkan kusurwowinsa, kuma ya zama masani da dokoki da cikakkiyar masaniyar tafsirin ayoyin Kur'ani da kewayewa cikakkiya ga sanin sunnar Annabi, da bayanin addini, da amsa tambayoyn mutane a kowani fage, da kuma kyakkyawan jagoranci.
Bayan yin bayanin wadannan nazarorin, ya dace mu bayar da amsar wannan tambayar mai cewa; tun da akwai Kur'ani da sunnar Annabi (s.a.w) wane bukata kuma ake da ita ga Imami kamar yadda Shi’a suke imani da hakan?
Halayen Imam Hasan (S)
Imam Hasan (a.s) ya amsa wa sarkin mas'alolin da ya kawo zuwa ga babansa Imam Ali (a.s) domin a amsa masa su, sai Imam Ali (a.s) ya nemi dan sakon ya zabi wani daga 'ya'yansa domin ya amsa masa, sai ya zabi Imam Hasan (a.s).
Halayen Imam Ali (a.s)
Imam Ali (a.s) ya yaki kuraishawa suna kafirai, kuma ya yake su suna munafukai, kamar yadda ma'aikin Allah (s.a.w) ya yi masa alkawarin hakan. Game da tafiyar da dukiya kuwa ya yi wa musulmi jagoranci ne irin na lokacin manzon Allah (s.a.w), ya kasance yana cewa: "Da dukiyar nan tawa ce da na daidaita tsakaninsu, yaya kuwa, alhalin wannan dukiya ta Allah ce, kuma bayar da dukiya ba bisa hakkinsa ba barna ne, kuma yana daukaka mai yin haka a duniya, kuma ya kaskantar da shi a lahira, ya girmama shi gun mutane, ya kaskantar da shi gun Allah. Don haka ne ya yi kokarin samar da al'ummar da masu hannu da shuni ba su mamaye arzikin kasa ba, kuma ba a samu danniyar gurguzu ba.