bayyinaat

Shari'a
Mas'aloli
aikin hajji ya samu kulawa da himmatuwar musulmi da manya-manya malaman su tare da dukkanin sabanin mazhabobin su tun ranar farko da aka wajabta shi duk da sassabawar makarantun su na tunani da aqida da fiqihu
Xaya daga cikin mas’alolin da ake tuhumar shi’a da ita, ita ce batun Raja’a, wato dawuwa bayan mutuwa wanda da yawa daga cikin al’ummar musulmi basu yarda da ita ba, sannan kuma batu ne da ya daxe yana jawu cece kuce tsakanin al’ummar musulmi wasu ma suna ganin ‘yan shi’a ne kaxai suka yadda da wanann batu na raja’a,
Dukkanin wanda baya yin sallah hakika ya kafircewa ni’imomin Allah matsarkaki sannan dukkanin wand aya kafirce lallai azabar Allah tanada radadi cikin gidan duniya da lahira , idan kuma kuka gode sannan ita sallah tana daga nuna godiya kan ni’imomin Allah lallai Allah zai kara ni’imar
Kimar Mutum
Hakika mafi girman da kuma daukakan abin da mutum zai iya mallaka a rayuwarsa shi ne hali da kuma mutumcin kansa, hakan kuwa wata amana ce da take a kan wuyansa wacce Allah Madaukakin Sarki Ya daukaka shi da ita. Sannan kuma Ya haramta masa ha'intar kansa ko kuma kaskantar da ita da kuma ha'intar abin da Ya ba shi na kwarewa. Imam Sadik (a.s.) ya yi bayanin wannan al'amari mai muhimmanci cikin fadinsa ce wa: "Allah Madaukakin Sarki Ya bar (halalta) wa mumini dukkan kome in ban da wulakantar da kansa.
4