bayyinaat

Al umma
Iyali
Duk wani dan’adam zai iya yin aiki na gari ya kuma bawa wasu lada wadannan ayuukan wanda daga ciki akwai mahaifansa wadanda su ma zai iya ba su ladan wannan aikin kuma kari kan ladan da za’a ba su shi ma za’a ba shi makamancin wannan ladan ko ma a ba shi sama da haka.
A muslunci, kalmar aure an fi alaqanta ta da kalmar 'Nikah' wato saduwa tsakanin mace da namiji, amma a shari’a Kalmar aure tana nufin yarjejeniya (ta saduwa) tsakanin namiji da mace wanda hakan ke halatta saduwa tsakaninsu a wajen Allah (S.W.T) da kuma al’umma gaba xaya.
Wannan ayar kawai ta isa ta nuna mana cewa waccan maganar ta cewa Allah na nan shi zai yi komai ba tare da shi bawa ya dauki wani mataki ba babu wani asasi da take da shi!. A wannan bangaren zamu kawo muku bayanai kan ma'anar yin aure a hayaiyafa bisa ma'anar da ta dace da shari'a da hankali.
Arzikin Kasa Da Mutane
Haka nan mu sani abin da muke gani na lalacewa, talauci, musibu, daidaicewa, fitintinu, rashin albarkar rayuwa, rashin zaman lafiya, da sauran abubuwan da suka addabi wannan duniyar bai takaita da gazawar dan adam kan matakan da yake dauka ba kawai, lamarin ya hada da rashin kyawawan halaye da keta hurumin Allah (s.w.t) da yake wakana a duk fadin wannan duniyar. Da al’umma ta yi imani ta gyara halayenta da ta samu ludufi da tausayawar Allah mai girma, don haka akwai tasirin rashin tsarkin badini a rayuwar al’ummu wurin samun dagulewar al’ummarsu da lissafinsu.
Tasirin Mahangar Kaddara
Wannan koyarwar mai hasken littafin Allah tana nuna mana cewa kowane mutum yana daukar nauyin alhalin aikinsa. Da wannan ne zamu ga Imam Ali (a.s) yana ba wa mai tambaya amsa cewa da mutum ya zama abin tilastawa ne ba shi da wani zabi a aiyukansa da shari'a, sakon Allah, lada, zunubi, hisabi, duk sun zama bataccen lamari!.
Kaiyade Iyali A Wasu Ruwayoyi
An yi amfani da wasu ruwayoyi domin nuni da cewa; dole ne mu kawo mutane masu yawan gaske a wannan duniya ko da kuwa ba mu dauki wani mataki kan hakan ba lamarin da suke ganin yana nuni da rashin halaccin kaiyade iyali. An yawaita amfani da hadisan da idan muka duba babu ko daya daga cikinsu da yake hana kaiyade iyali da tsara su ko da a matsayin karahiya balle kuma ya kai matakin haram, maimakon haka ma sai dai akwai hadisai da muke da su wadanda kai tsaye suke halatta kaiyade iyali da tsara su.