bayyinaat

Al umma
Iyali
Hukuncin Kaiyade Iyali
Na daya; Tsara Iyali wato daina haihuwa zuwa wani dan lokaci. Na biyu; Tsayar da haihuwa lokaci mai dan tsawo ta yadda za a tsayar da haihuwa a daina samar da dan adam a Duniya wani lokaci. Amma idan ya kasance da ma’anar tsayar da samar da dan adam ta yadda halittar dan adam zata kare ne wannan tabbas haramun ne a shari’a, amma da ma’anar da aka ambata ko kuma daidaikun mutane su tsayar da haihuwa da kansu ta yadda zasu daina haihuwa wannan babu dalili a kan haramcinsa, a bisa ka’ida wannan halal ne.
Tsarin Iyali Ko Kaiyade Iyali
Rashin lafiyar da ake dauka wanda kan iya samun jariri, da kuma mutane da suke dauke da nauyi mai girma a kansu ba su da mai taimaka musu wajan warware matsalarsu kuma kawo ‘ya’ya duniya zai kara matsalar ne kawai, wannan tsarin ya shafi mutum daya ne da iyalinsa a kankansa kuma ba a kansa ba ne duniya take cece-kuce.
Alak'ar Iyaye Da ‘Ya’yansu
Kuma ka sassauta musu fikafikin rusunawa na rahama, kuma ka ce Ubangiji ka tausaya musu kamar yadda suka rene ni ina karami. Isra': 24. Iyali su nemafi muhimmancin abin da yake iya sanya mutum daukaka ko kaskanta, kuma alakar uba da uwa da 'ya'yansu, ko ta 'ya'ya da su iyaye, ita ce take samar da nauyi da ya hau kan kowanne daga cikinsu.
Mutum halitta ne mai bukatar rayuwa a al'umma da ta iyali, rayuwar iyali kuwa ita ce mafi karancin haduwar zaman tare amma a lokaci guda kuma mafi zama asasin gina al'umma, wannan asasin an gina shi ne da namij da mace. Sanin nauyin da ya hau kan namiji da mace, da sanin yanayi da aiyuka da alakar yadda za a zauna da juna tsakanin namiji da mace shi ne abin da yake iya karfafa dankon soyaiya mai karfi da alaka tsakanin iyali.