bayyinaat

Duniyar Musulmi
Mas'alolin Yau
Ita wannan kalmar "shi'a" tana da ma'anar nabiya da mataimaka kamar yadda ya zo a littafin kalmomi "kamus" na kusan dukkan "kamus' din larabci, Fairuz abady a cikin kamus ya ce kalmar "shi'a" ... "shi'aturrajul" na nufin mabiyansa ko mataimakan sa, haka nan ma'anar su daya da firka, tana doruwa kan mutum daya, biyu
Sannan kuma Alusi ya ambata a cikin tafsirinsa bayani mai tsawo domin kore takiyya da yin raddinta, zamu ambato su akunshe mu kuma bada amsa a kai:
Tabbas musulmin farko da suka yi zamani da annabi (s.a.w) suna da nasu matsayin rigo da imani da daukar nauyin sakon annabin rahama (s.a.w) zuwa ga duniya lamarin da yake falala da daukaka ne mai girma, sai dai wannan ba ya nufin cewa duk musulmin da ya yi zamani da annabi (s.a.w) adali ne. Akwai bambanci tsakanin girmama al'umma sakamakon a cikinta akwai mutanen da suke tarihi ya yi sheda da daukakarsu da himmarsu da sadaukarwarsu da kuma hukuncin daidaikun mutanen da suke cikin wannan al'ummar.
SAHABI: Sahabi kalmar larabci ce da a kan kalle ta a lokuna da wasu fuskoki: Na farko duban kalmar a Luga da abin da take nufi; 1. Wanda ya lizimci abu kamar idan ya saba da yawo da wata riga da ta zama ana tuna shi da ita. Ko ya saba da kiwon shanu da in an gan shi ana tambayarsa shanun. 2. Ko mai mallakar abu, kamar mai gida, mai littafi da sauransu. Ko mai mallakar tasarrufi da abu.
Hujjoji Kan Halaccin Yin Mauludin Annabi
A Wannan Bahasi Mai Take (Hujjojin Yin Mauludi) na ke so in kawo kadan daga cikin dalilan yin Mauludi, amma kafin nan zan so in fara da kawo dalilan da wadanda ba sa yin Mauludin suke kafawa, na rashin inganci ko ma haramcin yin Mauludin a gurinsu.
Gwagwarmayar Musulunci
Harkar muslunci a Najeriya ta bukaci gwamnatin tarayyar Najeriya da saki Sheikh Ibrahim Zakzaky da ake tsare da shi ba tare da tuhumarsa da wani laifi ba.