Wahabiyanci da Salafanci

Wahabiyawa da salafawa Magana kan wadannan mutane na da matukar muhimmanci a yau, domin kuwa jama'a ne da ke gudanar da aikace – aikace iri – iri da su ka ja hankalin duniya musamman a kafafen yada labarai, wahabiyawa da salafawa suna da sunaye daban – daban a duniya, Magana kan sun a da muhimmanci sabida yawan hujumi da su ke kan sauran 6angarorin musulman da suka sa6a musu, musamman shia da darikun sufaye tare da kafirta su.
Tattaunawa da Kiristoci

Tattaunawa da Kiristoci

Ku kuna cewa Dadadde Madaukaki (s.w.t) ya hade da Masihi Dansa (a.s). Me kuka nufi da wannan magana?. Shin kuna nufin Dadadde ya zama Fararre saboda wannan Fararren da ya hade da shi wanda shi ne Isa (a.s) ko kuna nufin Fararren da yake shi ne Isa (a.s) ya koma Maras farko kamar samuwar Dadadde wanda yake shi ne Allah?.
Hujja kan Tauhidi

Hujja kan Tauhidi

Na yi imani da Allah daya ba shi da abokin tarayya, na kuma kafirce wa duk wani abin bauta ba shi ba. Sannan ya ce: Allah (s.w.t) ya aiko ni zuwa ga mutane gaba daya Mai albishir da gargadi ga mutane, sannan zai mayar da kaidin duk mai kaidi kansa.
Kadaitaka A Cikin Zati

Kadaitaka A Cikin Zati

Kasancewarsa ba shi bangarori da yanke-yanke da suka hada shi, wato sai ya zama tilo a cikin samuwarsa, wannan shi ne ake cewa da shi “Ahad”. Kore masa bangarori yana iya kasancewa ta hanyoyi hudu;
Dalilin Kididdiga

Dalilin Kididdiga

Muna ganin ni’imomin halitta da suka babaye mu, ni’imar rana, da ni’imar dare da ba mu san iyakacin su ba, ni’imar iska, da ruwa, da lafiya, da tunani, da zafi, da sanyi, da shiriya, ta hankali da ta wahayi, da sauran ni’imomi da ba zasu kirgu ba.
1 2 3 4 5 6 7 8