bayyinaat

Sīrāh
Imamai Sha Biyu
Daya daga cikin lamarin mai mihimmancin gaske da ya zama wajibi al’ummar musulmai su waiwaya shi ne lamarin halifanci bayan Manzo (s.a.w)
Tabbas batun haxin kan al’ummar musulmi wajen tun karar maqiya abu ne mai kyau matuqa, amma hakan kuma ba yana nufin a jefar da Aqidar asali ta addinin ba, munsamman tunda mun yarda cewa ta hanyar ladabi da magana mai kyau zamu iya tabbatar da alaqa mai kyau tsanin mu za kuma mu iya tattauna savanin da ke sakanin mu, amma bata hanyar watsar da aqidun mu ba
Bayan duk wadannan ni’imomi masu girma da ya yi mana bai nemi sakaiya a garemu ba face kawai ya umuurcemu da mu nuna soyaiyarmu ga wadannan tsarkakkun bayi nasa ta hanyar yin koyi da zantuka da ayukansu, sannan kuma da raya sha’a’ir xin su (ko kace alaminin) ya kuma tanaji sakamako mai girma ga wanda ya aikata hakan
Imam Sadik (a.s) karni daya da rabi ya wuce ya shude bayan bayyanar muslunci, karni guda ciki ya kasance ya shagaltu da futuhat din muslunci ta yadda ya yi shahada a shekara ta 148 da hijra, cikin wannan lokaci wasu al’umma biyu ko kuma muce uku daga musulmai suka kara bayyana suka fara ayyukansu daga tarjama hankali daga cikinsu akwai masu barazana ga al’ummar musulmi ta yadda cikinsu zindikai suka bayyana wadanda sune wadanda suka tafi kan wanzuwar zamani haka ma mulhidai masu inkarin samuwar Allah,
Bayani kan Ashura
Dukkanin Manyan Malamai magabata ba bu wanda ya saba akan cewar an kashe Imam Husaini dan Aliyyu dan Abu Dalib (dan Fadima ‘yar Manzo Allah) da sauran Jikokin Annabi da Sahabban Annabin da na Husainin a ranar goma ga watan Muharram. Watan da Hausawa suke kira da watan CIKA-CIKI, kuma suka dauki ranar goma ga watan ranar cika-ciki. Har sukan ce duk wanda bai cika cikin sa ba Ubangiji zai cika masa da wuta Ranar Al-Kiyama.
Imam Mahadi A Wata Mahanga: Jagoran Shi’a na karshe kuma halifan Manzon Allah (s.a.w) na goma sha biyu, ya zo Duniya ne a ranar juma’a a watan sha’aban shekarar hijira kamariyya 255, wato miladiyya 868 a garin Samra’u (ko samarra) daya daga garuruwan Iraki.